Netanyahu Ya Yi Waya da Trump, Ya Fadi Abin da Suka Tattauna kan Nukiliyar Iran

Netanyahu Ya Yi Waya da Trump, Ya Fadi Abin da Suka Tattauna kan Nukiliyar Iran

  • Shugaba Donald Trump da Benjamin Netanyahu sun tattauna game da yakin Iran da ake ci gaba da yi a Gabas ta Tsakiya
  • Shugabannin biyu sun amince cewa duk wata yarjejeniya da Iran dole ta rushe cibiyoyin tace sinadarin nukiliya tare da kwashe kayan nukiliyarta
  • Trump ya ce tattaunawa da Tehran na tafiya yadda ake bukata amma ya gargadi cewa ba za a yi kuskure ba kan batun makamin nukiliyar Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce shi da shugaban Amurka Donald Trump sun tattauna kan yaki da Iran.

Netanyahu ya ce sun amince cewa duk wata yarjejeniya da Iran dole ta kawo karshen barazanar nukiliya gaba daya.

Netanyahu ya yi magana da Trump kan yakin Iran
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a birnin Tel Aviv. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin Firayim ministan Isra'ila wanda ya wallafa a X a yau Lahadi 24 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Trump ya yi maganar sulhu da Iran, ya fadi makomar mashigar Hormuz

Netanyahu ya magantu kan nukiliyar Iran

Ya bayyana cewa dole ne a rushe cibiyoyin tace sinadarin nukiliyar Iran tare da kwashe duk kayan nukiliya daga cikin kasar.

Netanyahu ya bayyana hakan ne bayan wata tattaunawa da ya yi da Trump kan yarjejeniyar bude mashigar Hormuz da kuma shirin ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka da Iran.

Ya yaba wa Trump saboda goyon bayan tsaron Isra’ila da kuma hadin gwiwar da kasashen biyu suka nuna wajen tinkarar barazanar Iran.

Trump ya bayyana cewa ya umarci masu tattaunawa daga Amurka kada su yi gaggawar kulla yarjejeniya da Iran.

Ya ce lokaci na hannun Amurka, kuma za a ci gaba da matsin lamba har sai an rattaba hannu kan yarjejeniya mai inganci da za ta hana Iran mallakar makamin nukiliya.

Shugaban na Amurka ya ce tattaunawar da ake yi yanzu ta fi karfi idan aka kwatanta da yarjejeniyar shekarar 2015 da tsohon shugaban kasa Barack Obama ya cimma.

Kara karanta wannan

Iran ta amince da mika muhimmin arzikinta domin yarjejeniya da Amurka

Ya ce ana tafiyar da tattaunawar cikin tsari amma ya gargadi cewa ba za a amince da wata kuskure ba kan shirin nukiliyar Iran.

Iran ta karyata iƙirarin Trump na yarjejeniyar tsananinsu
Sabon jagoran Musulunci a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Iran ta karyata Trump kan yarjejeniya

A gefe guda, jami’an Iran sun yi watsi da wasu bayanan Trump musamman kan batun mashigar Hormuz. Kamfanin dillancin labaran Fars ya ce mashigar tana karkashin ikon Iran kuma kalaman Trump ba su dace da hakikanin abin da ake tattaunawa ba

Wata majiya daga Iran ta shaida wa CNN cewa tattaunawar na iya zama wata babbar dama ta kawo karshen rikici tsakanin Amurka da Iran tare da samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Majiyar ta ce an samu gagarumin ci gaba wajen tsara yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.

Trump ya juyawa Isra'ila baya

A baya, mun ba ku labarin cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana adawarsa ga shirin Isra’ila na kara mamaye yankin Yammacin Kogin Jordan da Falasdinawa ke zaune a ciki.

Wani jami’in Fadar White House ya ce zaman lafiya da kwanciyar hankali a Yammacin Kogin Jordan na da muhimmanci wajen kawo zaman lafiya.

Kasashen Musulmi da dama, majalisar dinkin duniya da wasu kasashen Turai sun yi kakkausar suka kan matakan mamaya da Isra'ila ke dauka a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.