Majalisar Amurka Ta Janye Kokarin Tilasta wa Trump Bin Umarninta a Yaki da Iran
- Jam’iyyar Republican a Majalisar Wakilai ta Amurka ta dakatar da kada kuri’ar takaita ikon yaƙin da Donald Trump yake yi da kasar Iran
- ‘Yan Democrat sun zargi shugabannin Republican da kare Trump daga suka, suna cewa kudirin zai samu goyon bayan jam’iyyu biyu idan aka kada kuri’a
- Dan majalisar New York, Gregory Meeks, ya ce an dage zaben ne saboda shugabanni sun fahimci kudirin zai yi nasara cikin sauki a majalisa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugabannin jam’iyyar Republican a Majalisar Wakilai ta Amurka sun soke kada kuri’ar da aka shirya yi domin takaita ikon yaƙin Donald Trump kan Iran.
An dauki matakin ne bayan alamun cewa Republican za su iya faduwa a zaben saboda rashin halartar wasu ‘yan majalisa masu goyon bayansu.

Source: Getty Images
Kudirin da majalisa ta yi niyyar yi kan Trump
Jam’iyyar Democrat ta dade tana matsa lamba domin hana Trump amfani da ikon soja ba tare da amincewar majalisa kan rikicin Iran ba, cewar CNN.
Dan majalisar New York mai suna Gregory Meeks ne ya gabatar da kudirin, wanda ke shugabantar mambobin Democrat a kwamitin harkokin waje na majalisa.
Manyan shugabannin Democrat sun soki soke zaben, suna zargin Republican da kare gwamnatin Trump maimakon kare muradun al’ummar Amurka gaba daya.
Hakeem Jeffries da wasu shugabannin Democrat sun ce Republican sun tsorata saboda kudirin yana samun goyon bayan jam’iyyun siyasa daban-daban a majalisar kasar.

Source: Getty Images
Dalilin dage kawo kudirin a majalisar Amurka
Gregory Meeks ya ce an dage zaben ne saboda shugabanni sun fahimci cewa kudirin zai samu rinjaye idan aka bar ‘yan majalisa su kada kuri’a.
Ya bayyana cewa karin farashin mai da kayan abinci na daga cikin matsalolin da suka sa wasu Republican suka fara goyon bayan kudirin.
Meeks ya kara da cewa za a sake kawo kudirin bayan hutun 'Memorial Day' da majalisar za ta dawo gudanar da ayyukanta nan gaba, cewar ABS News.

Kara karanta wannan
Atiku ko Amaechi?: ADC ta sanya ranar da za ta tsayar da ɗan takarar shugaban kasa
A makon nan ma majalisar dattawa ta amince da wani kudiri makamancin wannan domin takaita ikon Trump wajen kai harin soja kan Iran.
Sai dai Donald Trump ya dage cewa yakin Iran yana samun karbuwa daga jama’ar Amurka musamman idan aka danganta shi da barazanar makaman nukiliya.
Wani sabon bincike ya nuna kaso 77 cikin 100 na Amurkawa na ganin manufofin Trump sun kara tsadar rayuwa a yankunansu daban-daban.
Amurkawa da dama sun yi ta nuna rashin goyon baya game da yakin da Amurka ke shiga da suke ganin bai kamata ba.
Trump da Netanyahu sun yi 'cacar' baki
A baya, an ji cewa R\rahotanni sun ce an samu sabani mai zafi tsakanin Shugaba, Donald Trump da Firayim minista, Benjamin Netanyahu.
Lamarin ya biyo bayan zargin cewa shugabannin biyu sun samu sabani kan sake kai hari Iran bayan tattaunawar sirri mai tsawo.
Wani rahoto ya bayyana cewa Isra’ila da Amurka sun yi shirin mayar da Mahmoud Ahmadinejad kan mulki bayan kashe Ayatollah Ali Khamenei a farkon yakin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
