Tirkashi: Makami Mai Linzami da Iran Ta Harba wa Isra'ila Ya Lalata Ofishin Amurka
- Makamai masu linzamia da Iran ta harba wa Isra'ila ya lalata ofishin jakadancin Amurka a Tel Aviv, amma babu wani ma'aikaci da ya jikkata
- Harin Iran martani ne ga hare-haren da Isra'ila ta kai mata a baya inda biranen Tel Aviv da Haifa suka fuskanci ruwan makamai masu linzami
- Amurka ta rufe ofisoshinta da ke Isra'ila tare da umartar Amurkawa su nemi mafaka yayin da ake fargabar barkewar babban yaki a nan gaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Isra'ila - Jakadan Amurka a Isra’ila, Mike Huckabee, ya da cewa makami mai linzami da Iran ta harba wa birnin Tel Aviv ya shafi ofishin jakadancin Amurka na kasar.
Mike Huckabee ya ce ofishin jakadancin Amurka a Tel Aviv ya lalace sakamakon fashewar makamin na Iran, amma babu wani ma’aikacin Amurka da ya jikkata.

Asali: Getty Images
Harin Iran kan Isra'ila ya shafi ofishin Amurka
A cikin sanarwa da ya fitar ta shafinsa na X, Mike Huckabee ya ce an rufe ofishin jakadancin, tare da umartar 'yan Amurka su nemi mafaka, yayin da yankin ke ƙara fuskantar hare-hare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jakadan ya shaida cewa harin wani ɓangare ne na jerin rukunan makamai masu linzami da Iran ta harba zuwa ga biranen Isra’ila, ciki har da Tel Aviv, Haifa, da Petah Tikva.
A cewarsa, hare-haren wani martani ne ga hare-haren da Isra’ila ta kai kan ababen more rayuwa na soja da na makamashin nukiliyar Iran.
Hotuna daga AFP sun nuna yadda gine-gine suka kama da wuta a Tel Aviv, inda sojojin Isra’ila suka yi kira ga mazauna yankin da su nemi mafaka don tsira da rayukansu.
Asalin rikicin: Harin Isra'ila da martanin Iran
Wannan fashewar makamai mai linzami da Iran ta harba ya biyo bayan wasu manyan hare-hare da Isra’ila ta kai wa Iran din tun a ranar 13 ga Yuni.
A yayin farmakin, ta mafani da jiragen sama masu sakin bama-bamai, an ce Isra'ila ta farmaki wuraren da Iran ke hada nukiliya tare da kashe manyan kwamandoji da masana kimiyya.
Sai dai Iran ta yi martani mai zafi, da ta yi wa lakabi da “True Promise 3,” wanda ya haɗa da harba makamai 100.
Yayin da aka ce matakan tsaron Isra'ila sun lalata wasu daga cikin makaman, sai dai an ce akwai wadanda suka tsallake, inda suka yi barna ga gidaje da ababen more rayuwa na Isra'ila.
Hukumomin Isra’ila sun ce aƙalla mutane 24 ne suka mutu, sannan sama da 90 suka ji rauni, yayin da Iran ta tabbatar da rasa rayuka 224 a hare-haren Isra’ila, inji rahoton Daily Mail.
Duk da cewa an shafe shekaru ana rikici tsakanin Iran da Isra'ila, amma ana ganin wannan sabon rikicin zai iya jawo barkewar yakin Gabas ta Tsakiya.

Asali: Getty Images
Matsayin Amurka da neman ayi sulhu
Mike Huckabee, wanda ke goyon bayan Isra’ila sosai, ya jaddada cewa babu hannun Amurka a hare-haren farko da aka kai Iran ba, amma ya ce Shugaba Donald Trump ya nemi a yi sasanci.
A rahoton da aka samu, Shugaba Trump, ya hana shirin kashe Shugaban Iran, Ayatollah Ali Khamenei, tare da yin kira ga bangarorin biyu da su zauna kan teburin sulhu.
Reuters ta rahoto cewa Amurka ta taimaka wajen lalata wasu makamai masu linzami da Iran ta harba wa Isra'ila, amma har yanzu ba ta yi yunkurin shiga fadan kai tsaye ba.
A gefe guda, shugabannin Iran sun yi alkawarin mayar da martani mai ƙarfi, yayin da Shugaba Masoud Pezeshkian ya ƙi amincewa tattaunawar tsagaita wuta a halin yanzu.
Kasar Saudiya ta yanke alaka da Isra'ila
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Saudiyya ta sake jaddada matsayarta na cewa ba za ta kulla huldar jakadanci da Isra'ila ba har sai an bai wa Falasdinu cikakken 'yanci da cin gashin kai.
Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, ya bayyana cewa Saudiyya na fatan Falasdinu ta samu 'yanci na zama kasa, sannan Gabashin Kudus ya zama babban birninta.
Wannan bayani ya fito ne a yayin bude taron majalisar Shura na tara, inda Yarima Salman ya wakilci Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz Al Saud.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng