Hormuz: Bayan Ruwan Wuta a Isra'ila, Iran Ta Toshe Hanyar kai Mai Kasashen Duniya

Hormuz: Bayan Ruwan Wuta a Isra'ila, Iran Ta Toshe Hanyar kai Mai Kasashen Duniya

  • Dakarun Iran sun ayyana rufe mashigin ruwa na Hormuz, suna cewa babu wani jirgin ruwa da zai bi ta yankin har sai da izini daga gwamnati
  • Wannan mataki na zuwa ne bayan harin da Isra’ila ta kai kan Iran da nufin hana ta mallakar makamin nukiliya
  • Kasashen Turai da hukumomin sufurin jiragen ruwa sun fara gargadin jiragen su da su guji yankin saboda yiyuwar barkewar rikici mafi muni

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Dakarun sojin Iran sun sanar da cewa sun rufe mashigin ruwa na Hormuz, daya daga cikin manyan hanyoyin jigilar danyen mai a duniya.

Sojojin sun bayyana cewa babu wani jirgin ruwa da zai bi ta yankin har sai an samu sahalewa daga gwamnati.

Iran ta rufe tashar ruwan hormuz
Iran ta dakatar da jigilar mai ta Hormuz. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Legit ta gano matakin ne a cikin wani sako da rundunar sojin Iran ta wallafa a X bayan kai hare hare kasar Isra'ila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar, wacce aka fitar a ranar Juma’a, ta ce:

“Mu mabiyan Sayyidina Abbas ne, ko sauro ba zai iya ketare ruwanmu ba tare da izini ba!”

Wannan mataki ya biyo bayan harin da Isra’ila ta kai kan wasu wuraren nukiliya da sansanonin soja a Iran, lamarin da ya haifar da sabon yanayi na tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

Jiragen ruwa sun fara kauracewa yankin

Kafin sanarwar Iran, rundunar sojin ruwan kasa da kasa da Amurka ke jagoranta ta bayyana cewa jigilar kaya ta ci gaba da gudana.

Sai dai duk da haka, rahotanni daga Reuters sun nuna cewa kamfanonin jiragen ruwa na duniya na kokarin kauracewa yankin saboda barazanar da ke kara habaka.

Rahoton ya nuna cewa:

“Mashigin Hormuz hanya ce mai matukar muhimmanci wadda babu wata hanya madadinta.
"Ko da tangarda kadan aka samu kan zirga-zirgar jiragen ruwa na iya janyo tasiri ga tattalin arzikin duniya.”

Kasashen duniya na daukar matakan tsaro

Kasashen Girka da Birtaniya sun riga sun bukaci jiragen ruwan su da su guji tashi ta yankin mashigin Hormuz.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikinsu sun bukaci jiragen su da su sanar da kowace tafiya da suke yi ta yankin.

Haka zalika, Ma’aikatar Harkokin Sufuri ta Birtaniya ta gargadi jiragen ruwa da ke dauke da tutocin UK da su dauki matakan tsaro mafi tsauri idan sun shiga yankin.

Yakin Iran da Isra'ila zai shafi tattalin duniya
Danyen mai ya fara tashi saboda yakin Iran da Isra'ila. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Tasirin tashar ruwan ga kasuwannin man fetur

Masana tattalin arziki sun ce rufe mashigin Hormuz na iya kawo tangarda ga safarar danyen mai a duniya.

Sun bayyana haka ne ganin cewa kaso mafi tsoka na man fetur da ake safara daga Gabas ta Tsakiya na ratsa ta wannan hanya.

Tuni dai farashin danyen mai ya fara tashin gwauron zabo, wanda zai iya yi wa tattalin arzikin kasashe masu dogaro da shigo da mai illa.

Iran ta kai hare hare a kasar Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Iran ta kai munanan hare hare kan Isra'ila a yammacin ranar Juma'a.

Hakan na zuwa ne bayan Isra'ila ta kai hari Iran tare da kashe wasu daga cikin manyan sojojinta a safiyar ranar Juma'a.

Tun da farko dai dama Iran ta ce za ta kai harin ramakon gayya da zai girgiza Isra'ila saboda harin da ta kai mata kan makaman nukiliya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng