Isra'ila Ta Yi wa Iran Babbar Barna, An Kashe Babban Hafsan Sojoji, Ali Shadmani
- Sojojin Isra'ila (IDF) sun tabbatar da cewa sun kashe Ali Shadmani, sabon babban hafsan sojojin Iran, a harin sama da suka kai Tehran
- An kashe Shadmani, babban kwamandan soji kuma mai ba Ali Khamenei shawara, bayan sahihan bayanan sirri da Isra'ila ta samu
- Kafin mutuwar babban hafsan sojin, Shadmani ya jagoranci ayyukan yaƙi da harba makamai masu linzami kan kasar Isra'ila
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Isra'ila – A ranar Talata, sojojin Isra'ila (IDF) suka sanar da cewa sun yi nasarar kashe Ali Shadmani, sabon babban hafsan sojojin Iran.
An kashe Shadmani, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin soji na Iran yayin wani hari ta sama da Isra'ila ta kai da daddare kan wata hedikwata da ke tsakiyar Tehran.

Asali: Getty Images
Isra'ila ta kashe hafsan sojojin Iran
A cikin wata sanarwa da sojojin Isra'ila suka raba a shafin su na X, sun ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A karo na biyu cikin kwanaki 5 – IDF ta kawar da babban hafsan sojojin Iran a lokacin yaki, ya kasance babban kwamandan soji na gwamnatin.
"An kashe Ali Shadmani, babban jami'in soji na Iran kuma babban mai ba Khamenei shawara kan harkokin soja, a harin IAF a tsakiyar Tehran, biyo bayan sahihan bayanan sirri."
An tabbatar da cewa Iran ta gudanar da harin ne biyo bayan sahihan bayanan sirri da ta samu, kuma ta yi amfani da damarta wajen hallaka ɗaya daga cikin manyan jami'an sojin Iran.
Kadan daga ayyukan marigayi Ali Shadmani
Ali Shadmani ya fara aiki a matsayin babban hafsan sojojin Iran kuma kwamandan hukumar gaggawa ta sojoji a farkon wannan watan, bayan mutuwar Alam Ali Rashid.
Idan ba a manta ba, an kashe Alam Ali Rashid a farkon hare-haren Isra'ila, wanda ta yi wa take da Operation “Am Kalavi.” ta kai Iran.
Karkashin jagorancin Shadmani, hukumar kai daukin gaggawa ta "Khatem Al-Anbiya" ce ke da alhakin sarrafa ayyukan yaƙi da amincewa da shirye-shiryen kai hari kan Isra'ila.
Kafin kara masa matsayi, Shadmani ya yi aiki a matsayin mataimakin kwamandan hukumar kuma ya jagoranci sashen ayyukan rundunar sojin Iran.
A tsawon lokacin aikinsa na soja, ya taka muhimmiyar rawa wajen daidaita harba makamai masu linzami, hare-haren jirage marasa matuƙa, da sauran hare-haren da aka kai Isra'ila.

Asali: Getty Images
An ji fashe-fashe a Tabriz a kasar Iran
An ji fashe-fashe guda biyu a ranar Talata a birnin Tabriz na Arewa maso Yammacin Iran, kamar yadda kafofin yada labarai na gida suka ruwaito yayin da Iran da Isra'ila ke musayar wuta na kwana na biyar.
Jaridar France 24 ta ruwaito cewa:
"Fashe-fashe guda biyu sun faru a Tabriz da tazara ta minti biyar."
Yayin da ya wallafa faifan bidiyon Tabriz, kamfanin dillancin labarai na Times of Israel ya ruwaito cewa:
"An ga hayaki mai yawa ya tashi sama a kusa da Tabriz a safiyar Talata bayan fashewar wani abu."
Iran ta yi luguden wuta kan birnin Tel Aviv
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Iran ta kai hari da makamai masu linzami kan Isra'ila, inda aka ce mutane takwas sun mutu a birnin Tel Aviv a ranar Litinin, 16 ga Yuni 2025.
Sai dai a hannu guda, Isra'ila ta gargadi mazauna Tehran da suka haura mutane 330,000 da su gaggauta barin garin kafin ta kai farmaki.
Isra'ila ta kuma shaida cewa ta sami cikakken rinjaye a sararin samaniyar Iran, inda ta ce ta lalata wuraren harba makamai 120 na kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng