Yakin Duniya?: Iran Ta Harba Jirage 100 Isra'ila bayan Kashe Mata Manyan Sojoji

Yakin Duniya?: Iran Ta Harba Jirage 100 Isra'ila bayan Kashe Mata Manyan Sojoji

  • Dakarun Isra’ila sun kai hare-hare kan wuraren soja da na nukiliya a Iran, ciki har da tsakiyar birnin Tehran, lamarin da ya tayar da hankali a duniya
  • Ayatollah Ali Khamenei ya yi barazanar cewa Isra’ila za ta fuskanci “mummunar hukunci” bayan kashe manyan hafsoshin soja da masana nukiliya
  • Iran ta mayar da martani da harba jiragen yaki marasa matuki guda 100, yayin da Isra’ila ta ce za ta ci gaba da farmaki muddin ya zama dole

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da cewa ta kaddamar da jerin hare-haren sama kan wuraren soji da na nukiliya a Iran.

Hare haren da Isra'ila ta kai ya haifar da wani sabon salo na tsanani a rikicin da ke tsakanin kasashen biyu.

Iran za ta mayar da martani kan Isra'ila
Iran ta ce za ta yi ramako kan harin Isra'ila. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shugaban Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya wallafa a X cewa Isra'ila za ta dandana kudarta kan harin da ta kai musu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa wasu manyan hafsoshin soja da masana nukiliya shida daga cikin jami’an Iran sun mutu a hare-haren, tare da wasu fararen hula ciki har da mata da yara.

Iran ta mayar da martani zuwa Isra'ila

Bayan hare-haren Isra’ila, Iran ta harba jiragen yaki marasa matuki guda 100 zuwa kasar Isra’ila a wani mataki na ramuwar gayya.

Sai dai rahoton Al Jazeera ya nuna cewa rundunar sojin Isra’ila ta ce tana aiki tukuru don dakile jiragen kafin su isa.

Shugaban gwamnatin Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce za su cigaba da daukar mataki har sai an cimma nasara.

Iran ta bukaci daukar matakin ramuwar gayya

Shugaban kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya bayyana hare-haren a matsayin “laifi” wanda ba za a yafe ba.

Ya ce:

“Isra’ila ta shirya fuskantar mummunan hukunci.”

A garin Qom, ɗaya daga cikin wurare masu tsarki a Iran, daruruwan masu zanga-zanga sun taru suna rera wakokin ƙiyayya ga Isra’ila da yin kira ga gwamnati da ta dauki mataki.

Jiragen sama sun dakatar da zirga zirga

Biyo bayan rikicin, kamfanonin jiragen sama da dama sun dakatar da tashi zuwa da dawowa daga Iran.

Kamfanin jiragen sama na Jamus, Lufthansa, ya sanar da cewa ya dakatar da dukkan jiragen da ke zuwa da dawowa daga Tehran har sai wani lokaci.

Kamfanin jirgin sama na Rasha, Aeroflot, ya bi sahu inda ya soke zirga-zirgar jiragen sa daga Moscow zuwa Tehran, tare da sauya wasu hanyoyi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Amurka ta ce ba ta da hannu a harin Isra'ila kan Iran
Amurka ta ce ba ta da hannu a harin Isra'ila kan Iran. Hoto: Donald J Trump
Asali: Twitter

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce Amurka ba ta da hannu cikin wannan farmaki na Isra’ila.

Rikicin Isra'ila da Falasdinu

Rikicin tsakanin Isra’ila da Falasɗinu na ɗaya daga cikin rikice-rikicen da suka fi dadewa a duniya, kuma yana da asali mai zurfi da ya shafi addini, siyasa da sarrafa ƙasa.

Rikicin ya samo asali ne tun bayan kafuwar ƙasar Isra’ila a shekarar 1948 da ake yiwa kallon haramtaciyya, wanda ya haifar da gudun hijira ga dubban Falasɗinawa daga ƙasarsu ta asali.

Tun daga wannan lokaci, akwai yawan rikice-rikice da fada tsakanin bangarorin biyu, ciki har da yaƙe-yaƙe guda huɗu da Isra’ila ta gwabza da makwabtan Larabawa.

Aikin Hamas a yaki da Isra'ila

Ƙungiyar Hamas, wadda ke da iko a Gaza, na ci gaba da fafutukar 'yantar da Falasɗinu daga mamayar Isra’ila, lamarin da ke haifar da hare-hare daga ɓangarorin biyu.

A cikin shekarun baya-bayan nan, rikicin ya ƙara tsananta, musamman bayan farmakin Hamas kan Isra’ila a watan Oktoba 2023, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.

Isra’ila ta mayar da martani da luguden wuta da hana kayan agaji shiga Gaza, wanda ya janyo fushin duniya kan yadda Isra'ila ta nuna halinta na karar da dangi kan Falasdinu.

Wannan rikici tsakanin Isra’ila da Falasɗinu yana ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka janyo fitintinu a Gabas ta Tsakiya, wanda yanzu ya shafi Iran kai tsaye, yayin da Isra’ila ke kai farmaki kan manyan wuraren Iran.

Birtaniya ta raba gari da Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa Birtaniya ta gargadi Isra'ila kan cigaba da kai hare haren soji a kan Falasdinawa.

Firaminatan Birtaniya ya sanar da yanke cigaba da kulla ciniki da Isra'ila kan kin amincewa da bude hanyoyin kai tallafi Gaza.

Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da matsa lamba ga Isra'ila kan haren haren da ta ke kaiwa kan fararen hula a yankin Falasdinawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng