Iran Ta Harba Makamai Fiye da 100 Isra'ila, Ta Ki Yarda da Tsagaita Wuta

Iran Ta Harba Makamai Fiye da 100 Isra'ila, Ta Ki Yarda da Tsagaita Wuta

  • Iran ta harba makamai fiye da 100 kan Isra’ila a safiyar Litinin, lamarin da ya jawo mutuwar mutane da jikkatar wasu sama da 80
  • Rahotanni sun nuna cewa Isra’ila ta mayar da martani da farmaki a Tehran, inda ta kai hari kan cibiyoyin soji 10 na Quds
  • Kasar Iran ta ce mutane 224 sun mutu a hare haren Isra’ila, ciki har da yara kanana da mata a gine-ginen fararen hula

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Rikicin Isra’ila da Iran ya shiga rana ta huɗu cikin tarzoma da tashin hankali, inda kowanne bangare ke kai wa ɗaya hari ba tare da sassauci ba.

A safiyar Litinin, Iran ta sake harba makamai fiye da 100 kan Isra’ila, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane biyar da jikkatar wasu da dama a ƙasar.

Iran ta ki amincewa da shirin tsagaita wuta a Isra'ila
Iran ta ki amincewa da shirin tsagaita wuta a Isra'ila. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Rahoton Arab News ya nuna cewa duk da kamari da rikicin ke karawa, Iran ta ce babu maganar tsagaita wuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Isra’ila, ana cigaba da ayyukan agaji a kusan duk fadin ƙasar, yayin da aka tabbatar da mutuwar wasu maza da mata huɗu ‘yan shekaru 70 a garin Petah Tikva.

Iran ta kai hari, Isra’ila ta mayar da martani

Ministan kiwon lafiya na Iran, Hossein Kermanpour, ya bayyana cewa mutane 224 sun mutu tun daga ranar Juma’ar da Isra’ila ta fara kai farmaki, inda ya ce kashi 90 cikin 100 fararen hula ne.

Hossein Kermanpour ya ƙara da cewa yara fiye da 30 sun mutu a wani ginin bene mai hawa 14 da ya rushe a Tehran.

Isra’ila ta mayar da martani da farmaki kan cibiyoyin soji 10 da ta ce na kungiyar Quds ne a birnin Tehran.

Haka kuma ta kai hari kan ma’aikatar tsaro da wasu wuraren da ta bayyana a matsayin cibiyoyin shirin nukiliya na Iran.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Isra’ila, Dean Elsdunne, ya ce:

“Muna ganin karara yadda ake kai hari kan fararen hula. Wannan gida guda ne kawai cikin wuraren da dama da aka kai wa hari.”
Netanyahu ya zargi Iran da kai hari kan yara da mata
Isra'ila ta zargi Iran da kai hari kan yara da mata. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tsoro ya mamaye birnin Tel Aviv a Isra'ila

Wata jami'ar agaji, Magen David Adom ta tabbatar da jikkatar mutane 87, ciki har da wata mata ‘yar shekara 30 da ke cikin mawuyacin hali.

Jami’an ceto a kasar Isra'ila sun ce har yanzu suna aikin tono mutane a wasu daga cikin gine ginen da suka rushe.

A Tel Aviv kuwa, ana ci gaba da fuskantar fashe-fashe da girgizar gini sakamakon makaman da ake harbawa da kuma kokarin kawar da su ta hanyar kariya da sojin Isra’ila ke yi.

Iran ba za ta shiga tattaunawa da Amurka ba

Rahoton Reuters ya ce Iran ta shaida wa Qatar da Oman da ke shiga tsakani cewa ba za ta tattauna ko yarda da tsagaita wuta da Amurka ba muddin Isra’ila na ci gaba da kai mata farmaki.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin ƙasashe G7 ke gudanar da taro a Kanada, inda Firaministan Jamus Friedrich Merz ya ce yana fatan taron zai kawo mafita da rage rikicin.

Saudiyya ta goyi bayan Iran kan Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Saudiyya ta goyi bayan Iran yayin da ake cigaba gwabza fada tsakaninta da Isra'ila.

Saudiyya ta yi Allah wadai da harin da Isra'ila ta fara kai wa Iran, lamarin da ya jawo martani daga gwamnatin Iran.

Baya ga haka, Saudiyya ta amince da ba alhazan Iran kulawa ta musamman har zuwa lokacin da za a samu kwanciyar hankali a kasar su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng