Bikin Sallah: Yadda Matafiya Za Su Kauce wa Cunkoso a Hanyar Abuja zuwa Kaduna

Bikin Sallah: Yadda Matafiya Za Su Kauce wa Cunkoso a Hanyar Abuja zuwa Kaduna

  • Hukumar kiyaye hadurra ta kasa ta gargadi matafiya da su kiyaye dokokin hanya yayin da cunkoso ya yi tsanani a hanyar Abuja zuwa Kaduna
  • FRSC ta bayyana cewa yankin Nasarawa–Azara tsakanin Katari da Jere ne ya fi fama da cunkoso saboda tafiye tafiyen Sallah da gyaran hanya
  • Hukumar ta ba matafiya shawarar amfani da hanyar Kaduna–Kachia–Maraban Kubacha–Jere–Bwari–Dutse Abuja domin rage wahalar zirga-zirga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A ranar 27 ga watan Mayun 2026 ne ake sa ran za a gudanar da idin babbar Sallah, kuma dubunnan mutane ne ake sa ran za su bi hanyar Abuja zuwa Kaduna don zuwa gida yin bikin sallar.

Hukumar FRSC ta shawarci masu bin hanyar Abuja zuwa Kaduna da su kasance masu hakuri tare da bin dokoki domin kauce wa hatsari da cunkoso a lokacin bukukuwan babbar Sallah.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi karin haske kan zargin shirin sauya sunan Najeriya, rusa shari'ar Musulunci

FRSC ta ce tafiye tafiyen sallah da gyaran hanya sun haddasa cunkoso a hanyar Kaduna zuwa Abuja
Cunkoson ababen hawa a hanyar Kaduna zuwa Abuja. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Akwai cunkoso a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X ranar Lahadi, inda ta ce yawaitar zirga-zirgar Sallah da kuma aikin gyaran hanya sun haddasa cunkoso mai tsanani a wasu sassan hanyar.

A cewar FRSC, yankin da ya fi fama da matsalar shi ne tsakanin Nasarawa da Azara, daga Katari zuwa Jere, inda ake samun jinkirin tafiyar motoci sakamakon cinkoson da direbobin da ke karya dokokin hanya ke haddasawa..

Hukumar ta ce direbobin da ke son wuce na gabansu ta kowane hali da kuma masu tukin ganganci ne suke kara dagula lamarin tare da haddasa hadurra.

“An shawarci masu ababen hawa da su kasance masu hakuri tare da kiyaye dokokin hanya yayin da ake fama da cunkoso sakamakon zirga-zirgar Sallah da aikin gyaran hanya,” in ji sanarwar FRSC.

FRSC ta kara da cewa rashin bin layin mota yadda ya kamata da tuki cikin ganganci suna daga cikin abubuwan da suka fi janyo tsaikon zirga-zirga a hanyar.

Kara karanta wannan

Ana shirin babbar salla, 'yan bindiga sun yi fashin ragunan layya a Kano

Yadda za a kauce wa cunkoso a Abuja-Kaduna

Domin rage cunkoso da taimaka wa matafiya su isa inda za su cikin sauki, hukumar FRSC ta bukaci matafiya tsakanin Kaduna da Abuja da su bi wata hanya ta daban.

Ta ce matafiya za su iya amfani da hanyar Kaduna–Kachia–Maraban Kubacha–Jere–Bwari–Dutse Abuja domin guje wa cunkoso a babban titin Abuja–Kaduna.

Hukumar ta kuma bukaci direbobi su guji tuki a hannun da ba nasu ba, su dauki shawarwarin jami’an kula da zirga-zirga tare da bin dukkan ka’idojin hanya domin kare rayuka da dukiyoyi.

Hukumar FRSC ta bukaci matafiya su kiyaye dokoki tuki a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Jami'an hukumar FRSC suna kokarin kiyaye hadurra da ba direbobi shawara. Hoto: @FRSCNigeria
Source: Twitter

FRSC ta tura jami’ai sama da 30,000

A wani bangare kuma, FRSC ta sanar da fara gudanar da sintiri na musamman a fadin kasar nan domin bukukuwan babbar Sallah na shekarar 2026, in ji rahoton Punch.

Hukumar ta ce ta tura jami’ai sama da 30,000 zuwa manyan hanyoyi da wuraren da ake yawan zirga-zirga domin tabbatar da tsaro da rage hadurra a lokacin bukukuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa

FRSC ta bayyana cewa aikin sintirin zai gudana daga ranar 25 ga watan Mayu zuwa 31 ga watan Mayu, 2026.

Fusatattu sun farmaki ofishin FRSC

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaban FRSC Shehu Mohammed ya yi Allah-wadai da harin da wasu fusatattun mutane suka kai wa ofishinsu.

Wani jami'in kiyaye hadurra da direban tirela sun rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota da kuma harin fusatattun mutane.

Hukumar FRSC ta ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan abin da ya haddasa hatsarin da kuma harin da aka kai ofishinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com