An Tafka Kuskure: Gidan Redio a Birtaniya Ya Sanar da Mutuwar Sarki Charles III
- Wata tashar rediyo a Birtaniya ta nemi afuwa bayan kuskuren na’ura ya sanar da mutuwar Sarki Charles III a ranar Talata
- Manajan tashar, Peter Moore, ya bayyana cewa tsarin sanar da rasuwar sarki ya kunna ba da gangan ba saboda matsalar kwamfuta a ofishinsu da ke Essex
- Bayan sanarwar kuskuren, tashar ta dakatar da shirye-shiryenta na wani lokaci kafin dawo da watsa shirye-shirye tare da neman afuwar Sarki da masu sauraro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
London, Birtaniya - Wata tashar rediyo a Birtaniya mai suna Radio Caroline ta nemi afuwa bayan kuskuren kwamfuta ya sa aka sanar da mutuwar Sarki.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa tashar ta sanar a ranar Talata da rana cewa Sarki Charles III ya yi bankwana da duniya.

Source: Getty Images
Charles III: An sanar da mutuwar sarki

Kara karanta wannan
Iran da Amurka: An samu sauyin farashin mai a duniya yayin da ake tattaunawar sulhu
Manajan tashar, Peter Moore, ya wallafa a shafin gidan rediyon a Facebook cewa tsarin sanar da rasuwar Sarki wanda gidajen rediyo ke ajiyewa domin gaggawa ne ya kunna bisa kuskure.
Ya ce bayan sanarwar, tashar ta yi shiru kamar yadda doka ta tanada idan sarki ya rasu, lamarin da ya sa suka gano matsalar cikin gaggawa.
Moore ya bayyana cewa tashar ta dawo da shirye-shiryenta tare da gabatar da neman afuwa kai tsaye saboda firgicin da sanarwar ta jawo wa masu sauraro da fada.
Ya kara da cewa Radio Caroline ta taba yada sakonnin Kirsimeti na sarauniya da kuma sarki, kuma suna fatan ci gaba da yin hakan nan gaba.
Rahoton bai bayyana tsawon lokacin da aka dauka kafin gano kuskuren ba, amma an ce an cire sake sauraron shirin na ranar Talata daga shafin tashar.
Lamarin ya faru ne yayin da Sarki Charles III da sarauniya Sarauniya Camilla ke ziyara a Arewacin Ireland inda suka halarci wasannin gargajiya da taruka.

Source: Getty Images
Sarkin da matarsa sun kuma ziyarci yankin Titanic Quarter da ke Belfast inda suka kalli rawa tare da dandana giya irin ta Irish whiskey a ziyarar tasu.
Takaitaccen tarihin gidan rediyon Carolina
An kafa Radio Caroline ne a shekarar 1964 a matsayin tashar rediyon ‘pirate’ wacce ke gudanar da shirye-shirye daga jiragen ruwa kusa da gabar tekun Ingila.
Bayan dokar shekarar 1967 da ta tilasta rufe irin wadannan tashoshi, rediyon ya ci gaba da aiki lokaci-lokaci kafin dakatar da watsa shirye-shiryen teku baki daya a 1990.
Tashar da sauran makamantansu sun zama abin koyi ga fim din barkwanci mai suna The Boat That Rocked wanda aka saki a 2009 tare da jarumai ciki har da Bill Nighy.
Trump ya yaba wa Sarki Charles na Ingila
Mun ba ku labarin cewa Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce mahaifiyarsa Mary Anne MacLeod Trump ta kasance mai matuƙar son gidan sarautar Birtaniya.
Trump ya ce mahaifiyar tasa na kallon duk wani bikin sarauniya a talabijin inda ya ce har nuna kauna take yi ga Sarki Charles a baya.
Shugaban Amurkan ya bayyana cewa mahaifiyarsa tana cewa Yarima Charles yana da kyau sosai tun yana matashi a wancan lokaci.
Asali: Legit.ng
