Gwamnan Kebbi Ya Kafa Sashen Kula da Kiristoci, An Ji Dalili
- Gwamna Nasir Idris ya umarci Ma’aikatar Harkokin Addini ta Kebbi ta kafa sashe na musamman domin kula da kiristoci a yankin
- Ya ce za a naɗa daraktan Kirista domin jagorantar sabon sashen bisa ka’idojin adalci da daidaito a lokacin da idon duniya ke kan Najeriya
- Gwamnan ya yaba wa Kiristocin jihar kan addu’o’insu da goyon bayan da suka ba shi a ƙoƙarinsa na neman wa’adin mulki na biyu a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kebbi –Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya umarci Ma’aikatar Harkokin Addini ta jihar da ta kafa Sashen Harkokin Kiristoci, wanda zai kasance ƙarƙashin jagorancin daraktan Kirista.
Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne yayin da shugabannin reshen Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta Jihar Kebbi suka kai masa ziyarar godiya.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Gwamnan ya bayyana cewa kafa sashen na daga cikin matakan tabbatar da adalci da daidaito tsakanin al’ummomin jihar.
Alkawarin gwamnan Kebbi ga jamaar jihar
Gwamna Nasir Idris ya shaida wa shugabannin CAN cewa Allah ne Ya ba su damar kasancewa a kan madafun iko, don haka suna iya bakin ƙoƙarinsu wajen magance matsalolin da al’ummar jihar ke fuskanta.
Ya ce gwamnatin jihar tana ba da muhimmanci sosai ga adalci da daidaito wajen tafiyar da harkokin mulki wanda zai kula da kowa ba tare da nuna banbamcin ba.

Source: Original
A cewarsa, babu wani dalili da zai sa Kiristoci su kasance ba tare da wakilci a Ma’aikatar Harkokin Addini ba, ko ma a kasafta musu ma’aikata ta musamman kamar yadda ake yi a wasu jihohin ƙasar.
Ya ce gwamnatinsa ba za ta taba nuna son kai ko wariya ga wasu ba, tare da bayyana cewa za a rika aiki domin kowane dan jiha
Gwamna ya gode wa mutanen Kebbi
Gwamnan ya kuma gode wa shugabannin CAN bisa addu’o’in da suke yi domin samun zaman lafiya a Jihar Kebbi da ma ƙasar baki ɗaya.
Haka kuma, ya yaba musu bisa goyon bayan da suka nuna masa a ƙoƙarinsa na neman sake zaɓe a matsayin gwamnan jihar Kebbi a zaɓen 2027.
Ya ce haɗin kai da fahimtar juna tsakanin mabambantan addinai na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar.
Gwamna ya kirkiro sabbin masarautu a Kebbi
A baya, mun kawo labarin cewa gwamnan jihar Kebbi, Dr Nasir Idris, ya amince da kafa sabuwar gunduma mai kunshe da yankunan kauyuka takwas a karamar hukumar Dandi.
Dr. Nasir Idris ya kuma amince da nada sabon mai unguwa a karamar hukumar Augie domin karfafa tsarin mulkin gargajiya da inganta shugabanci a matakin kasa da ke kusa da jama'a.
Gwamnan ya kuma nada mutumin da zai jagoranci sabuwar gundumar da aka kafa domin gudanar da harkokin mulki wanda zai kara kusanta shugabanni da jama'arsu.
Asali: Legit.ng

