Manyan Jami'an Iran da Isra'ila Ta Hallaka a Harin Bazata

Manyan Jami'an Iran da Isra'ila Ta Hallaka a Harin Bazata

A safiyar Juma’ar da ta gabata, Isra’ila ta kaddamar da wani mummunan hari a kan Iran, inda ta kai farmaki kan sansanonin soja, gine-ginen nukiliya da har da gidajen fararen hula.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Iran – Rahotannin sun nuna cewa Isra’ila ta kashe wasu manyan hafsoshin sojin Iran da dama, da kuma wasu fitattun mutane da ke da hannu wajen ci gaban shirye-shiryen nukiliyar kasar.

An samu musayar wuta tsakanin Isra'ila da Iran
Manyan jami'an Isra'ila shida sun rasu a harin Isra'ila Hoto: Getty images
Asali: Getty Images

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim, wanda ke da nasaba da dakarun IRGC, ya tabbatar da cewa wasu masana nukiliya guda shida sun rasa rayukansu a harin.

Kazalika, daruruwan fararen hula ciki har da yara kanana sun mutu, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga wasu daga cikin manyan mutanen da aka tabbatar da mutuwarsu:

1. Isra'ila ta kashe Janar Mohammad Bagheri

BBC ta wallafa cewa Bagheri shi ne babban hafsan hafsoshin tsaron Iran, wanda ke jagorantar dakarun soji da na Revolutionary Guards (IRGC).

Ya shiga IRGC a 1980 yana dan shekara 20, inda tare da dan uwansa suka kafa sashen leken asirin rundunar lokacin yakin Iran da Iraq.

Shugaban Isra'ila Benjamin Netanyahu
Harin da kasar Isra'ila ta kai ya hallaka shugabannin tsaron Iran da masana a fannin nukiliya Hoto: Benjamin Netanyahu
Asali: Facebook

A watan Afrilu, ya janyo cece-kuce bayan wani jawabi a Persepolis inda ya yi kira da a guji yaki da a marawa zaman lafiya baya.

Ana kallonsa a matsayin mai sassaucin ra’ayi idan aka kwatanta da wasu kwamandoji.

A yanzu, Janar Abdolrahim Mousavi, ya maye gurbinsa a matsayin sabon shugaban hafsoshin tsaro.

2. Janar Hossein Salami ya mutu a harin Isra'ila

Janar Hossein Salami, shi ne kwamandan rundunar IRGC kafin rasuwarsa a harin da Isra'ila ta kai kasarsa.

Ya shiga rundunar a 1980 lokacin yakin Iran da Iraq, ya zama mataimakin kwamanda a 2009 sannan aka nada shi kwamanda a 2019.

An san shi da tsaurin ra’ayi kan Isra’ila, ko a bara, ya sha alwashin cewa Iran za ta “bude ƙofofin wuta” idan Isra’ila ko Amurka suka kai hari.

Jaridun gwamnatin Iran sun bayyana cewa Mohammad Pakpour ne sabon kwamandan IRGC.

3. Isra'ila ta kashe Janar Gholamali Rashid

Janar Gholamali Rashid shi ne shugaban babban hedikwatar Khatam-al Anbiya na IRGC, wanda ke hada-hadar dabarun hadin gwiwa na rundunonin sojin Iran.

Ya yi yaki da Iraq a shekarun 1980 kuma ya taba zama mataimakin shugaban hafsoshin tsaro na kasa.

Ali Shadmani ne aka nada a matsayin sabon shugaban wannan runduna, a cewar kafafen yada labaran gwamnati.

4. Amir Ali Hajizadeh ya rasu

Shugaban sashen Aerospace Force na IRGC, Amir Ali Hajizadeh yana kula da shirye-shiryen makaman roka na Iran.

Rundunar tsaron Isra’ila (IDF) ta ce Hajizadeh ya tara manyan kwamandojin IRGC a wani sansani a karkashin kasa domin shirya kai farmaki kan Isra’ila, kafin a kashe su a wani hari da aka kai ginin da suke ciki.

Shi ne ya jagoranci hare-haren roka da Iran ta kai wa Isra’ila a watan Oktoba da Afrilu na bara.

Hajizadeh ya sha suka daga jama’a bayan da ya dauki alhakin harbo jirgin fasinjojin Ukraine a 2020, inda mutane 176 suka mutu.

5. Harin Isra'ila ya kashe Dr. Fereydoon Abbasi

Shi ne shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran tsakanin 2011 zuwa 2013, sannan daga baya ya zama dan majalisa tsakanin 2020 zuwa 2024.

A watan Mayu, ya bayyana a tashar talabijin ta SNN.ir inda ya nuna goyon baya ga kera makamin nukiliya, yana mai cewa zai aiwatar da umarni idan aka ba shi.

6. Masana Nukiliya 6 da suka rasu

Kamfanonin labaran Iran sun bayyana jerin wasu kwararrun masana kimiyyar nukiliya da aka kashe da suka hada da Dr. Mohammad Mehdi Tehranchi, shugaban jami’ar Azad da ke birnin Tehran.

Sai Dr. Abdulhamid Minouchehr, shugaban sashen injiniyan nukiliya na jami’ar Shahid Beheshti Farfesoshi a bangaren injiniyan nukiliya jami'ar Dr. Amirhossein Feqhi da Dr. Ahmad Reza Zolfaghari.

Iran ta kai harin ramuwar gayya Isra'ila

A baya, mun wallafa cewa Majiyoyi sun tabbatar da cewa Iran ta harba makamai masu linzami kan ƙasar Isra’ila a safiyar yau Asabar, a wani hari da aka bayyana a matsayin ramuwar gayya.

Sautin kararrawar barazana da fashewa ya cika wasu sassa na Isra’ila, musamman a birnin Tel Aviv, bayan da Fira Ministan kasar, Benjamin Netanyahu, ya ce yana sa ran jerin hare-hare daga Iran.

Harin Iran na zuwa ne kwana guda bayan da Isra’ila ta kaddamar da wani hari da ba a taba irinsa ba, wanda ya hallaka manyan hafsoshin sojin Iran ciki har da Janar Mohammad Bagheri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.