Bayan Lashe Zaben Fitar da Gwani, Kallo Ya Koma kan Tinubu game da Kujerar Shettima

Bayan Lashe Zaben Fitar da Gwani, Kallo Ya Koma kan Tinubu game da Kujerar Shettima

  • Shigaba Bola Tinubu ya samu tikitin takarar APC ba tare da wata hamayya mai ƙarfi ba, yayin da hankula suka koma kan wanda zai zama mataimakinsa
  • Masu sharhi sun bayyana Kashim Shettima a matsayin mataimaki mai biyayya sosai, wanda ke fahimtar manufofin gwamnatin Tinubu
  • Duk da rade-radin siyasa da ƙoƙarin sauya mataimaki, ana ganin cire Shettima yanzu zai iya jawo matsala ga Tinubu a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaba Bola Tinubu bai fuskanci wata babbar matsala wajen samun tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ba.

Sabanin shekarar 2022, wannan karo an bayyana lamarin tamkar naɗa shi kai tsaye ne ba tare da hamayya mai ƙarfi ba.

Ana dakon ganin mataimakin Tinubu yayin da ake zargin yana rigima da Shettima
Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Kashim Shettima.
Source: Twitter

A shekarar 2022, Tinubu ya fafata da mataimakin shugaban ƙasa na wancan lokaci, Farfesa Yemi Osinbajo, da tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Mutumina ne': Peter Obi ya yi magana da ake zargin yana gujewa Atiku

Yanzu dai ana ganin shugaban ƙasar yana da cikakken iko a APC, kuma kusan babu wanda zai iya ƙalubalantarsa wajen neman tikitin takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar kafin zaɓen 2027.

Menene makomar kujerar Kashim Shettima

Bayan samun tikitin takarar, tambayar da ta rage ita ce ko Tinubu zai ci gaba da tafiya tare da mataimakinsa, Kashim Shettima, ko kuma zai zaɓi wani daban domin takarar.

A shekarar 2022, an samu wasu ƙorafe-ƙorafe lokacin da Tinubu ya zaɓi Shettima a matsayin mataimakinsa saboda batun tikitin Musulmi da Musulmi wanda ya tayar da muhawara a ƙasa baki ɗaya.

Sai dai yanzu, yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa, akwai alamun cewa Tinubu zai sake tsayawa takara tare da Shettima saboda yadda suke aiki tare cikin fahimta da jituwa.

Wasu masana siyasa sun bayyana Shettima a matsayin mataimakin shugaban ƙasa mafi biyayya cikin kusan shekaru talatin na mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya saboda yadda yake goyon bayan shugaban nasa.

Ana dakon ko Tinubu zai ci gaba da tafiya da Shettima a matsayin mataimaki
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Yadda Shettima ke taka tsantsan da Tinubu

Masu sharhin sun ce Shettima yana bayyana manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu yadda ya kamata ba tare da nuna adawa, rikici ko wata alamar rashin jituwa da shugaban ƙasa ba.

Kara karanta wannan

Dan Ganduje ya fara nema takarar majalisar tarayya a NDC mai adawa

Haka kuma, an ce Shettima ya yi taka-tsantsan wajen kaucewa duk wani kuskure da zai iya haifar da rashin amincewa tsakaninsa da Tinubu a harkokin siyasa da mulki.

Batun tikitin Musulmi da Musulmi ma ya ragu sosai saboda uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, Kirista ce kuma fasto a cocin Redeemed Christian Church of God.

Rahoton ya ce zargin cewa gwamnati na son musuluntar da ƙasa ba zai tsaya ba saboda irin tasirin da uwargidan shugaban ƙasar ke da shi a gwamnati da ayyukan jama’a, cewar Punch.

Ana kuma ganin Tinubu a matsayin gogaggen ɗan siyasa wanda zai yi asarar goyon baya idan ya cire Shettima, duba da irin tasirin mataimakin shugaban ƙasar a Arewa.

Masu lura da al’amura sun ce Shettima yana da magoya baya masu yawa da za su iya tsayawa masa kai da fata wajen tabbatar da nasarar tafiyar siyasarsa a gaba.

Tinubu ya samu daruruwan kuri'a a Kano, Borno

An ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a zaben fitar da gwani da aka gudanar a sassan Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Tikitin Tinubu da Kashim: Malami ya gano abin da zai kawo karshen APC

Majiyoyi sun ce shugaban ya samu kuri’u kusan miliyan daya a zaben fitar da gwani na APC a Kano da Borno.

A Kano, Gwamna Abba Kabir ya fadi yawan kuri'u da Tinubu ya samu da kuma abin da abokin takararsa Stanley Osifo ya samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.