'Atiku da Peter Obi Sun Sake Bude wa Tinubu Kofa, APC na Iya Lashe Zaben 2027'

'Atiku da Peter Obi Sun Sake Bude wa Tinubu Kofa, APC na Iya Lashe Zaben 2027'

  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya ce da yiwuwar a maimaita abin da ya faru a babban zaben shekarar 2023 a Najeriya
  • Fayose ya ce rabuwar Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran manyan 'yan adawa na iya sake bai wa Shugaba Bola Tinubu da APC nasara a 2027
  • Ya ce hada kan 'yan adawar Najeriya wuri guda tare da marawa 'dan takara guda baya ne kadai zai iya ba su damar kalubalantar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana irin damar da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ke da ita na sake lashe zabe a 2027.

Fayose ya ce sabanin siyasa da rashin hadin kai tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da tsohon dan takarar LP, Peter Obi, na iya sake bai wa Tinubu damar samun nasara a karo na biyu.

Kara karanta wannan

'Tinubu jan wuya ne a murde zabe': Babachir Lawal na ganin APC za ta zarce

Ayo Fayose.
Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose Hoto: Ayo Fayose
Source: Facebook

Ayo Fayose ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV ranar Litinin.

Wane 'dan takara zai iya fuskantar Bola Tinubu?

A cewarsa, jam’iyyun adawa sun rage wa kansu karfin da za su iya kalubalantar APC ta hanyar kasa hada kai karkashin inuwa daya domin fuskantar zaben 2027.

Tsohon gwamnan ya ce duk da yadda ake ta muhawara a kafafen sada zumunta kan siyasar Najeriya, a zahirin gaskiya babu wata babbar barazana da ke fuskantar Shugaba Tinubu a halin yanzu.

“Mutane ba za su so su ji wannan ba, amma akwai bambanci tsakanin abin da ke faruwa a zahiri da kuma hayaniyar da ake yi a kafafen sada zumunta.
"A gaskiya babu wanda zai iya kalubalantar Tinubu yadda ya kamata,” in ji Fayose.

Atiku da Obi na shirin ba Tinubu dama

Ya bayyana cewa da a ce shugabannin adawa sun samu nasarar kafa hadaka mai karfi tare da tsayar da dan takara guda, da lamarin ya kasance babban kalubale ga shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Sabuwar rigima: Atiku da Wike na musayar yawu kan zaben 2027

Fayose ya ce idan Atiku, Peter Obi da sauran jiga-jigan adawa sun zauna sun hada kai a jam’iyya guda, APC za ta fuskanci gagarumin kalubale, kamar yadda Tribune Nigeria ta rahoto.

“Da hadakar adawa ta tsaya tsayin daka a jam’iyya guda domin fuskantar Tinubu, zan iya cewa zai sha wahala sosai wajen samun nasara. Amma yanzu sun raba kansu zuwa bangarori daban-daban,” in ji shi.
Obi, Atiku da Tinubu.
Manyan yan takarar shugaban kasa da ke shirin fafatawa a zaben 2027, Peter Obi, Atiku Abubakar da Shugaba Bola Tinubu Hoto: Mr. Peter Obi, Atiku Abubakar, Bayo Onanuga
Source: Twitter

Yadda Tinubu ya yi nasara a 2023

Fayose ya ce irin abin da ya faru a zaben 2023 na iya maimaituwa a 2027, yana mai tuna yadda Atiku Abubakar, Peter Obi da Bola Tinubu suka fafata a wata gasa mai zafi tsakanin manyan ‘yan takara uku.

“A 2023 an samu gasa tsakanin manyan ‘yan takara uku. Saboda rashin hadin kai tsakanin adawa ne Tinubu ya samu nasara. Ina ganin hakan na iya sake faruwa a 2027 cikin sauki,” in ji shi.

Fayose ya jefi Gwamna Seyi Makinde da zargi

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi zargin cewa an shirya sace ɗalibai da malamai a wasu makarantun jihar Oyo ne da gangan.

Kara karanta wannan

'Tinubu ya cancanci tazarce saboda dukufa kan magance rashin tsaro,' APC

Ya yi zargin cewa gwamnatin Gwamna Seyi Makinde ce ta shirya sace su a matsayin wani yunƙuri na ƙoƙarin bata sunan Bola Ahmed Tinubu.

Fayose ya ce Gwamna Seyi Makinde bai mayar da martani cikin gaggawa ba, yana zargin cewa ya fi mayar da hankali kan harkokin siyasa fiye da magance matsalar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262