"Ni ma na Rame": Tinubu Ya Amince Manufofinsa Sun Jefa Ƴan Najeriya a Wahala
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince cewa sauye-sauyen tattalin arziki sun jawo wa kowa wahala a Najeriya, har da shi kansa
- Ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke amincewa da sake takarar shugaban kasa a jam’iyya mai mulki APC a babban zaben 2027
- Tinubu kara da cewa kamar yadda sauran yan Najeriya ke cikin wani hali, shi da kansa ya rasa barci kuma ya yi rama saboda matasalolin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta aiwatar sun jawo wa ‘yan Najeriya wahala, kuma shi ma bai tsira daga irin wannan hali ba
Tinubu ya bayyana haka ne ranar Lahadi, 24 ga watan Mayu, 2025 yayin da ya karɓi tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC domin sake tsayawa takara a zaben shekarar 2027.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa da yake jawabi ga shugabannin jam’iyya da magoya baya a cibiyar taro ta Bola Tinubu da ke Abuja, ya ce ya san irin wahalar da ake sha sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnati ta kawo.
Ina rasa barci - Tinubu
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa yana rasa barci saboda tarin matsalolin da suka saka yan kasar nan a gaba, wanda hakan ya jawo shi ma ya rame.
Ya ce:
“Na san abin da ake buƙata domin gyara ƙasar nan da muka tarar a lalace. Idan kun rasa barci, ni ma na rasa wani ɓangare. Idan kun rame, ni ma na rame.”
Tinubu ya ƙara da cewa tun a shekarar 2022 ya nemi shugabancin ƙasar, kuma ‘yan Najeriya suka ba shi goyon baya.
A cewarsa:
“Amma akwai abu guda da kullum nake tunawa da shi: a shekarar 2022 na nemi wannan aiki. Dukkaninku kun mara min baya kuma na samu. Don haka dole ne na yi aikin.”
Tinubu ya karɓi tikitin APC na 2027s
Yayin karɓar tikitin takarar shugaban kasa na APC, Tinubu ya nuna godiya ga jam’iyyar bisa sake ba shi damar neman wa’adi na biyu.
Ya ce:
“Ina karɓar wannan takara cikin tawali’u da godiya ga babbar jam’iyyarmu ta APC domin sake tsayawa takara a zaben shugaban kasa na 2027.”

Source: Facebook
Shugaban ya kuma bayyana cewa ya bi yadda zaɓen fitar da gwanin ya gudana a sassa daban-daban na ƙasar nan ta talabijin bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a Legas.
Tinubu ya ce ganin yadda dimbin jama’a suka fito a Kano da Kaduna da kuma yadda aka gudanar da zaɓen cikin lumana ya ba shi ƙwarin gwiwa.
Tinubu ya tara kuri'a a Kano Borno
A baya, kun samu labarin cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a zaben fitar da gwani da aka gudanar a dukkanin jihohin Najeriya gabanin sake tsayar da shi takara a zaben 2027.
Majiyoyi sun ce shugaban ya samu kuri’u kusan miliyan daya a zaben fitar da gwani na APC a Kano da Borno, yayin da ya samu kuri'a mai yawa a sauran jihohin kasar nan da aka yi zaben
A Kano, Gwamna Abba Kabir ya fadi yawan kuri'u da Tinubu ya samu da kuma abin da abokin takararsa Stanley Osifo ya samu bayan jama'a sun fito sun kada kuri'arsu a mazabu daban-daban.
Asali: Legit.ng


