‘Zaben Fitar da Gwani Ya Tabbatar da Kaunar da Yan Najeriya Ke Yi ga Tinubu’
- Tsohuwar minista, Nkeiruka Onyejeocha ta yabawa shugabannin APC kan yadda aka gudanar da zaben fidda gwani cikin lumana
- Onyejeocha ta bayyana cewa yawan fitowar jama’a a zaben APC alama ce da ke nuna karin amincewa da salon shugabancin Bola Tinubu
- Tsohuwar ministar ta bukaci ‘yan APC da sauran ‘yan Najeriya su ci gaba da marawa gwamnatin Tinubu baya domin cimma manufofinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohuwar karamar ministar kwadago da samar da ayyukan yi, Nkeiruka Onyejeocha, ta yi martani kan zaben fitar da gwani na shugaban kasa.
Onyejeocha ta yabawa shugabannin jam’iyyar APC bisa yadda aka gudanar da zaben fitar da gwani na shugaban kasa cikin kwanciyar hankali.

Source: Twitter
Onyejeocha ta bayyana haka ne bayan duba yadda aka gudanar da zaben a mazabar Isuikwuato/Umunneochi inda ake hasashen za ta zama ‘yar takarar APC a 2027, cewar Tribune.
An yabawa yan Najeriya kan zaben fitar da gwani
Tun da farko, tsohuwar ministar ta kada kuri’arta a mazabar Ezingodo tare da shugabannin jam’iyya da magoya baya yayin gudanar da zaben fidda gwani.
Bayan zagaya rumfunan zabe a yankin, Onyejeocha ta nuna gamsuwa da yawan mutanen da suka fito domin kada kuri’a a zaben APC.
Ta bayyana cewa irin wannan yawan fitowa alama ce ta yadda jama’a ke kara amincewa da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
A cewarta, goyon bayan da aka nuna wa Tinubu ya tabbatar da yadda mutane ke yaba wa salon shugabancinsa da manufofinsa na ci gaban kasa.

Source: Twitter
Tsohuwar minista ta bayyana shirin gwamnatin Tinubu
Onyejeocha ta ce shirin gwamnatin Tinubu mai suna Renewed Hope Agenda na da manufar sake farfado da Najeriya domin samun ci gaba mai dorewa.
Ta bayyana shugaban kasar a matsayin shugaba mai hangen nesa wanda ke kokarin inganta rayuwar ‘yan Najeriya da bunkasa tattalin arziki.
Ta kara da cewa Najeriya za ta kai matsayin da ake buri idan aka ci gaba da mara wa manufofin gwamnatin Tinubu baya a fadin kasa, cewar rahoton Punch.
Tsohuwar ministar ta kuma bukaci ‘yan APC da sauran ‘yan Najeriya su hada kai domin tabbatar da nasarar manufofin gwamnatin yanzu.
A cewarta, hadin kai da cikakken goyon baya daga jama’a ne zai taimaka wajen tabbatar da sauye-sauyen da gwamnati ke kokarin aiwatarwa.
Ta jaddada cewa ci gaba da marawa gwamnatin baya zai taimaka wajen karfafa kokarin da ake yi na sauya fasalin Najeriya da samar da ci gaba.
Tinubu ya yi nasara a Kano da Borno
Mun ba ku labarin cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a zaben fitar da gwani da aka gudanar a sassan Najeriya baki daya.
Majiyoyi sun ce shugaban ya samu kuri’u kusan miliyan daya a zaben fitar da gwani na APC a jihohin Kano da Borno.
A Kano, Gwamna Abba Kabir ya fadi yawan kuri'u da Tinubu ya samu da kuma abin da abokin takararsa Stanley Osifo ya samu.
Asali: Legit.ng

