Ta Tabbata Tinubu ba Zai Je Amurka ba, Ya ba Shettima Umarni kan Taron UNGA

Ta Tabbata Tinubu ba Zai Je Amurka ba, Ya ba Shettima Umarni kan Taron UNGA

  • Shugaba Bola Tinubu ya tura Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilce shi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81
  • Shettima zai jagoranci tawagar Najeriya da ta ƙunshi gwamnoni, ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati zuwa birnin New York
  • Babban taron na Majalisar Ɗinkin Duniya zai gudana daga ranar 22 zuwa 28 ga watan Satumba 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya wakilce shi tare da jagorantar tawagar Najeriya zuwa babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 a New York, Amurka.

Hakan ya kawo ƙarshen ce-ce-ku-ce da aka kwashe makonni ana yi kan ko Tinubu zai halarci taron da kansa, wanda ke tattara shugabannin ƙasashe daga sassa daban-daban na duniya.

Kara karanta wannan

Shettima ya yi magana da aka fahimci kalamansa a baibai kan Tinubu

Shettima zai je taron UNGA
Kashim Shettima na hawa jirgin sama Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Kashim Shettima, Stanley Nkwocha, ya fitar a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, 20 ga watan Satumban 2026.

Tinubu ya tafi hutun makonni uku

A watan Yulin shekarar 2026, Jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce Shugaba Bola Tinubu zai halarci taron da kansa.

Jakadan ya ce an yi tanadin wurin zama kusa da Shugaban Amurka Donald Trump domin Tinubu yayin taron na shugabannin ƙasashe.

Sai dai Tinubu ya bar Abuja a ranar 30 ga Agusta domin fara hutun makonni uku a Turai, inda birnin Landan na Birtaniya ya kasance zangonsa na farko kafin ya wuce Faransa.

Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar da cewa Tinubu zai dawo Najeriya bayan kammala hutunsa, lamarin da ya haifar da hasashen cewa ba zai halarci taron Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Amurka ba.

Shettima zai jagoranci tawagar Najeriya

Kara karanta wannan

Babbar magana: An kai korafin dan majalisa gaban NDLEA kan zargin shan hodar iblis

A wata sanarwa da Stanley Nkwocha, ya fitar, fadar shugaban k​asa ta tabbatar da cewa Kashim Shettima ne zai jagoranci tawagar Najeriya.

Sanarwar ta ce tawagar za ta ƙunshi Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, tare da ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati.

Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya

Babban taron muhawarar Majalisar Ɗinkin Duniya na karo na 81 zai gudana daga 22 zuwa 28 ga watan Satumba 2026.

A yayin muhawarar, Kashim Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya, inda zai bayyana matsayar ƙasar da abubuwan da ta fi bai wa muhimmanci kan manyan batutuwan duniya.

Waɗannan batutuwa sun haɗa da ci gaban ƙasa, zaman lafiya da tsaro, bunƙasar tattalin arziki da haɗin gwiwar ƙasashe. Bayan kammala ayyukansa a New York, Kashim Shettima zai dawo Najeriya.

Shettima zai wakilci Tinubu a UNGA
Kashim Shettima tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Shettima ya yaba da shirin NELFUND

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) a matsayin wani muhimmin shiri da ya taimaka wa yaran talakawa wajen samun tallafin kuɗin karatu.

Shettima ya ce Gwamnatin Tarayya ta mayar da NELFUND wani muhimmin shiri wajen rage gibin tattalin arziki da kuma yaɗa damar samun ilimi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng