Pantami na Fuskantar Kalubale, Wasu Manyan Jiga Jigai Sun Koma APC a Gombe

Pantami na Fuskantar Kalubale, Wasu Manyan Jiga Jigai Sun Koma APC a Gombe

  • Wasu manyan jiga-jigan siyasa a jihar Gombe sun rungumi tafiyar 'dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a zaben 2027, Jamil Isyaku Gwamna
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen zaben 2027, wanda ake ganin zai yi zafi a Gombe musamman tsakanin Gwamna da Farfesa Isa Pantami
  • Jamilu Gwanna ya yabi masu sauya shekar, yana mai cewa sun dauki matakin da ya dace don ba da gudummuwa wajen inganta jihar Gombe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Gombe, Nigeria - Wasu manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa a jihar Gombe sun sauya sheka zuwa APC domin marawa dan takarar gwamnan jam’iyyar a zaben 2027, Jamil Isyaku Gwamna baya.

Sauya shekar ta fito ne yayin wata ziyara da suka kai wa Gwamna a Gombe ranar Litinin, inda suka bayyana cewa sun dauki matakin ne saboda yadda suke ganin yana da kwarewa, gaskiya da kuma farin jini.

Kara karanta wannan

"Kun tona wa kanku asiri," Wike ya taso Atiku, Peter Obi da Kwankwaso ana shirin zaben 2027

Gwamna.
Dan takarar gwamnan APC a Gombe, Jamil Gwamna tare da wasu manyan jiga-jigai Hoto: Dr. Jamil Gwamna
Source: Facebook

Manyan jiga-jigai sun shiga APC

Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Jamilu Gwamna kan harkokin yada labarai, Ibrahim Sani Shawai, ya fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa wadanda suka sauya shekar sun fito ne daga manyan jam’iyyun adawa kamar PDP, ADC da LP.

Daga cikin fitattun mutanen da suka jagoranci sauya shekar akwai Farfesa Sulaiman Dankande, wani jigo a PDP, Hon. Nura Abba, mataimakin sakataren tsare-tsare na PDP a jihar da Hon. Abdullah Amtai, sakataren tsare-tsare na ADC.

Sauran sun hada da Hon. Dedan Mela, tsohon shugaban karamar hukumar Billiri, da kuma Hon. Murtala Usman Dukku, tsohon jami’in hulda da jama’a na PDP a jihar Gombe.

Sun bayyana dalilin komawa APC

Da yake magana a madadin tawagar, daya daga cikin jagororin masu sauya shekar ya ce sun yanke shawarar komawa APC ne domin goyon bayan shugaban da suke ganin yana da hangen nesa da kuma damar kawo ci gaba ga jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ajiye girma yana rokon talaka afuwa da sake zaben APC a 2027

“Mun yanke shawarar shiga APC ne saboda muna ganin Dr. Jamil Isyaku Gwamna yana da nagarta, kwarewa da kuma kyakkyawan tsari na bunkasa jihar Gombe. Mun kuduri aniyar marawa takararsa baya domin samun nasara a zaben 2027,” in ji su.
Gwamna.
Dan takarar gwamnan APC a jihar Gombe, Jamil Gwamna a wurin wani taro na mata Hoto: Dr. Jamil Gwamna
Source: Facebook

Gwamna ya yi maraba da masu shiga APC

A nasa bangaren, Jamil Isyaku Gwamna ya tarbi sababbin mambobin cikin farin ciki tare da bayyana sauya shekar a matsayin wani babban ci gaba ga kokarin da ake yi na hada kan al’umma domin ci gaban Gombe.

A wata sanarwa da ya wallafa a Facebook, Gwamna ya yaba musu kan abin da ya kira jarumtaka da kishin jihar Gombe, yana mai tabbatar musu cewa gudunmawar da za su bayar za ta taimaka wajen gina kyakkyawar makoma ga al’ummar jihar.

Pantami ya samu karin goyon baya

A wani labarin, kun ji cewa Dr. Ibrahim Adamu Usman, wanda ya nemi takarar kujerar Sanata na Gombe ta Arewa a jam’iyyar LP, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyya.

Rahotanni sun nuna cewa dan siyasar ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar gwamnan na jam'iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.

Ibrahim Usman ya bayyana wannan matsaya ne a wani taron magoya bayansa, inda ya ce ya yanke shawarar bayan doguwar tattaunawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262