2027: Shugaban Karamar Hukuma Ya Fada wa Wadanda ba ‘Yan APC ba Su Bar Abuja
- Sai inda karfin Samuel Danjuma Shekwolo ya kare wajen ganin nasarar APC a babban zaben da za a yi a 2027
- Shugaban karamar hukumar Kuje ya ce ba za su bar ayyukan gwamnatin Nyesom Wike su tafi haka nan a banza ba
- Mai girma Shekwolo ya fada wa ‘yan adawa su tattara kayansu su bar Kuje a Babban birnin tarayya na Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Shugaban karamar hukumar Kuje a Babban birnin tarayya Abuja, Samuel Danjuma Shekwolo yana neman tada kura.
Samuel Danjuma Shekwolo ya fada wa mazauna Kuje a Abuja cewa duk wanda ba ‘dan APC ba ya bar yankin gabanin zaben 2027.

Source: Getty Images
Shugaban karamar hukumar Kuje ya yi barazana
Daily Trust ta ce an ji Samuel Danjuma Shekwolo yana wannan magana ne lokacin da APC ta fara shirin yakin zaben shugaban kasa.
An ga bidiyon shugaban karamar hukumar a shafukan sada zumunta na zamani yana cewa ba za su yarda da adawa da Bola Tinubu ba.
A lokacin da ake so a yi zaben badi cikin lumuna, Samuel Shekwolo ya fito karara yana nuna yadda za su yaki ‘yan adawar jam’iyyar APC.
Ciyaman ya yabi ayyukan Wike a Abuja
Shugaban karamar hukumar ya nemi mazauna Kuje su goyi bayan jam’iyya mai mulki saboda ayyukan da ya ce Nyesom Wike yana yi.
Ciyaman din ya yabi kokarin gwamnatin Bola Tinubu da ta Nyesom Wike a birnin Abuja. Labarin ya zo a jaridar Daily Post ranar Talata.
A cewarsa, babu wata tababa a zabe mai zuwa domin kuwa zai yi duk bakin kokarinsa wajen yakar wadanda ba su tare da APC mai ci.
Hakan yana zuwa ne bayan an ji Wike yana maganar cewa zai dage ya tabbatar da nasarar shugaba Tinubu a birnin Abuja da jihar Ribas.
Shi ma Shekwolo ya nanata wannan, yana mai tada hankalin ‘yan jam’iyyun adawa.
"Na fada a karamar hukuma ta, ko dai kana tare da APC ko kuma ka bar karamar hukumar. Kuma babu tababa a kan wannan ko kadan."
- Samuel Danjuma Shekwolo

Source: Getty Images
Ko a bi APC ko a bar Abuja
Shekwolo yana mai mamakin yadda mutane za su ga ayyukan Wike da na gwamnatin tarayya kuma su ki zaben APC a zabe mai zuwa.
Samuel Danjuma Shekwolo ya ce:
"Kun san meyasa? Ba zai yiwu a samu Minista da Shugaban kasa suna aikin da suke yi ba, kuma a ranar zabe ka ce za ka taka ni. Ba zan yarda ba.
"Ko dai kana tare da mu ko kuwa ba ka tare da mu."
Wannan magana dai ta jawo masa tir musamman daga wajen masu bibiyar dandalin Facebook.
APC ta lashe duka kujeru a zaben Ebonyi
A lokacin da baban shi yake minista, an ji labari yaron tsohon gwamnan Ebonyi Sanata David Umahi zai zama ciyaman a karamar hukumarsa.

Kara karanta wannan
Minista ya fasa kwai, an ji yadda ake shirin ƙarawa Atiku 'hawan jini' kafin zaben 2027
Jam'iyyar APC mai mulki ce ta lashe dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 13 gaba ɗaya da kuma kujerun kansiloli 171 na jihar.
Daga cikin waɗanda suka samu nasara har da Osborn Nweze Umahi, wanda ɗan Ministan Ayyuka ne, zai shugabanci ƙaramar hukumar Ohaozara.
Asali: Legit.ng

