Gwamnati Ta Fara Yi wa Mutane Allurar Hana Kamuwa da Cutar HIV a Najeriya
- Gwamnatin Anambra ta fara amfani da maganin LEN PrEP domin dakile yaduwar cutar HIV musamman tsakanin masu hadarin kamuwa da ita
- Ana yin sabuwar allurar rigakafin cutar kanjamau (HIV) sau biyu kacal a shekara sabanin magungunan da ake sha kullum don yaki da cutar
- Jihar Anambra na da 2.4% na masu dauke da HIV, mafi yawa a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, kamar yadda rahoto ya nuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Anambra - Gwamnatin jihar Anambra ta fara rabo da amfani da Lenacapavir (LEN PrEP), wata sabuwar allurar rigakafin HIV mai daukar dogon lokaci domin rage yaduwar cutar.
An kaddamar da shirin ne a birnin Awka, inda kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Afam Obidike, ya bayyana cewa wannan wani babban mataki ne a yakin da ake yi da cutar HIV/AIDS.

Kara karanta wannan
2027: Kakakin majalisar Kwara ya raba gardama a zaben fitar da dan takarar gwamnan APC

Source: Getty Images
Muhimmancin rigakafin cutar HIV
Kwamishinan ya ce rigakafi na daga cikin manyan hanyoyin dakile yaduwar HIV a tsakanin al’umma, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito.
Ya kuma gargadi mutane da kada su karkatar ko sayar da allurar saboda an tanade ta ne domin amfanin lafiyar jama’a kawai.
“Muna godiya ga gwamna Chukwuma Soludo saboda goyon bayan da yake bai wa bangaren lafiya da fadada ayyukan ceton rayuka a jihar,” in ji Obidike.
Ya kara da cewa yawan masu dauke da HIV a Anambra na bayyana ne saboda mutane da dama suna zuwa gwaji tare da sanin matsayinsu.
Anambra na da mafi yawan masu HIV a Kudu
Mai kula da shirin yaki da cutar HIV/AIDS ta jihar, Tonia Mbagwu, ta bayyana cewa jihar Anambra na da kaso 2.4 cikin 100 na masu dauke da HIV, wanda shi ne mafi yawa a yankin Kudu maso Gabas.
Jaridar Premium Times ta ruwaito Tonia Mbagwu ta ce sama da mutane 56,000 ne ke rayuwa da cutar HIV a jihar.

Kara karanta wannan
Bayan kai ruwa rana, jam'iyyar APC ta tsaida 'dan takarar gwamnan Yobe a zaben 2027
A cewarta, hakan na nuna bukatar kara daukar matakan wayar da kai da kuma samar da hanyoyin kariya domin dakile yaduwar cutar.
An yaba da sabon tsarin allurar
Babbar daraktar asibitin koyarwa na jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu (COOUTH), Maureen Umeakuewulu, ta ce fara amfani da maganin ya zo a daidai lokacin da ake samun karin masu kamuwa da HIV tsakanin matasa.
Ta yabawa gwamnatin tarayya bisa sanya Anambra cikin jihohin da aka zabo domin fara wannan shiri.
Rahotanni sun nuna cewa sabuwar allurar LEN PrEP ta bambanta da tsofaffin magungunan rigakafin HIV da ake sha kullum.
Ana yin wannan allura sau biyu kacal a shekara, wanda hakan ke bai wa masu amfani da ita saukin kariya daga kamuwa da cutar.
An bayyana cewa ana bayar da allurar kyauta a wasu cibiyoyin lafiya da aka ware a fadin jihar, kamar:
- Asibitin COOUTH da ke Awka
- FMC Onitsha
- Trauma Centre da ke Oba
- Cibiyoyin lafiya na Ukpo da Neni
Asali: Legit.ng