Tsohon IGP Adamu Ya Yi Barazana bayan Rasa Tikitin APC na Zaben Gwamnan Nasarawa

Tsohon IGP Adamu Ya Yi Barazana bayan Rasa Tikitin APC na Zaben Gwamnan Nasarawa

  • Tsohon shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu Abubakar, ya sha kasa a zaben fitar da gwani na gwamna na APC a jihar Nasarawa
  • Mohammed Adamu Abubakar ya nuna rashin gamsuwarsa kan sakamakon zaben wanda ya nuna Sanata Ahmed Wadada ya yi nasara
  • Tsohon shugaban 'yan sandan ya nuna cewa zai iya barin jam'iyyar APC idan har ba a saurari kokensa da idon basira ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Nasarawa - Tsohon shugaban rundunar ’yan sandan Najeriya (IGP), Mohammed Adamu Abubakar (mai ritaya) ya yi barazanar fita daga jam’iyyar APC.

Mohammed Adamu Abubakar ya yi barazanar ne idan har ba a saurari kokensu ba game da zargin rashin adalci da aka yi masa a lokacin zaɓen fitar da gwani da aka kammala a jihar Nasarawa.

Mohammed Adamu ya yi barazanar barin APC
Tsohon shugaban rundunar 'yan sanda, Mohammed Adamu Abubakar Hoto: Wali Vanguard
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa Mohammed Adamu, ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a birnin Lafia a ranar Asabar, 23 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi hasashe da ya ga yawan mutanen da suka fito zaben Tinubu

Shafin Wali Vanguard ya sanya bidiyon jawabin da tsohon IGP, Mohammed Adamu Abubakar, ya yi a manhajar Facebook.

Adamu ya yi zargi kan APC

Tsohon shugaban ’yan sandan ya yi zargin cewa an karkatar da sakamakon zaɓen fitar da gwanin domin fifita ɗan takarar da gwamnati ke so, wato Sanata Ahmed Aliyu Wadada.

Mohammed Adamu ya ƙara da cewa shi ne ya lashe zaɓen fitar da gwanin na zabar dan takarar gwamna na APC da gagarumar nasara.

Ya lura cewa ayyana Wadada a matsayin wanda ya lashe zaɓen bai samu amincewar kashi 90 cikin 100 na mambobin APC da masu ruwa da tsaki a jihar ba saboda zargin kura-kurai da suka biyo bayan aikin.

Tsohon shugaban 'yan sandan ya buƙaci kwamitin ƙararrakin zaɓe da shugabancin jam’iyyar na ƙasa da su sauya sakamakon domin ba shi nasara, yayin da ya nuna yakinin cewa zai samu adalci.

Wace barazana tsohon IGP ya yi?

Sai dai kuma, ya lura cewa idan shugabancin jam’iyyar ya gaza yin adalci a kan lamarin, yana shirye ya koma wata jam’iyyar siyasa ta daban domin cimma burinsa.

Kara karanta wannan

2027: Kakakin majalisar Kwara ya raba gardama a zaben fitar da dan takarar gwamnan APC

“Idan adalci ya yi tasiri, za mu ci gaba da tafiyarmu a cikin APC. Amma kuma, idan aka hana mu adalci, za mu sanar da ku mataki na gaba da kuma tsarin siyasar da za mu tsaya takara a ƙarƙashinsa a zaben gwamna na shekarar 2027."

- Mohammed Adamu Abubakar

Mohammed Adamu ya bukaci APC ta yi masa adalci
Mohammed Adamu Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: Wali Vanguard
Source: Facebook

Adamu ya bukaci a kwantar da hankula

A cewarsa, muradinsa na ceto da kuma gyara fasalin jihar Nasarawa yana nan da rai, kuma ya nuna yakinin cewa tare da goyon bayan al'umma zai tsaya takara kuma ya yi nasara a shekarar 2027 ko dai a ƙarƙashin APC ko kuma kowace jam'iyya ta daban.

Ya buƙaci magoya bayansa da su kwantar da hankulansu, su kasance cikin zaman lafiya, masu bin doka da oda, da kuma jajircewa ga gwagwarmayar samar da adalci da kuma mafi kyawun jihar Nasarawa.

Shugaban majalisa ya rasa tikitin APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dokokin jihar Nasarawa, Danladi Jatau, ya sha kaye a zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC.

Danladi Jatau, ya rasa damar tsayawa takarar kujerar Majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Keffi/Karu/Kokona bayan da ya sha kaye.

Hon. Danladi Jatau ya samu kuri’u 5,873 ne kacal, yayin da abokin takararsa, Hon. Daniel Ogazi, ya lashe zaben da kuri’u 13,083.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng