Abubuwa 5 da Za Su Iya Faruwa a Yakin Isra'ila da Iran da Yadda Zai Shafi Duniya
Abin da ya fara a matsayin zargin juna tsakanin makiya biyu, yanzu ya rikide zuwa mummunan rikici mafi hadari a Gabas ta Tsakiya da aka gani cikin 'yan shekarun nan.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
A ranar Alhamis, 13 ga Yuni, Isra’ila ta kaddamar da hare-haren sama masu karfi kan fiye da wurare 100 masu mahimmanci a Iran; daga cibiyoyin nukiliya har zuwa sansanonin soja.

Asali: Getty Images
Abin da masana ke cewa kan yakin Iran-Isra'ila
Iran kuwa ba ta tsaya kallon abin da ke faruwa ba, ta mayar da martani da ruwan makamai da jirage marasa matuka zuwa cikin Isra’ila, inda ta lalata gine-ginen gwamnati da wasu kayayyakin more rayuwa, inji rahoton BBC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane fiye da 100 aka rahoto cewa sun mutu a Iran, yayin da Isra’ila ta rasa mutane da dama, yayin da kuma daruruwan mutane suka jikkata a kasashen biyu.
Yayin da kasashen biyu ke musayar wuta, manyan kasashen duniya na nuna damuwa matuka, suna tsoron rikicin zai rikide zuwa yakin da zai shafe Gabas ta Tsakiya, ko kuma yajawo yakin duniya na III.
Ga wasu daga cikin hadurran da masana ke tsoron ka iya afkuwa a rikicin Iran da Isra'ila:
1. Amurka ta tsunduma cikin rikicin
Ko da yake Amurka na musanta hannu a harin da Isra’ila ta kai Tehran, amma Iran na zargin cewa sojojin Amurka sun ba da goyon baya a boye.
Masana na ganin wannan ka iya sa Iran ta kai hari kan sansanonin Amurka a Iraki, Gulf da sauran wuraren da ke da muhimmanci.
Ko da yake mayakan Hamas da Hezbollah sun raunana yanzu, amma Iran na da mayakan sa kai a Iraki masu karfin makamai, wadanda ke zaman jiran ko-ta-kwana.
Sai dai Amurka ta riga ta dakile yiwuwar faruwar hakan, domin tuni ta janye wasu daga cikin jami’anta, tare da jan kunnen Iran da murya mai karfi akan harin da ka iya shafar Amurkawa.
To amma ana ganin Shugaba Donald Trump zai iya tsunduma cikin wannan yaki idan wani dan Amurka ya mutu a Tel Aviv ko wani wuri na daban, musamman idan hakan ta faru saboda harin Iran.
Idan kuwa har hakan ta faru, to za a iya cewa, faduwa ta zo daidai da zama ga Isra'ila, domin an dade ana zargin Benjamin Netanyahu yana kokarin janyo Amurka cikin yaki da Iran.
Masana harkokin soja na cewa sai da taimakon Amurka ne kawai za a iya lalata cibiyoyin nukiliya na Iran da ke karkashin kasa irin na Fordow.
Kodayake Trump ya sha alwashin ba zai sake sanya Amurka cikin “yaƙe-yaƙe” ba, yawancin ‘yan jam’iyyarsa na goyon bayan Isra’ila da ra’ayin cewa lokaci ya yi da za a tumbuke gwamnatin Iran.
Amma idan hakan ta faru, za a tsunduma cikin mummunan rikici, wanda zai iya yin tasiri har zuwa ga sauran kasashen duniya.
2. Kasashen Gulf su ma sun shiga fadan
Idan Iran ta gaza kai farmaki kan manyan cibiyoyin sojin Isra’ila, ana ganin za ta iya mai da hankalinta kan kasashen Gulf da ta dade tana zargi da taimaka wa abokan gabar ta.
Wannan yanki na dauke da kamfanonin mai da na’urorin wutar lantarki. Ko a shekarar 2019, Iran ta kai hari kan filayen man Saudiyya, sannan a 2022, Houthi, wakilan Iran a Yemen, sun kai hari a UAE.
Ko da yake yanzu an samu dan zaman lafiya da wadannan kasashe, amma suna dauke da sansanonin sojin Amurka, kuma wasu sun taimaka wa Isra’ila a boye wajen kare kanta daga harin Iran a bara.
Idan Iran ta kai farmaki a Gulf, za a iya bukatar taimakon Amurka wajen kare kai, lamarin da zai kara tayar da jijiyoyin wuya a fadan Gabas ta Tsakiya.
3. Isra’ila ta gaza lalata makaman nukiliya
Me zai faru idan Isra’ila ta kasa lalata makaman nukiliyan Iran? Wannan ma babbar tambaya ce, wacce amsarta za ta dogara ne kawai ga abin da zai faru a kwanaki masu zuwa.
Da yawa na ganin cewa ba lallai ne Isra'ila ta iya lalata sinadarin uranium da Iran ke da shi ba. Sinadarin ne mataki na daya kafin samar da makamin nukiliya, kuma ana ganin zai iya boye wa cikin duwatsu ko karkashin kasa.
Duk da cewa Isra'ila ta kashe kwararrun masana nukiliya, amma ana ganin ba za ta iya kawar da ilimin da Iran ke da shi na kera nukiliar ba.
Idan har Iran ta yanke shawarar cewa hanyar kare kanta ita ce ta gaggauta kera makamin nukiliya, to lallai hakan zai iya zama hadari matuka, ba ga Isra'ila kadai ba, har ma ga duniya.
Kuma ana ganin sababbin shugabannin soja na Iran na iya zama masu zafin rai da rashin tsoro, wanda hakan ka iya sa Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare yayin da take samun martani daga Iran din.
Idan kuwa Isra'ila ta samu nasarar lalata makaman nukiya ko dukkanin sinadaran hada su a Iran, to za a iya cewa yakin yazo karshe, kuma Iran za ta zama ganima ga Isra'ila.
4. Iran ta rufe mashigar Hormuz
Me zai faru idan Iran ta rufe mashigar ruwa ta Hormuz, hanyar da ta ke da matukar muhimmanci, kuma mai daukar kaso mai tsoka a sufurin man fetur na duniya?
Masana na fargabar cewa idan Iran ta ji matsin lamba, za ta iya rufe mashigar ruwa ta Hormuz, wanda hakan zai kawo cikas ga rarraba mai a kasashen duniya, inji rahoton Forbes.
A gefe guda ma, Houthi da ke Yemen, wacce abokiyar Iran ce ta karshe da suka rage, na iya kara kai farmaki kan jiragen ruwa a Tekun Bahar Maliya.
Dama dai kasashe da dama na fama da tsadar rayuwa, don haka ake ganin rufe mashigar Hormuz zai jawo hauhawar farashin man fetur tare da jefa tattalin arziki cikin mawuyacin hali.
Kuma kada a manta, wanda zai fi cin moriyar hakan shi ne shugaban Rasha, Vladimir Putin, domin ana ganin zai samu karin kudaden shiga domin cigaba da yakin Ukraine.
5. Tumbuke gwamnatin kasar Iran
Me zai faru idan Isra’ila ta cimma burinta na ruguza mulkin juyin juya halin Iran?
Netanyahu ya bayyana cewa babban burinsa shi ne dakile Iran daga mallakar makamin nukiliya. Amma cikin jawabin sa na jiya, ya bayyana cewa yana fatan rikicin zai taimaka wa al’ummar Iran wajen samun ‘yanci daga “gwmantin zalunci”.
Tumbuke gwamnatin Iran zai iya faranta wa wasu a yankin rai, musamman Isra’ilawa. Amma me zai biyo baya? Akwai bukatar ku tuna da halin da aka shiga a Iraki da Libiya bayan faduwar gwamnatocinsu masu karfi.
Ana ganin rusa gwamnatin Iran zai iya jawo rikicin cikin gida, rushewar doka da oda da kuma jawo wata matsala a duniya gaba daya da ba za a iya misaltawa ba.
Don haka, masa na ganin makomar kasashen biyu na hannun Iran kan yadda za ta ci gaba da mayar da martani da kuma yadda Amurka za ta iya takawa Isra’ila birki.

Asali: Getty Images
Tasirin rikicin Iran da Isra’ila ga tattalin arzikin duniya
Bayan mun duba abubuwa 5 da ka iya faruwa a rikicin Iran da Isra'ila, akwai bukatar mu kalli tasirin rikicin kasashen biyu ga tattalin arzikin duniya, kamar yadda rahoton ICIS ya nuna.
1. Yanayi na 1: Dawo da zaman lafiya
Idan kasashen biyu suka dakatar da kai wa juna hare-hare, ta hanyar yin sulhu da tattaunawar diflomasiyya, walau a tsakaninsu kadai ko da taimakon wasu kasashe, to ana sa ran:
- Farashin man fetur zai sauka cikin gaggawa, kasuwanni za su daidaita, sabanin yadda a yanzu komai ya rikice.
- Ba za a ci gaba da samun tsadar farashin kayayyaki ba, kuma bankunan duniya za su ci gaba da aiki ba tare da matsin lamba ba.
- A bangaren hanyoyin sufuri ma, ba za a samu matsala ba; kuma mashigar Hormuz za ta ci gaba da zama a bude ga jiragen dakon kaya.
- Kasuwannin zuba jari da cinikayya za su dawo da karfinsu, wadanda ke da sauran kudin da ba su tsiyaye ba a yanzu, za su iya samun riba mai yawa.
2. Yanayi na 2: Yakin sunkuru ya ci gaba tsakaninsu
Idan sasanci ya ki samuwa, to ana ganin Isra’ila da Iran za su ci gaba da farmakar juna, amma ba za su yi hakan kai tsaye ba, za su iya yin yakin sunkuri a kasashen da ke makwabtaka da su, kamar Iraki, Lebanon, Syria, da Yemen.
Idan har hakan ta faru, to:
- Farashin man fetur zai yi tashin gwauron zabi, kuma kasuwanni za su rikice tare da karuwar kudin kaya.
- Za a samu hauhawar farashin kaya da karancin makamashi, wanda zai shafi tattalin arzikin duniya gaba daya.
- Kasuwanni zuba jari za su zagwanye, masu saye-da-sayarwa za su rude, yayin da kayayyakin da ake cinikayyarsu za su rage daraja.
3. Yanayi na 3: Yani ya tsananta, da rufe Hormuz
Idan yaki mai tsanani ya barke tsakanin kasashen biyu, to ana fargabar:
- Farashin man fetur zai kai kololuwar tashi, sannan zai zama barazana ga al'umma domin zai jawo tsadar rayuwa a duniya.
- Za a fuskanci karancin kayayyaki a kasuwanni da masa'antu saboda yankewar hanyoyin ruwa da tsayawar dakon kaya ta jiragen ruwa.
- sananin rikicin zai iya haifar da mummunar koma baya ga tattalin arzikin duniya, ko ma ya jawo durkushewar tattalin arzikin gaba daya.
- Kasuwannin hada-hadar kudi za su fuskanci mummunar faduwa, kuma ma ba za a iya dogaro da zinariya ko dala a yayin rikicin ba.
Mahangar Edita:
Yayin da duniya ke addu’ar samun kwanciyar hankali, yana da muhimmanci a fahimci illolin da kowanne daga cikin wadannan yanayi ka iya haifarwa, musamman ga kasashen da ke dogara da makamashi da harkokin kasuwancin waje.
Idan har matsin lamba ya ci gaba a tsakanin kasashen biyu, to ko ma ba a shiga yaki ba, hakan ka iya jefa duniya cikin sabon yanayi na hauhawar farashi da tabarbarewar tattalin arziki.
Isra'ila ta kashe sabon hafsan sojin Iran
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sojojin Isra’ila (IDF) sun tabbatar da cewa sun yi nasarar kashe Ali Shadmani, sabon babban hafsan sojojin Iran, a wani hari ta sama da suka kai birnin Tehran.
An kashe Shadmani, wanda shi ne babban kwamandan soji kuma mai ba Ali Khamenei shawara ta kusa, bayan bayanan sirri ingantattu da Isra’ila ta samu.
Kafin rasuwar sa, Ali Shadmani ya kasance jagoran ayyukan yaƙi da harba makamai masu linzami kan kasar Isra’ila, kuma ya samu nasararori da dama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng