Ko Tinubu na da Abubuwan da Zai Shawo kan Yan Najeriya Su Zabi APC a 2027? An Samu Bayani
- Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya ce gwamnatin Tinubu ta samu gagarumar nasara a fannoni daban-daban
- Ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu da APC na da abubuwan da za su gabatar wa ’yan Najeriya yayin yakin neman zaben 2027
- Shugaban Majalisar Dattawa ya yi hasashen cewa ’yan Najeriya za su sake zaben Tinubu a wa’adi na biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom, Nigeria - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce jam’iyyar APC tana da isassun nasarorin da za ta gabatar wa ’yan Najeriya yayin da take shirin tunkarar zaben 2027.
Akpabio ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu gagarumar nasara cikin shekaru uku da suka gabata, musamman a bangarorin tattalin arziki, noma, tsaro, ilimi da manufofin kula da kudaden gwamnati.

Source: Facebook
Yadda Bola Tinubu ya gaji Najeriya
Ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, lokacin da ya karbi bakuncin mambobin Kwamitin Majalisar Dattawa, kamar yadda Leadership ta rahoto.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawunss Jackson Udom, ya fitar, Akpabio ya ce gwamnatin Tinubu ta gaji tattalin arzikin kasa cikin mawuyacin hali, amma ta bullo da sauye-sauye da suka taimaka wajen inganta yanayin.
APC za ta gabatar da nasarori
“Shugaban kasa ya yi abubuwa da dama ga ’yan Najeriya, ya tarar da tattalin arziki cikin mawuyacin hali.
"Lokacin da ya zo, jihohi 27 ba sa iya biyan albashi da kudaden fansho, amma yau labarin ya canza saboda sake fasalin da ya yi da kuma tunaninsa na kawo sababbin hanyoyi,” in ji Akpabio.
Ya kara da cewa a zaben 2027, ’yan Najeriya za su iya bambance tsakanin wadanda suka cancanta da wadanda ba su cancanta ba, tare da sake zaben Tinubu domin ya yi wa’adi na biyu a matsayin shugaban kasa.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fitar da saƙo ga masu murnar ranar haihuwar Annabi Muhammad SAW a Najeriya
Shugaban Majalisar Dattawan ya ce gwamnatin ta bullo da sababbin tsare-tsare da za su bai wa APC nasarori masu yawa da za ta gabatar wa jama’a yayin yakin neman zaben 2027.
Akpabio ya ce wasu daga cikin masu kalubalantar Tinubu a zaben 2027 ba za su iya bayyana irin nasarorin da suka samu lokacin da suke gwamnonin jihohinsu ba, cewar rahoton Guardian.

Source: Twitter
Akpabio ya soki ’yan adawa
Shugaban Majalisar Dattawan ya kuma yi ikirarin cewa ’yan siyasar adawa sun san irin nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu, amma ba sa son amincewa da su saboda kasancewarsu a bangaren adawa.
“Wadanda suke adawa sun san nasarorin da wannan gwamnati ta samu a bangarorin tattalin arziki, noma, tsaro, ilimi da manufofin kudade, amma saboda suna adawa, ba za su fadi hakan ba,” in ji shi.
Akpabio ya sasanta da Adams Oshiomhole
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya ba Adams Oshiomhole hakuri game da sabanin da ya rika shiga tsakaninsu a majalisa.
Rahoto ya nuna cewa Sanata Akpabio ya ba shi hakuri saboda ya bayyana wasu kalaman Adams Oshiomhole da cewa ba su dace da na sanata ba.
Asali: Legit.ng
