'Dan Majalisar Dokokin Kano Ya Bar Tafiyar Kwankwaso, Ya Fice daga Jam'iyyar NDC
- 'Dan Majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar mazabar Makoda, Muhammad Ahmad Tomas ya sauya sheka daga NDC zuwa APC
- Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya karbe shi a wata ziyara daya kai masa har gida a Abuja yau Litinin
- Barau ya tabbatar wa dan ajalisar cewa za a ba shi cikakkiyar dama kamar yadda kowane mamba ke samu a jam'iyyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya karbi dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar mazabar Makoda, Muhammad Ahmad Tomas, wanda ya sauya sheka zuwa APC.
'Dan Majalisar ya koma jam'iyyar APC mai mulki ne bayan ya fice daga NDC, wacce ya shiga tare da 'yan tafiyar Kwankwasiyya a makonnin da suka gabata.

Source: Facebook
Sanata Barau ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook tare da hotuna yau Litinin, 1 ga watan Yuni, 2026.
Dawowar Muhammad Tomas APC na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin siyasa ke kara daukar zafi gabanin babban zaben shekarar 2027, musamman a jihar Kano.
'Dan Majalisa ya sanar da komawa APC
'Dan majalisar ya bayyana komawarsa APC ne yayin wata ziyara da ya kai gidan Sanata Barau Jibrin da ke Abuja ranar Litinin.
Muhammad Tomas ya samu rakiyar shugabannin kananan hukumomin Makoda da Dambatta, Alhaji Isa Currency da Alhaji Jamilu Abubakar Dambatta, yayin ziyarar.
A wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, Sanata Barau ya bayyana dawowar Muhammad Tomas a matsayin wani muhimmin ci gaba ga jam’iyyar APC a Kano.
“Yau na yi farin cikin karbar Hon. Muhammad Ahmad Tomas, dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar mazabar Makoda, wanda ya dawo babbar jam’iyyarmu ta APC daga NDC,” in ji Barau.
Barau ya yaba da matakin dan majalisar
Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce matakin da Muhammad Tomas ya dauka na komawa APC ya nuna hangen nesa da kuma jajircewarsa wajen mara baya ga ci gaba da kyakkyawan shugabanci.
Ya bayyana cewa dawowar 'dan majalisar za ta kara wa APC karfi musamman a yankin Sanatan Kano ta Arewa da kuma jihar Kano baki daya.
“Matakin da ya dauka na sake hada kai da APC ya nuna kudurinsa na ganin an samu ci gaba da shugabanci nagari,” in ji shi.

Source: Facebook
Barau ya tabbatar wa dan Majalisar cewa zai samu cikakkiyar dama kamar sauran ‘ya’yan jam’iyyar, tare da kira ga mambobin APC da su ci gaba da hada kai domin karfafa jam’iyyar.
'Dan majalisar Kano ya koma NDC
A wani labarin, kun ji cewa dan majalisar dokokin Kano mai wakiltar mazabar Gwale, Hon. Abdulmajid Isa Umar Mai Rigar Fata, ya tattara kayansa daga APC ya koma NDC.
Tsohon gwamnan Kano kuma jigo a NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ya iarbi dan majalisar a gidansa da ke Maitama a Abuja.
Kwankwaso ya bayyana cewa shigowar sababbin mambobin zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi a matakin ƙasa da kuma tushen al’umma a Kano.
Asali: Legit.ng

