Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Chinda Ya Yi Murabus daga Mukaminsa

Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Wakilai, Chinda Ya Yi Murabus daga Mukaminsa

  • Dan takarar gwamnan jihar Rivers na jam'iyyar APC, Hon. Kingsley Chinda ya ajiye mukamin shugaban marasa rinjaye na Majalisar wakilai
  • Chinda ya sanar da haka ne a takardar da kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya karanta, inda ya sanar da ficewarsa daga PDP zuwa APC
  • Tun farko dan Majalisar, wanda ke da alaka ta siyasa da ministan Abuja, Nyesom Wike ya lashe tikitin takarar gwamna na APC a jihar Rivers

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilai ta Tarayya, Kingsley Chinda, ya yi murabus daga mukaminsa tare da ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ne ya sanar da murabus da sauya shekar Chinda a zaman majalisar na ranar Talata bayan dawowa daga hutun makonni hudu.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Jam'iyyar APC ta dakatar da dan majalisar tarayya daga jihar Jigawa

Kingsley Chinda.
Tsohon shugaban marasa rinjaye na Majalisar wakilai, Hon Kingsley Chinda Hoto: @nyerishii
Source: Twitter

Sanarwar ta kawo karshen rade-radin da suka dade suna yawo kan makomar siyasar Chinda, kamar yadda jaridar Premium Times ta rahoto.

Tun farko an fara ce-ce-ku-ce kan siyasar dan majalisar ne bayan ya shiga zaben fidda gwani na APC domin neman takarar gwamnan jihar Rivers ba tare da ya bayyana murabus daga PDP ko mukaminsa na majalisa ba.

Hon. Chinda ya fice daga PDP zuwa APC

Takardar murabus dinsa da Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya karanta ta nuna cewa ya ajiye mukamin ne tun daga ranar 23 ga Afrilu, 2026.

A cikin wasikar da ya aikewa shugaban majalisar, Chinda ya nuna godiya bisa damar da aka ba shi na jagorantar 'yannadawa a majalisar.

Dan majalisar ya ce ya dauki hakan a matsayin wata babbar dama ta yi wa kasa hidima tare da bayar da gudunmawa wajen bunkasa dimokuradiyya da ci gaban Najeriya.

Chinda ya kuma tabbatar da cewa duk da murabus dinsa daga mukamin jagoran marasa rinjaye, zai ci gaba da gudanar da aikinsa a matsayin dan majalisa tare da mara wa ayyukan majalisar baya.

Kara karanta wannan

'Dan majalisar dokokin Kano ya bar tafiyar Kwankwaso, ya fice daga jam'iyyar NDC

Sai dai abin lura shi ne Chinda bai halarci zaman majalisar da aka sanar da murabus dinsa ba, kamar yadda tashar Channels tv ta ruwaito.

Tasirin matakin da Chinda ya dauka

Masu lura da harkokin siyasa na ganin sauya shekar tasa na daga cikin manyan sauye-sauyen siyasa da suka faru a Majalisar Wakilai kafin zaben 2027, la’akari da matsayinsa a PDP da kuma tasirinsa.

Majalisa.
Majalisar wakilan tarayya yayin da mambobi ke tsakiyar zama a Abuja Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Bayan ficewar Hon. Chinda, ana sa ran mambobin PDP a majalisar za su fara tuntubar juna domin zakulo sabon wanda zai maye gurbinsa a matsayin jagoran marasa rinjaye.

Chinda na cikin jerin manyan ‘yan siyasar jihar Rivers da suka koma APC a ‘yan watannin nan yayin da ake ci gaba da samun sauye-sauyen siyasa a jihar gabanin babban zaben shekarar 2027.

Yan Majalisa 6 sun bar PDP zuwa APM

A wani labarin, kun ji cewa 'yan majalisar wakilan tarayya daga jihar Oyo, shida da ke biyayya ga Gwamna Seyi Makinde sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APM.

ikin wasiƙunsu na sauya sheƙa, ‘yan majalisar sun bayyana cewa rikicin cikin gida da takaddamar shugabanci a PDP ne ya sa suka zaɓi wata sabuwar hanyar siyasa domin cimma burinsu na 2027.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace tsohon manjo janar da matarsa a Katsina

Tun farko Makinde ya fice daga PDP zuwa APM makonnin da suka gabata, kuma tuni ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262