Rikicin Iran da Isra'ila: Mutane Sun Ji Azaba, Sun Fara Tserewa daga Gidajensu
- Yayin da rana ta fito a Tehran birnin Iran, tsakiyar birnin ya fara zama kufai, yayin da aka ga shaguna da kasuwar Grand Bazaar a rufe
- Mazauna birnin na ƙoƙarin tserewa daga gidajensu domin gudun hare-haren Isra'ila ya rutsa da su, bayan gargadin da IDF ta yi
- Sojojin Isra'ila sun yi ikirarin cewa sun kai "hare-hare" kan sojojin yammacin Iran, inda suka lalata wuraren ajiya da harba makamai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Iran – Yayin da rana ta fara fitowa a safiyar Talata a Iran, yankin tsakiyar birnin Tehran, babban birnin kasar, ya fara zama kufai.
An rahoto cewa an rufe yawancin shaguna a babban birnin yayin da ita ma babbar kasuwar birnin ta tarihi, watau Grand Bazaar take a rufe.

Asali: Getty Images
Mazauna Tehran sun fara tserewa daga gidajensu
Rahoton France 24 ya nuna cewa ba babban al'amari ne kawai yake sa a rufe babbar kasuwar Grand Bazaar, kamar lokacin zanga-zanga ko kuma annobar cutar korona.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kan hanyoyin da ke fitowa daga Tehran zuwa yamma kuwa, an samu cunkushewar ababen hawa, yayin da titin ya cika makil da masu kokarin barin birnin.
Da yawa daga cikin matafiyan sun bayyana cewa suna kan hanyarsu ta zuwa yankin Tekun Caspian ne, inda rahotanni suka ce an samar da barauniyar hanyar barin Tehran cikin sauki.
Birnin Tehran, gida ne ga kimanin mutane miliyan 10, wanda kusan yake daidai da yawan jama'ar Isra'ila gaba ɗaya.
Har yanzu dai ba a san yadda za a iya kwashe mutanen birnin ba yayin da jami'an gwamnatin Iran suke ci gaba da nacin cewa barazanar Isra'ila ko Shugaba Donald Trump ba za ta yi tasiri ba.
'Ta ya za a kwashe mutane daga Tehran?'
Mutane da yawa suna ƙoƙarin tserewa daga Tehran, amma zirga-zirgar ababen hawa na ci gaba da cunkushewa, har ta zarce yadda take a kwanakin farko na yakin.
BBC ta rahoto wani iyali da suka yi tafiyar sa'o'i 14 kafin su fita daga Tehran, maimakon tafiyar sa'o'i uku kacal, kuma a hakan suna ganin sun yi sa'a da suka fita lafiya.
Rahoton ya nuna cewa mutane da yawa, waɗanda suka yi nasarar tserewa daga Tehran, sun nuna damuwarsu game da abokai da 'yan uwansu da har yanzu ba su bar birnin ba.
Da aka tambayi wani a daren ranar Talata ko sun bar Tehran, sai cewa ya yi:
"Hanyoyin sun toshe gaba ɗaya, don haka ba bu amfanin mu bar gida mu hau hanya, amma a karshe mu makale a cunkoson zirga-zirgar da ake gani."

Asali: Getty Images
Isra'ila ta kai hare-hare masu yawa kan Iran
Sojojin Isra'ila sun ce sun aiwatar da hare-hare masu yawa kan sojojin yammacin Iran.
Dakarun Sojojin sun bayyana a cikin wata sanarwa da suka wallafa a shafinsu na X cewa:
"A lokacin hare-haren, an kai hari kan wuraren ajiya da wuraren harba makamai masu linzami. Bugu da ƙari, an kai hari kan ajiyar jirage marasa matuƙa a yammacin Iran."
Kasar Isra'ila ta kashe sabon hafsan sojin Iran
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sojojin Isra'ila (IDF) sun ce sun kashe Ali Shadmani, sabon babban hafsan sojojin Iran. An kashe shi ne a wani hari ta sama da suka kai Tehran.
An kashe Shadmani, wanda babban kwamandan soji ne kuma mai ba Ali Khamenei shawara, biyo bayan sahihan bayanan sirri da Isra'ila ta samu.
Kafin mutuwar babban hafsan sojin, Shadmani ya jagoranci ayyukan yaƙi da harba makamai masu linzami kan kasar Isra'ila.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng