An Kashe Wani Bawan Allah a Hanyar Dawowa daga Wurin Maulidin Annabi SAW a Kano

An Kashe Wani Bawan Allah a Hanyar Dawowa daga Wurin Maulidin Annabi SAW a Kano

  • Rahotanni sun nuna cewa yan daba sun kashe wani matashi mai suna Yusuf Ahmad a unguwar Dorayi da ke karamar hukumar Gwale a Kano
  • Bayanan da ke fitowa sun nuna cewa lamarin ya biyo bayan rikicin ramuwar gayya da ya samo asali daga jikkata wani matashi a unguwar
  • Dakarun yan sanda sun ce an kama wasu da ake zargi da hannu a kashe Yusuf, wanda ya dawo daga wurin Maulidi yayin da bincike ke ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - An kashe wani matashi mai suna Yusuf Ahmad, wanda ake zargin wasu ’yan daba ne suka kashe shi a unguwar Dorayi da ke karamar hukumar Gwale a Jihar Kano.

Wannan al'amari ya tada hankulan mutanen yamkin, musamman saboda jik cewa mamacin ya dawo ne da wurin taron masu maulidin Annabi Muhammad SAW.

Kara karanta wannan

Wani mutumi ya zare bindiga, ya buɗe wa mutane wuta a wurin bikin aure a jihar Kano

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rikicin da ya rutsa da dan Maulidi

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mummunan lamarin ya faru ne bayan wani rikici da ya samo asali ga jikkata wani matashi a wata unguwar makwabta, lamarin da ya rikida ya zama tashin hankali.

Rahotanni sun ce lamarin ya fusata abokan matashin da ya jikkata, inda suka tattara kansu domin neman daukar fansa kan wadanda suka taba abokinsu.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an tura jami’an tsaro yankin ne bayan samun kiran neman agaji.

Yadda aka kashe matashin a Kano

Wani ganau, Salihu Shamsu Saleh, ya shaida cewa marigayin yana kan hanyarsa ta komawa gida ne bayan halartar taron Mauludi, lokacin da wasu ’yan daba suka tare shi tare da kai masa hari da makamai.

Ya ce maharan sun yi wa matashin mummunan sara a kirji da wuya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Kara karanta wannan

Surutun jama’a da mantawa da wasu ya jawo an janye sunayen kwamitin kamfen Tinubu

’Yan sandan sun ce an kama wasu mutane da ake zargi da hannu a kisan, yayin da bincike ke ci gaba da gano tare da cafke sauran wadanda ke da hannu a lamarin.

Mazauna yankin sun yi kira ga matasa da su guji daukar doka a hannunsu, suna gargadin cewa rikicin kungiyoyin ’yan daba na ci gaba da jefa rayukan al’umma cikin hadari.

Kano.
Kwamishinan yan sandan Kano, CP Bakori yana hira da manema labarai Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Yan Maulidi na bukatar tsaro

Wani matashi, Sani Ahmad ya shaida wa Legit Hausa cewa akwai bukatar hukumomi su tashi tsaye don kare rayukan al'umma musamnan a wannan lokaci na Maulidi.

Ya ce bai kamata rayukan masu zuwa Maulidi su rika shiga hadari ba, domin suna fitowa ne domin nuna farin ciki da murnar watan da aka haifi fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.

"Ba mu nemi kowa da fada ba, murna kawai muke yi saboda wannan wata yana da daraja, mu masoya Manzon Allah SAW ne, don haka muna bukatar tsaro," in ji shi.

Kano: An kashe mutum 1 a taron biki

Kun ji cewa wani mutumi dan kimanin shekaru 34, Rabiu Mukthar,nya bude wa mutane suna tsakiyar shagali a taron bikin aure a jihar Kano.

Ana zargin mutumin ya fito daga gidansa dauke da bindiga tare da bude wa mutane wuta saboda sun dame shi da kiɗa, inda mutum daya ya rasa ransa, yayin da wasu uku suka jikkata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262