Sheikh Mansur Isa Yelwa Ya Dawo Limanci a Masallacin ATBU Bauchi, Ya Fadi Dalili

Sheikh Mansur Isa Yelwa Ya Dawo Limanci a Masallacin ATBU Bauchi, Ya Fadi Dalili

  • Sheikh Mansur Isah Yelwa ya sanar da komawarsa limancin masallacin Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa bayan kwanaki hudu da yin murabus
  • Malamin ya ce dama can ya sauka ne saboda rashin amincewa da bai wa wata kungiyar dalibai fili domin gina masallaci a jami’ar
  • Ya ce bayan shawarwari daga malamai da majalisar Shura ta jami’at, ya yanke shawarar janye murabus dinsa domin gujewa wata barnar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Bauchi - Fitaccen malamin addinin Musulmi, Sheikh Mansur Isah Yelwa ya dawo limanci a masallacin jami'ar Abubakar Tafawa Balewa da ke jihar Bauchi.

Wannan na zuwa ne kwanaki hudu bayan da malamin ya sanar da murabus daga limancin masallacin sakamakon ba kungiyar dalibai 'yan Darika fili su gina masallaci a jami'ar.

Sheikh Mansur Yelwa ya dawo limanci a masallacin ATBU Bauchi
Sheikh Mansur Isa Yelwa, limamin masallacin jami'ar ATBU Bauchi. Hoto: Professor Mansur Isa Yelwa
Source: Facebook

Batu kan tsarin jami'o'i ta fuskar addini

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi minista 1 da ya fahimci nufin gwamnatinsa ga 'yan Najeriya

A cikin wani karatu da ya gabatar a yau Talata, wanda aka watsa kai tsaye a shafinsa na Facebook, Sheikh Mansur Isa Yelwa ya ce ya dawo limancin masallacin bayan abubuwan da suka faru.

Sheikh Mansur Yelwa ya fara tabo batun da ya shafi tsarin da jami'o'i ke amfani da shi, inda ya ce:

"Jami'a ta kansa al'amuran addini a karkashin MSSN idan daga dalibai ne, abin da ya shafi Kiristoci yana karkashin CAN. Kuma ba a yarda wata kungiya, ta ci gashin kanta, har a bata wani wuri na ibada, saboda idan aka yi hakan, matsalar da za ta haifar ba za ta kau ba."

Malamin ya ce a soshiyal midiya ne ya ga sanarwar an ba wata kungiyar dalibai 'yan Tijjaniya fili don su gina masallaci a jami''ar, a cewarsa wannan dalilin ne ya sa ya fito ya nuna adawarsa ta hanyar ajiye limancin, don gujewa fitinar da ita makarantar ba ta hango ba.

Gaskiyar dalilin malam na ajiye limanci

Malamin ya ce da farko, ya tashi ne ranar Juma'a da zummar zai yi huduba game da wannan al'amari, sai dai a karshe ya yanke shawarar ya sanar da murabus dinsa daga limancin masallacin.

Kara karanta wannan

An sa mata sun yi tsirara da wasu sojoji suka kai samame ɗakunan ɗalibai a jami'ar UNIOSUN

Sheikh Mansur Yelwa ya ce:

"Ni ina ganin kamar an cuce ni, kamar an zalunce ni, Allah kuma ya hana a dake ka kuma a hana ka kuka. Sai na yi amfani da ayar Allah, sai na fada na ce ni ba a yi mun dai dai ba, sai na ce tun da ni ba ni da karfin da zan fada in ce a bari dole to ni na sauka."

Malam ya yi tsokaci kan maganganun mutane

Sheikh Mansur Yelwa ya ce duk da ba ya bibiyar soshiyal midiya sosai, amma ana ba shi rahoto kan maganganun da mutane suka yi, kuma ya fahimci da masu goyon bayansa da masu sukarsa, duk suna kaunarsa ne.

Ya ce akwai wadanda suka nuna masa kuskurensa na ajiye limanci duk da sun ce yana kan daidai a batun bada filin, sannan akwai wadanda su ba su ga kuskurensa ta kowace fuska ba, saboda suna sonsa sosai.

"Kuma na gode wa kowa, kowa ya taimake ni," - Farfesa Yelwa.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan ta'adda suka hallaka 'yan Najeriya kusan 80,000 daga 2020 zuwa 2025

Malam ya amsa kiraye kirayen jama'a

Tun bayan fadin cewa ya yi murabus, malamin ya ce ya samu kiraye kiraye daga manyan malamansa, iyayensa, abokansa, da duk masu fada a ji, don ganin an samu maslaha a kai.

Sheikh Mansur Yelwa ya ce:

"Kun san shi addini ba abin wasa ba ne. Na tsaya na yi nazari sosai a kan maganganu, na wadanda suka kira ni daga cikin malamai na, shugabanni, iyaye da kuma abokaina masu daraja, kuma dukansu suna sa ni, suna hana ni.
"Don haka nake cewa, cikin dukkan wadanda suka yi mun nasiha, a kan cewa na ce ba daidai ba ne, shi wannan dai dai ne, amma cewa na sauka daga kan limanci shi wannan ba dai dai ba ne.
"To lallai na yi nazari a kai sosai, ba za mu ba shaidan kofa ba. Malamanmu, da majalisar Shura ta jami'ar ATBU, suka yi zama da mu, suka kuma roki cewa don Allah mu janye wannan maganar.

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta yi martani kan sukar da ake yi mata dangane da ba mata jarin kosai

"Don haka ina sanar da ku cewa, idan abin da na yi kuskure ne Allah ya yafe mun, su ma mutane ina neman yafiyarsu, na dawo, don haka ina maku magana ne a matsayin babban limami na ATBU Bauchi."

Kalli bidiyon a nan kasa:

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com