Milo Ya Tallafawa Masu Sana'ar Shayi a Kano da Jos

Milo Ya Tallafawa Masu Sana'ar Shayi a Kano da Jos

Kamfanin Nestlé Milo ya tallafa wa masu sana’ar sayar da shayi 2,000 a Kano da Jos ƙarƙashin shirinsa na tallafa wa kwastomomin da suka jima suna hulda da shi domin ƙarfafa gwiwar masu kananan sana’o’i.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kamfanin ya ce rabon tallafin zai kuma ƙarfafa rawar da Milo ta shafe tsawon shekaru tana takawa a matsayin mahadin shan shayi a Arewacin Najeriya.

Shirin ya bai wa masu shayi kayan tallafin da suka hada da risho mai amfani da iskar gas, tukunyar gas, malafar kare rana, fitila mai amfani da hasken rana, kofuna da kuma sinadarin Milo.

Masu shirya taron sun ce an kaddamar da shirin ne domin karrama rawar da masu shayi ke takawa wajen samar da karin kumallo a kullum a Arewacin Najeriya, tare da taimaka musu wajen bunƙasa sana’o’insu.

Yadda aka tallafawa masu shayi
Lokacin da kamfamin Milo ya tallafawa masu shayi.
Source: Facebook

Da yake jawabi a yayin taron da aka gudanar a Kano a makon da ya gabata, wakilin kamfanin na Nestle Milo a Najeriya, Gilbert Tweneboah-Koduah, ya ce wannan tallafi na nuna yadda kamfanin ke son inganta alaka da al’umma.

Kara karanta wannan

Ba yadda ake tsammani ba, gwamna ya fadi silar rashin tsaro a yankinsa

“Masu shayi sun zama wani muhimmin bangare na al’adar Arewacin Najeriya inda jama’a da dama ke dogaro da su wajen karin kumallo.
"A matsayinsa na abin sha lamba daya a Najeriya, Milo na son kasancewa jigo a wannan al’ada tare da tallafa wa masu shayi su bunkasa kasuwancinsu,”

In ji shi.

Ya kuma ce shirin ya fara ne bara da masu shayi 400, amma yanzu an faɗaɗa shi zuwa mutum 2,000 a biranen Kano, Jos, Kaduna da Maiduguri, tare da shirin ƙara faɗaɗa shi zuwa fadin Arewacin Najeriya.

Shugaban Ƙungiyar Masu Sayar da Shayi ta Jihar Kano, Usman Muhammad Usman, ya yaba wa Nestlé Milo bisa goyon bayan da ya daɗe yana ba su tsawon lokaci.

Wajen taron kamfanin Milo
Mahalarta taron da kamfanin Milo ya tallafawa masu shayi a Kano da Jos
Source: Facebook
“Na shafe shekaru 36 ina sana’ar shayi, kuma a kullum Milo abokin hulɗa ne da na jima ina hulda da shi. Jama’a suna gamsuwa da ingancinsa, wannan tallafi zai taimaka mana wajen bunkasa sana’armu,”

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

In ji shi.

Ita ma Jakadiyar Milo kuma fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Mansura Isa, ta ce kamfanin ya saba tallafa wa al’umma ta hanyoyi da dama, ciki har da ciyar da daruruwan mutane a kullum a lokacin azumin watan Ramadan da ya gabata.

Shi ma wani jakadan kuma jarumin fina-finan na Hausa, Sulaiman Yahaya wanda aka fi sani da Bosho, ya ce dawar da ake nomawa a Najeriya ce kaso 85 cikin 100 na kayan da ake amfani da su wajen sarrafa Milo, abin da ya sa ya dace da al’ada kuma yake ƙara tallafa wa manoma na gida.

Shi ma wani mai sana’ar shayin a Jos, Musa Ibrahim, ya yaba da taron inda ya ce suna alfahari da abin da kamfanin ya yi musu.

Wasu da suka samu tallafin Milo
Wasu masu shayi da suka samu tallafin Milo.
Source: Facebook

Ya kuma ƙalubalanci sauran kamfanonin da suke sarrafa kayayyakin da masu shayi ke amfani da su da su yi koyi da Milo wajen kyautata wa abokan sana’arsu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah

“Saboda duk wani sinadarin shayi da za ka saya ka kai gida domin a yi amfani da shi, kafin naka ya ƙare mai shayi ya sayar da ninkin haka,”

In ji shi.

Kamfanin dai ya sha alwashin ci gaba da faɗaɗa shirin domin tabbatar da cewa masu shayi a Arewacin Najeriya da dama sun samu kayan aikin da za su taimaka musu wajen biyan buƙatun kwastomominsu da kuma bunkasa rayuwarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng