Jihohin da Tinubu Ya Lashe Zaben Fitar da Gwani na APC da Yawan Kuri'un da Ya Samu
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya lashe jihohi 19 da aka sanar da sakamakonsu a zaben fitar da gwani na shugaban kasa na APC
- Rahotanni daga jihar Borno sun nuna cewa Tinubu ya samu kashi 100 na kuri’un mambobin jam’iyyar APC da aka kada
- Tinubu ya bayyana zaben a matsayin nasarar dimokuradiyya ta cikin gida tare da yabawa gwamnoni da shugabannin jam’iyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya ci gaba da mamaye sakamakon zaben fitar da gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC da aka gudanar ranar Asabar.
Sakamakon da aka tattara daga jihohi daban-daban ya nuna cewa shugaban ya samu gagarumar nasara yayin da ake ci gaba da tattara sauran sakamako daga fadin kasar nan.

Source: Twitter
Jihohin da Tinubu ya lashe
Ga jerin jihohin da Tinubu ya yi nasara da kuma yawan kuri’un da ya samu kamar yadda Arise News ta ruwaito:
- Adamawa — kuri’u 644,149
- Imo — kuri’u 582,960
- Gombe — kuri’u 450,516
- Delta — kuri’u 407,646
- Akwa Ibom — kuri’u 389,197
- Benue — kuri’u 374,787
- Ogun — kuri’u 322,485
- Zamfara — kuri’u 321,579
- Kwara — kuri’u 310,990
- Rivers — kuri’u 280,082
- Bayelsa — kuri’u 277,192
- Yobe — kuri’u 253,804
- Ebonyi — kuri’u 207,579
- Jigawa — kuri’u 206,520
- Kogi — kuri’u 197,370
- Taraba — kuri’u 183,698
- Abia — kuri’u 161,005
- Edo — kuri’u 131,096
- Osun — kuri’u 100,880
- Kano - kuri’u 500,852
- Borno - kuri’u 414,988
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a sanar da cikakken sakamakon jihar Kaduna ba.
Tinubu ya yaba da tsarin zaben APC
Da yake magana da manema labarai bayan kada kuri’arsa a Legas, shugaban kasa ya bayyana cewa tsarin zaben ya nuna dimokuradiyya ta cikin gida.
“Wannan yana nuna ingantaccen tsarin dimokuradiyya na cikin gida. Komai yana tafiya yadda aka tsara," In ji Tinubu

Kara karanta wannan
2027: APC ta raba gardama, ta tsaida 'yan takarar gwamna a jihohin Filato da Adamawa
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar a shafinsa na X, Tinubu ya ce tsarin ya bai wa dukkan mambobin jam’iyyar damar shiga cikin zaben domin tabbatar da gaskiya da adalci.

Source: Twitter
Tinubu ya yabawa gwamnoni da APC
Tinubu ya kuma yabawa gwamnoni da shugabannin APC saboda yadda suka gudanar da shirye-shiryen zaben daga matakin mazabu zuwa kananan hukumomi.
A cewarsa, an gudanar da tantance wakilai da tabbatar da rajistar mambobi cikin tsari da lumana. Shugaban ya ce dimbin magoya bayan da suka fito domin goyon bayansa sun kara masa kwarin gwiwa.
Kuri'un Tinubu a Kano, Borno
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a zabukan fitar da gwani da aka a jihohin Borno da Kano.
Tinubu ya samu jimillar kuri’u 915,840 a zabukan da aka yi na shugaban kasa na jam’iyyar APC a Kano da Borno domin zaben 2027.
A Kano, Tinubu ya samu kuri’u 500,852 inda ya doke abokin takararsa, Stanley Osifo, wanda ya samu kuri’u 2,675 a kananan hukumomi 44 na Kano.s
Asali: Legit.ng
