"Akwai Matsala": Halin da Musulmin Iran ke ciki bayan Luguden Wutar Isra'ila a Tehran

"Akwai Matsala": Halin da Musulmin Iran ke ciki bayan Luguden Wutar Isra'ila a Tehran

  • Mutane sun fara guduwa suna barin yankunasu a birnin Tehran na ƙasar Iran sakamakon munananan hare-haren da Isra'ila ta kai
  • Rahotanni sun nuna cewa tashin bama-bamai ya tilastawa mutane sama da 300,000 barin birnin Tehran domin tsira da rayukansu
  • Hakan dai na zuwa ne a lokacin da Iran ta fara nuna alamun amincewa da sulhu bayan wasu ƙasaashe sun sa baki ciki har da Saudi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - A wani sauyi mai cike da mamaki da ba a yi tsammani ba, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna aniyarta na amincewa da tsagaita wuta a yakin da take yi da Isra’ila.

Hakan na zuwa ne duk da jiragen yakin Isra’ila na ci gaba da ruguza manyan cibiyoyin soji da na gwamnati a birnin Tehran, har da hedikwatar gidan talabijin na gwamnati.

Mutane sun fara guduwa daga Tehran.
Mutane sun fara guduwa da Isra'ila ta sake kai hari Tehran Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shaidu sun bayyana hare-haren sun girgiza unguwanni, inda mutane suka fara gudu, yara na kururuwa saboda tsananin fashewar da ta afku, rahoton Al-Jazeera.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Halin da mutane ke ciki a birnin Tehran

Wani mazaunin Tehran ya ce:

“Abin da muka gani ba komai bane illa hayaƙi da gilasan da suka fashe. Mutane na gudu, yara na ihu. Mun zaci ƙarshen duniya ne.”

Harin bama-bamai da ake kaiwa ya sa fiye da mutum 330,000 sun fice daga birnin Tehran, yayin da hukumomi suka yi alamar haɗari a kusa da sansanonin sojin Iran.

A gefe guda, kasuwannin duniya sun fara nuna kwarin gwiwa yayin da farashin danyen mai ya sauka da kusan kashi 4% bayan da aka sami rahotanni cewa Iran za ta amince a yi sasanci.

Masu nazarin tattalin arziki sun ce duk da cewa hadarin barkewar yaki a yankin bai kare ba, yunkurin tsagaita wuta ya kwantar da fargabar samun tsaiko a jigilar mai ta mashigar Hormuz.

Alamu sun nuna Iran ta amince da tsagaita wuta

Tattaunawar Iran da wasu kasashen Larabawa kamar Qatar, Saudiyya da Oman na cikin ƙoƙarin da aka yi na kwantar da rikicin, inda suka shiga tsakanin Iran da Isra’ila a sirrance.

Duk da haka, Iran ta ce za ta amince da tsagaita wuta ne kawai idan Amurka ba ta shiga yakin ba.

Rahoton Vanguard ya nuna cewa duk da shirin da ake yi na samar da sulhu, Iran na fuskantar asara mai yawa a muhimman wurarenta.

A safiyar Litinin, Isra’ila ta kaddamar da hare-hare, ta kai farmaki a makaman roka, cibiyoyin da ake zargin na nukiliya ne, da kuma gidan rediyo da talabijin na kasa (IRIB) da ke tsakiyar Tehran.

Hare-haren Isra'ila sun kori mutane a Tehran.
Kasar Iran ta amince a yi zaman sulhu don tsagaita wuta tsakaninta da Isra'ila Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

Mutane sun fara guduwa daga birnin Tehran

Harin da aka kai IRIB ya girgiza gwamnati da al’umma, inda ya katse watsa shirye-shirye na kasa na tsawon sa’o’i, tare da haddasa tashin hankali a birnin.

Mutane da dama sun tsorata, sun fara guduwa daga gidajensu a Tehran yayin da yaƙin ke ƙara ta'azzara tsakanin ƙasashen biyu.

Iran ta naɗa sabon ministan tattalin arziki

A wani labarin, kun ji cewa Iran ta naɗa Ali Madanizadehta a matsayin sabon ministan harkokin tattalin arziki da kudi domin shawo kan matsalolin da ke tunkaro ƙasar.

Daga cikin kalubalen ake sa ran sabon ministan zai tunkara har da hauhawar farashin kayayyaki da kuma faduwar darajar kudin kasar Iran.

Wannan naɗi na zuwa ne watanni bayan an tsige Abdolnaser Hemmati, ta hanyar kada kuri’ar rashin yarda saboda kasa shawo kan matsalolin tattalin arziki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262