'Ba za Mu Bar 'Yan Adawa ba,' Tinubu Ya Magantu kan Zaben 2027

'Ba za Mu Bar 'Yan Adawa ba,' Tinubu Ya Magantu kan Zaben 2027

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta riga ta dauki manyan matakai wajen sake farfado da Najeriya da kawo cigaba
  • Bola Tinubu ya yi gargadin game da abin da ya kira yunkurin wasu ‘yan siyasa marasa wata fayyatacciyar manufa ta mayar da kasar baya
  • Ya fadi haka ne da yake jawabi a wajen karbar takardar shaidar samun takara karkashin tutar jam’iyyar APC a ranar Lahadi a birnin Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, AbujaShugaba Bola Tinubu a ranar Lahadi ya gargadi ‘yan Najeriya da kada su bari ‘yan siyasa marasa wata fayyatacciyar manufa su mayar da kasar baya.

Ya fadi haka ne yayin da 'yan jam'iyyun adawa da suka hada da ADC, PDP da NDC ke kokarin cewa za su kifar da shi a zaben 2027.

Kara karanta wannan

'Dan gwagwarmaya Sowore ya fito takarar shugaban kasa, zai kara da Tinubu a 2027

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu bayan samun tikitin takarar APC. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa Tinubu ya bayyana hakan ne lokacin da aka mika masa takardar shaidar samun takarar APC a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2027.

Gargadin Tinubu kan 'yan adawa

Tinubu ya yi alkawarin karfafa sauye-sauyen da gwamnatinsa ta fara, ya ce zai yi aiki tukuru domin makomar da ‘yan Najeriya suka dade suna fata, tare da daura kasar a kan hanyar da ba za a iya juyawa baya ba cikin wasu karin shekaru hudu.

A kan haka ne ya sanar da cewa ba za su yi sakaci wajen barin 'yan adawa su samu nasara su dawo da Najeriya baya ba bayan kafa tubalin cigaba.

Kiran Tinubu ga 'yan adawa

Shugaba Tinubu ya kuma bayyana shirinsa na tattaunawa da ‘yan adawa da masu sukar gwamnatinsa idan za su hada kai wajen kawo cigaba a kasa.

Da yake jawabi ga shugabannin jam’iyya da magoya bayansa, Tinubu ya ce dimokuradiyya ba ta ginu kan tunani iri daya ba, sai dai a kan bambancin ra’ayoyi da aka gina.

Kara karanta wannan

2027: ADC ta fitar da dan takarar shugaban kasa, ta ajiye Atiku a gefe

Tinubu ya ce rashin jituwa da ‘yan adawa wani bangare ne na dimokuradiyya maimakon a dauke shi a matsayin barazana a siyasa.

Martanin Tinubu da Osifo

Da yake jawabi kai tsaye ga wanda ya kalubalance shi, the Nation ta rahoto shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce:

“Ba ni gaba da kowa, har da Osifo, da ya kashe kudinsa.”

Osifo, wani dan kasuwa daga Jihar Edo, ya biya Naira miliyan 100 domin sayen fom din takarar shugaban kasa na APC kuma ya ki janyewa bayan wani shirin cimma matsaya ya rushe. Ya samu kuri’u 16,503 a fadin kasa.

Stanley Osifo da Bola Tinubu
Stanley Osifo na gaiswa da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tsagin ADC ya zabi dan takara

A wani labarin, kun ji cewa tsagin jam'iyyar adawa ta ADC ya fitar da dan takarar shugaban kasa, Dumebi Kachikwu domin fafatawa a 2027.

Rahotanni sun nuna cewa tsagin jam'iyyar ya sanar da rusa bangaren Sanata David Marka da ke aiki tare da Atiku Abubakar da Nasir El-Rufa'i.

Dumebi Kachikwu ya amince cewa zai yi wa jam'iyyar ADC takara a zaben 2027 domin kifar da Bola Tinubu da kawo cigaba a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng