China Ta Fito Fili, Ta Fallasa Rawar da Trump Ya Taka a Rikicin Iran da Isra'ila
- Kasar China ta zargi Shugaba Donald Trump da "rura wutar" rikicin Iran da Isra'ila, bayan gargadin da ya yi na kwashe mazauna Tehran
- Isra'ila ta kai hare-hare kan Iran don hana ta nukiliya, wanda ya haifar da fargabar cewa yaƙin na iya fadada a yankin Gabas ta Tsakiya
- China ta kuma bukaci 'yan ƙasarta da su bar Isra'ila saboda ƙaruwar rikici, lalacewar ababen more rayuwa, da yawaitar asarar rayuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
China – China ta zargi Donald Trump da "rura wutar" rikicin da ke faruwa tsakanin Iran da Isra'ila, bayan da shugaban Amurkan ya gargadi mazauna Tehran da su "bar birnin nan take."
Biyo bayan shekaru da dama na ƙiyayya da tsawaitaccen yaƙi, Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare ta sama ba zato ba tsammani a makon da ya gabata kan wurare daban-daban a Iran.

Asali: Twitter
China ta zargi Trump da rura rikicin Isra'ila-Iran
Isra'ila ta ce ta yi hakan ne domin hana abokiyar gabarta mallakar makaman nukiliya, zargin da Tehran ta musanta, kamar yadda Times of India ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barkewar rikicin ya haifar da fargabar faɗaɗawar rikicin a Gabas ta Tsakiya, inda Trump ya buƙaci Iran ta sake dawo wa kan teburin sansanci bayan hare-haren Isra'ila sun kawo cikas ga tattaunawar nukiliyar da ke gudana.
Trump ya kuma fitar da wani gargadi mai ban mamaki a dandalinsa na Truth Social, inda ya ce, "Kowa ya fice daga Tehran nan take!," wanda daga bisani ya goge.
Da aka tambaye shi game da kalaman Trump a ranar Talata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen China, Guo Jiakun, ya ce:
"Hura wuta, zuba mai, yin barazana da ƙara matsin lamba ba zai taimaka wajen rage rikicin ba, sai dai zai ƙara tsananta shi da faɗaɗa shi."

Asali: Getty Images
China ta bukaci 'yan kasarta su fice daga Isra'ila
Ofishin Jakadancin China a Isra'ila a ranar Talata ya kuma buƙaci 'yan ƙasarsa da su bar ƙasar "da wuri-wuri," bayan da Isra'ila da Iran suka ci gaba da musayar makamai masu linzami.
A wata sanarwa da ofishin jakadancin China ya fitar, wadda kafar labaran CGTN ta wallafa, an bukaci 'yan China mazauna Isra'ila da:
"Su bar ƙasar tun da wuri ta hanyar tsallakewa ta iyakokin ƙasa, bisa sharadin za su iya tabbatar da tsaron kansu. Ana ba jama'a shawarar yin kaura zuwa Jordan."
Ofishin jakadancin ya yi gargadin cewa:
"Yayin da rikicin ke ci gaba da ƙaruwa, an lalata yawancin ababen more rayuwa na fararen hula, sannan adadin rayukan da ake rasawa yana ƙaruwa, kuma yanayin tsaron ya ƙara ta'azzara."
Mazauna Tehran sun fara ficewa daga gidajensu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Tsakiyar Tehra, babban birnin Iran, ya fara zama kufai yayin da aka ga shaguna da kasuwar Grand Bazaar a rufe, wanda ba a saba gani ba.
Mazauna birnin na ƙoƙarin tserewa daga gidajensu domin guje wa hare-haren Isra'ila, biyo bayan gargadin da IDF (Sojojin Isra'ila) ta yi.
Sojojin Isra'ila sun yi ikirarin cewa sun kai "manyan hare-hare" kan sojojin yammacin Iran, sun kuma ce sun lalata wuraren ajiya da wuraren harba makamai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng