Sani Hamza
5699 articles published since 01 Nuw 2023
5699 articles published since 01 Nuw 2023
Mazauna kauyen Dansarai a Katsina sun yi artabu da ‘yan bindiga, inda aka kashe mutane hudu tare da fatattakar maharan. An ce 'yan bindiga sun tsere da suka ji wuta.
Gwamnan Oyo Seyi Makinde ya yi karamin sauyi a majalisar zartarwar jihar, inda ya sauke Toyin Balogun tare da nada Faosat Sanni a matsayin kwamishiniyar mata.
Babban Bankin Najeriya CBN ya soke lasisin wasu bankunan microfinance 46 daga 1 ga Yuli, 2026 saboda rashin cika ƙa’idojin aiki da doka ta tanada.
Hukumar FRSC ta sanar da fara ɗaukar aiki na shekarar 2026 daga 3 ga Yuli, inda za ta ɗauki ma’aikata a matakai uku tare da gargadin jama’a kan masu damfara.
‘Yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda biyu tare da raunata wani a Rivers a wani shingen bincike, yayin da rundunar ta fara bincike don kamo maharan.
INEC ta bayyana cewa jam’iyyun siyasa 9 sun karɓi lambobin shiga domin shigar da bayanan ‘yan takarar zaɓen 2027 na shugaban kasa da majalisar tarayya.
Fitaccen malamin addinin Musulmi, Sheikh Mansur Isah Yelwa ya dawo limanci a masallacin jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi bayan kwana 4 da murabus.
Jihohi biyar da suka hada da Bayelsa, Borno, Kano, Kebbi da Yobe za su samu dala miliyan 15 daga shirin HOPE Governance Programme na Bankin Duniya.
Gwamnatin Tarayya za ta kawo ƙarshen tsarin raba kanana da manyan makarantun sakandare (JSS da SSS) bayan ɗalibai miliyan 20 sun daina karatu a fadin Najeriya.
Sani Hamza
Samu kari