Ana saura Kwana 2 Sallah, Farashin Gas din Girki Ya Yi Tashin Gwauron Zabi a Najeriya
- Ƙungiyar dillalan gas din girki ta ce farashin 1kg na gas din ya haura N1,500, lamarin da ke ƙara jefa ‘yan Najeriya cikin wahala
- Sai dai, wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa yanzu farashin 1kg na gas din girki ya yi tashin gwauron zabi har zuwa N2,000
- NALPGAM ta yi gargaɗin cewa idan gwamnati ba ta ɗauki matakin gaggawa ba, za a fuskanci ƙarancin gas da tashin farashin abinci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Ƙungiyar masu sayar da iskar gas din girki ta Najeriya (NALPGAM) ta nuna damuwa kan yadda ake fama da ƙarancin gas da kuma tashin farashinsa a Najeriya.
Ƙungiyar ta ce wannan matsala na iya haddasa ƙarancin gas tare da ƙara jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin matsin tattalin arziki.

Source: Getty Images
Farashin gas din girki ya nunka kudinsa
A cewar ƙungiyar, yanzu farashin 1kg na gas ya haura N1,500 yayin da ‘yan kasuwa ke sayen ton 20 na gas tsakanin N25.2m zuwa N26.2m gwargwadon wurin da suke, in ji rahoton Punch.
Rahoton jaridar ya bayyana cewa wasu dillalai ma suna sayar da 1kg na gas din girki tsakanin N1,600 zuwa N2,000.
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa farashin 1kg na gas din girki ya tashi daga ƙasa da N1,000 zuwa sama da N1,500 cikin ƙanƙanin lokaci.
A cikin wata sanarwa da shugaban NALPGAM, Edu Inyang, tare da sakatarenta, Bassey Essien suka sanya wa hannu, ƙungiyar ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Sun ce:
“’Yan Najeriya sun wayi gari suna sayen gas a farashi mai tsanani da ya haura N1,500, yayin da 'yan kasuwa ke biyan sama da N25m domin sayen ton 20 na gas din.”
Tsadar gas ya jefa 'yan Najeriya a damuwa
NALPGAM ta ce tashin farashin gas din girki ya jefa iyalai masu ƙaramin ƙarfi, masu sana’ar girki da ƙananan ‘yan kasuwa cikin mawuyacin hali.
Ta bayyana cewa hakan na rusa ƙoƙarin gwamnati wajen ƙarfafa amfani da makamashi mai tsafta a Najeriya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan
"Suna mini fatan mutuwa"; Shugaba Tinubu ya fadi masu hannu a matsalar rashij tsaro
A cewar ƙungiyar, 'yan kasuwar gas din girki na fama da matsalar samun kaya saboda ƙarancinsa, tsadar ajiya, matsalar sufuri da hauhawar kuɗin gudanar da kasuwanci.

Source: UGC
NALPGAM ta yi gargadi ga gwamnati
NALPGAM ta yi gargadin cewa idan gwamnati ba ta magance matsalar cikin gaggawa ba, ƙasar na iya fuskantar ƙarin tashin farashin abinci da rugujewar ƙananan 'yan kasuwar gas.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa matsalar na iya haddasa asarar ayyukan yi, rage zuba hannun jari da kuma kawo cikas ga manufofin Najeriya na amfani da makamashi mai tsafta.
Farashin gas din girki a Janairu
A wani labari, Legit Hausa ta ruwaito cewa farashin gas din girki ya rage kudi a watan Janairun 2026, bayan an shafe watanni ana fuskantar karancinsa a kasuwanni.
A makon farko na Janairu, an sayar da kilogiram ɗaya na gas din girki tsakanin N1,000 zuwa N1,400, ya danganta da yanki da kuma mai sayarwa.
Shugaban ƙungiyar masu sayar da iskar gas din girki (LPGAR) na ƙasa, Ayobami Olarinoye, ya bayyana cewa yanayin kasuwar ya fara daidaita yanzu.
Asali: Legit.ng
