Iran Ta Sake Yin Luguden Wuta kan Birnin Tel Aviv, Isra'ilawa 8 Sun Bakunci Lahira
- Iran ta kai hari da makamai masu linzami kan Isra'ila, inda aka ce mutane takwas sun mutu a birnin Tel Aviv a ranar Litinin, 16 ga Yuni
- Sai dai a hannu daya, Isra'ila ta gargadi mazauna Tehran da suka haura mutane 330,000 da su gaggauta barin garin kafin ta kai farmaki
- Isra'ila ta kuma shaida cewa ta sami cikakken rinjaye a sararin samaniyar Iran, inda ta ce ta lalata wuraren harba makamai 120 na kasar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Israel — Iran ta harba jerin gwanon makamai masu linzami kan kasar Isra'ila a safiyar Litinin, inda aka ce akalla mutane takwas suka bakunci lahira.
Wadannan hare-haren na zuwa ne yayin da Isra'ila ta gargadi dubunnan daruruwan mutane da ke zaune a tsakiyar Tehran da su gaggauta barin wajen.

Asali: Getty Images
Isra'ila ta gargadi mazauna garin Tehran
Gargadin da Isra'ila ta yi ya zo ne a rana ta hudu ta sabon rikicin da ya barke tsakaninta da Iran, bayan sojojin kasar sun ce sun lalata tsaron Iran, kuma za su iya kai hari kowane lokaci, inji rahoton AP News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojojin kasar ta Isra'ila sun fitar da irin wannan gargadi na bukatar kwashe fararen hula a sassan Gaza da Lebanon kafin kai hare-hare.
Gargadin ya shafi mutane 330,000 a wani yanki na tsakiyar Tehran da ya haɗa da gidan Talabijin na ƙasar da hedikwatar 'yan sanda.
Harin Isra'ila ya lalata gidan talabijin Iran
Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Iran ya ruwaito cewa gidan talabijin mallakin gwamnati ya katse watsa shirye-shiryen kai tsaye ba zato ba tsammani bayan wani hari da Isra'ila ta kai.
Yayin watsa shirye-shiryen, wata mai rahoto ta gidan talabijin ta Iran ta ce ɗakin nazarin labarai ya cika da ƙura bayan "ƙarar farmaki kan ƙasar."
Nan take wata fashewa ta faru, ta lalata allon talabijin din da ke bayan ta yayin da take gaggawar barin wurin, lamarin da ya jawo tsayawar shirye-shiryen.
Sojojin Isra'ila sun ce sun karya lagon Iran
"A wannan lokacin, za mu iya cewa mun sami cikakken rinjaye a sararin samaniyar Tehran," in ji kakakin sojojin Isra'ila Birgediya Janar Effie Defrin.
Sojojin sun ce sun lalata sama da wuraren harba makami mai linzami 120 a tsakiyar Iran, wanda kusan kashi ɗaya bisa uku ne na jimillar wadanda Iran ke da su.
Kafar watsa labaran CBC ta rahoto cewa jami'an sojin Isra'ila sun kuma ce jiragen yaƙi sun kai hari kan cibiyoyin ba da umarni 10 a Tehran mallakin rundunar Quds ta Iran.
Birgediya Janar Effie Defrin ya ce hare-haren Isra'ila "sun zama babbar barazana da kuma karya lagon kasar Iran."

Asali: Getty Images
Harin Iran ya kashe Isra'ilawa 24, ya jikka wasu 500
A halin da ake ciki, Iran ta sanar da cewa ta harba makamai masu linzami kusan 100 kuma ta yi alƙawarin ƙara kai hare-haren ramuwar gayya kan Isra'ila.
Kawo yanzu, an kashe mutane 24 a Isra'ila kuma sama da 500 sun ji rauni, in ji jami'an Isra'ila, bayan da Iran ta harba makamai masu linzami sama da 370 da kuma daruruwan jirage marasa matuƙa.
Rikicin na baya-bayan nan ya fara ne bayan Isra'ila ta kai hari kan manyan shugabannin sojojin Iran, wuraren haɓaka uranium da masana kimiyyar nukiliya, wanda ta ce ya zama dole don dakile abokiyar gabarta gina makamin nukiliya.
Harin Iran ya lalata ofishin Amurka a Isra'ila
A wani labarin, mun ruwaito cewa, makami mai linzami da Iran ta harba wa Isra'ila ya lalata ofishin jakadancin Amurka a Tel Aviv, amma babu wani ma'aikaci da ya jikkata.
Harin Iran martani ne ga hare-haren da Isra'ila ta kai mata a baya. Biranen Tel Aviv da Haifa sun fuskanci ruwan makamai masu linzami.
Amurka ta rufe ofisoshinta da ke Isra'ila, ta kuma umarci 'yan Amurkawa su nemi mafaka, saboda fargabar barkewar babban yaki a nan gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng