Harin Bam kan biranen Saudiyya: Iran ce da Hizbolla ke son ruguza kasar mu - Saudiyya

Harin Bam kan biranen Saudiyya: Iran ce da Hizbolla ke son ruguza kasar mu - Saudiyya

- Iran kasa ce ta 'yan shi'a, wadda ke son ta kewaye Saudiya daga kowanne yanki

- A yanzu ana ffafatawa ne a Yemen, inda bayan Iran ta sanya Houthi sun mamaye kasar ta Yemen, Saudiyya ke ta kai hari dake ta ruguza Yemen din

- Su kuma Iran suna ta kara ingiza makamai cikin Yemen din don kaima Saudiyyar hari

Harin Bam kan biranen Saudiyya: Iran ce da Hizbolla ke son ruguza kasar mu - Saudiyya
Harin Bam kan biranen Saudiyya: Iran ce da Hizbolla ke son ruguza kasar mu - Saudiyya

Bama-bamai da makamai masu linzami da ake ta harbawa Saudiyya har cikin biranenta daga Yemen suna ta kara kawo barazana ga kasar dake da arzikin mai da ma kuma manyan masallatai na MAkka da Madina garin manzo.

A yanzu dai ma'aikatar tsaron kasar ta Saudiyya tace tana da kwakkwarar shaida dake nuna makaman, duk da cewa daga kudanci ake harbo su ta cikin kasar Yemen, to Houthi ne ke aiko su, kuma sun karbo su ne daga kasar Iran.

Su kuma Iran din sun aika Hizbolla ta Lebanon ne domin koya wa Houthi din aiki da sarrafa manyan makaman domin tayar wa da daulolin larabawa hankali a yakin basasa da ya shekara 1300 da ake yi, tsakanin Sunni da Shia a yankin.

DUBA WANNAN: Wata sabuwar cuta ta bulla a Kano

A yanzu da kasar ta Saudiyyar keda kwakkwarar shaida, wadda dama hakan ake zargi, ba'a san matakin da tayi niyyar dauka ba, shin ko Amurka zata kira, ko kuwa sauran Larabawa, ko ma dai kawai zata yi gaban kanta ne?

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng