Atiku ya 'tona wayau' da Tinubu yake shirin yi game da tallafin fetur

Atiku ya 'tona wayau' da Tinubu yake shirin yi game da tallafin fetur

  • Atiku Abubakar ya kira taron ‘yan jarida na duniya, a nan ya sake ya ragargazar zancen tallafin mai a 2027
  • ‘Dan takaran shugaban kasar na ADC ya yi bayanin yadda zai bi domin ganin fetur ya dawo ya yi araha
  • Abdul Rasheeth ya shaida cewa Atiku ya gano ana so a dawo da tallafi amma a sake cire shi bayan zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Atiku Abubakar mai neman takarar shugaban Najeriya a jam’iyyar ADC ya kira taron ‘yan jarida ranar Juma’ar nan.

Da yake magana da manema labarai ranar 18 ga watan Satumba, 2026, ya sake tabo zancen wahalar da jama’a suke ciki.

Bola Tinubu da Atiku Abubakar
Shugaba Bola Tinubu a kasar waje da Atiku Abubakar a gidansa Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Atiku Abubakar ya kira taron 'yan jarida

A bidiyon da Abdul Rasheeth ya daura a dandalin X, an ji Atiku Abubakar yana mai maganganu kan gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Sanata Shehu Sani ya cire Atiku cikin wadanda ya kamata su nemi shugaban kasa

Alhaji Abdul Rasheeth yana cikin Masu taimakon tsohon mataimakin shugaban na Najeriya.

Wazirin Adamawa ya dage cewa zai kawo sabon tsarin tallafin man fetur idan ya yi nasarar zama shugaban kasa a 2027.

Atiku Abubakar ya ce zai fito da tsarin tallafi na gaskiya a kan kayan mai da ake tacewa kuma ake saida su a nan Najeriya.

Yadda Atiku zai kawo tsarin tallafin mai

Ya bada misali da harkar casar shinkafa, ya ce gwamnati za ta iya saukake kudin casa ta yadda za a saye shinkafa da araha.

Idan shinkafa ta yi sauki, za a samu karin masu saye a gidaje wanda hakan yake nufin karfin tattalin arzikin manoma zai inganta.

Atiku yana ganin hakan zai yi sanadiyyar da za a iya fita da shinkafa har ketare, kenan miliyoyin mutane za su samu abin yi.

Wannan salo Atiku ya ce zai bi wajen kawo tallafi a man da aka tabbatar an tace a gida (ban da kayan da aka shigo da su).

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Obi sun zo da wani tsari da zai iya zama matsala ga Tinubu a zaben 2027

Za a dawo da tallafin fetur na dan lokaci

Abdul Rasheeth ya yi ikirarin Atiku ya ce masu amfani da abubuwan hawa suna shirin yin zanga-zanga a Legas saboda tsadar mai.

Ya ce Atiku ya bayyana cewa Bola Tinubu zai yi amfani da wannan dama domin ya dawo da tallafin fetur na wani gajeren lokaci.

A cewarsa, bayan zabe gwamnatin Najeriya za ta sake koma wa gidan jiya, sai ta yi fatali da tallafin man da ake mora kafin Yunin 2023.

Fai-fan da hadimin ‘dan takaran shugaban kasar bai nuna yana wannan magana ba kamar yadda Legit Hausa ta iya tabbatarwa.

Gwamnatin Tinubu ta sha nanata cewa ba ta da niyyar dawo da tsarin tallafin da ta cire tun tuni.

Tsofaffin 'yan majalisa sun ce sai Tinubu

An ji labari kungiyar FOPSHAN suna goyon bayan manfufofin gwamnati mai-ci, za su tallata tazarcen Bola Tinubu/Kashim Shettima a 2027.

Mambobin ƙungiyar sun yaba da matakan gwamnatin APC sannan sun yi alkawarin tattara masa ƙuri'u miliyan 11 don nasarar takararsa.

Manyan jami'an gwamnati da 'yan majalisu sun kare matakan da Bola Tinubu ya dauka a ofis duk da cewa sun yarda mutane suna shan wuya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng