Yadda Sojojin Najeriya Suka Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Suka Ceto Mutane 1,516

Yadda Sojojin Najeriya Suka Hallaka ’Yan Ta’adda 1,597, Suka Ceto Mutane 1,516

  • Hedikwatar Tsaro ta ce sojoji sun kashe 'yan ta'adda da masu tayar da ƙayar baya 1,597 tare da ceto mutane 1,516 da aka sace daga Janairu zuwa Yuni
  • Sojojin sun gudanar da ayyukan tsaro 14,221 a sassa daban-daban na ƙasar, inda suka ƙwato makamai, alburusai da bama-bamai masu yawa
  • Hedikwatar tsaro ta ce hare-haren sun rage ƙarfin Boko Haram, ISWAP da 'yan bindiga, yayin da mambobi 132 na ƙungiyoyin suka miƙa wuya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojin ƙasar sun kashe 'yan ta'adda da masu tayar da ƙayar baya 1,597 tare da ceto mutane 1,516 da aka yi garkuwa da su a tsakanin watan Janairu da Yunin 2026.

Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, wanda Group Captain Kabiru Ali ya wakilta, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin taron haɗin gwiwar hukumomin tsaro da aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan

Minista ka iya rasa kujerarsa, an kirayi Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 1,597, sun ceto mutane 1,516
Dakarun sojojin Najeriya da ke aikin kakkabe 'yan ta'adda. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Sojoji sun gudanar da ayyukan tsaro 14,221

A cewar Hedikwatar tsaro, dakarun sojin sun gudanar da ayyukan tsaro guda 14,221 ta sama, ƙasa da ruwa a sassa daban-daban na Najeriya, kamar yadda rahoton This Day ya nuna.

Rahoton ya nuna cewa an kai hare-hare da bayanan sirri suka jagoranta, an gudanar da sintiri, farmaki kan maɓoyar miyagu da kuma ayyukan ceto a jihohin Borno, Yobe, Taraba, Katsina, Kwara, Zamfara, Sokoto, Plateau, Benue, Neja, Oyo da Kaduna.

Hedikwatar tsaro ta ce sojoji sun ƙwato bindigogi 451, harsasai 16,726, bama-bamai da na'urorin fashewa (IEDs) guda 161, lamarin da ya rage ƙarfin ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

Wasu 'yan Boko Haram sun miƙa wuya

Haka kuma, an ceto mutane 261 daga maɓoyar Boko Haram da ISWAP, an kashe mayaƙansu 412, sannan an kama wasu 332 tare da ƙwato makamai, babura da dabbobi.

Rahoton ya ƙara da cewa mambobi 132 na Boko Haram da ISWAP sun miƙa wuya saboda matsin lambar da sojoji suka ci gaba da yi musu.

Kara karanta wannan

Bayan shan wuta, mayakin ISWAP na kan kogi ya mika wuya ga jami'an sojoji

Bugu da ƙari, dakarun sun lalata bama-bamai 31 cikin aminci domin kare rayukan jama'a, kamar yadda rahoton Punch ya nuna.

Hedikwatar tsaro ta ta ce an gudanar da ayyukan tsaro fiye da 1,000 kuma an samu nasarori masu yawa.
Wasu dakarun sojojin Najeriya a sansaninsu suna shirin fita aiki. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun ƙarfafa alaƙa da al'umma

Hedikwatar tsaro ta bayyana cewa sojoji sun gudanar da shirye-shiryen zaman lafiya guda 33, shirin wayar da kan jama'a 13 da kuma ganawa 33 da sarakuna da shugabannin addinai domin ƙarfafa haɗin kai da jama'a.

Har ila yau, rundunar ta fitar da sanarwar manema labarai 593, ta karyata rahotannin ƙarya guda 15 tare da wallafa sanarwar faɗakarwa guda 10 domin inganta yaɗa sahihan bayanai.

Hedikwatar tsaro ta jaddada cewa sojoji za su ci gaba da yaƙi da ta'addanci, 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane, masu tayar da ƙayar baya da masu satar ɗanyen mai, tare da roƙon 'yan Najeriya su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro ingantattun bayanan sirri domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Sojoji sun hallaka 'yan ta'adda a Neja

A wani labari, mun ruwaito cewa, hare-haren jiragen yaki na rundunar Operation Fansan Yamma sun kashe 'yan ta'adda da dama a Jihar Neja.

Kara karanta wannan

Ana batun 2027, gwamna Sule ya tono sirrrin APC kan nasarar da ta ke samu

Dakarun sojojin sun yi luguden wuta ta sama ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan motsin sama da 'yan ta'adda 200.

Bayan kashe da dama daga cikin yan bindigar, an kuma lalata wani wurin da ake zargin suna tara kayayyaki da man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com