Macron: 'Amurka Ta Mika Tayin Tsagaita Wuta ga Kasashen Isra'ila da Iran'

Macron: 'Amurka Ta Mika Tayin Tsagaita Wuta ga Kasashen Isra'ila da Iran'

  • Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya nemi Isra’ila da Iran su gaggauta dakatar da kai hare-hare kan fararen hula a kasashe juna
  • Ya bayyana bukatar hakan a yayin taron G7, daidai lokacin da Fadar White House ta sanar da cewa Donald Trump zai bar wannan zama
  • Macron ya yi fatan kasashen biyu za su karbi tayin da Amurka ta mika masu na sulhu, wanda bayan wannan ne za a yi tattaunawa mai zurfi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar France – Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya yi kira ga bangarorin Iran da Isra’ila da su gaggauta dakatar da hare-haren da suke kaiwa kan fararen hula a kasashen biyu.

Macron, yayin wani taron G7 da aka gudanar a Kananaskis, Alberta, Kanada, a ranar Litinin 16 ga Yuni, 2025, yayin da aka shafe kwanaki ana musayar wuta a tsakanin kasashen biyu.

Ana ci gaba da musayar wuta tsakanin Isra'ila da Iran
Shugaban Faransa ya ce ana kokarin tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra'ila Hoto: Getty
Asali: Getty Images

Reuters ta wallafa cewa Shugaba Macron ya bayyana cewa akwai wani tayin tsagaita wuta da Amurka ta gabatar domin dakile rikicin da ke kara kamari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Faransa ta nemi sulhu tsakanin Isra’ila da Iran

Times of Israel ta ruwaito Macron ya shaida wa manema labarai cewa akwai tayin da aka yi domin cimma tsagaita wuta, wanda daga nan ne za a fara tattaunawa mai fadi domin warware rikicin gaba daya.

Ya ce:

“Idan Amurka ta iya cimma tsagaita wuta, hakan zai kasance abu mai kyau matuka.”
Shugaban Amurka, Donald Trump
Amurka ta mika tayin tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran Hoto: Donald J Trump
Asali: Getty Images

Macron ya gargadi kasashen duniya da su daina ganin cewa sai ta hanyar farmaki daga waje ne za a iya ceton wata kasa, yana mai cewa:

“Duk wadanda suka taba tunanin cewa za su iya ceto wata kasa ta hanyar jefa mata bama-bamai daga waje, sun kuskure.”

Faransa na dakon amsar Isra’ila da Iran

Shugaban Emmanuel Macron ya bayyana cewa yanzu haka, ana jira a gani ko bangarorin biyu za su amince da tayin sulhu da aka mika musu.

Ya yi wannan bayani ne yayin taron G7, daidai lokacin da Fadar White House ta sanar da cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, duk da dai ya ce ba rikicin Gabas ta Tsakiya ne dalili ba.

Shugaba Macron ya ce:

“Abin da ya rage yanzu shi ne mu gani ko bangarorin za su bi sahun wannan tayin.”

Shugaban Faransa ya kuma bayyana cewa wani yunkuri na kifar da gwamnatin Iran ta addini zai kasance babban kuskure na dabarar siyasa.

Iran ta gano maboyar makaman Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa Hukumomin Iran sun bayyana cewa sun gano wani katafaren sansanin Isra’ila da ake amfani da shi wajen harba jiragen leƙen asiri marasa matuƙa.

Wannan sansani na Mossad yana cikin yankin Shahr-e Rey da ke birnin Tehran, kuma ana zargin shi ne ke ɗauke da kayan aiki na musamman da ake amfani da su wajen kai hare-hare.

A wani mataki na ƙara kare tsaron cikin gida, hukumomin Iran sun cafke mutane fiye da 80 da ake zargi da hannu a leƙen asiri ko goyon bayan Isra’ila yayin da ake ci gaba a yaki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.