Mutanen Gari Sun Yi Fito na Fito da 'Yan Bindiga a Katsina, An Rasa Rayuka 8

Mutanen Gari Sun Yi Fito na Fito da 'Yan Bindiga a Katsina, An Rasa Rayuka 8

  • Mazauna kauyen Katsina da jami’an sa-kai sun yi arangama da ‘yan bindiga da suka kai wa garinsu hari, inda aka kashe wasu maharan
  • ‘Yan bindigar sun shiga kauyen a kan babura dauke da bindigogi kirar AK-47, inda suka bude wuta tare da suka kashe mutane hudu
  • Mutanen garin Dansarai sun koka kan yadda jami'an tsaro suka gaza kai masu dauki duk da kiran da suka yi masu a lokacin wannan hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Katsina - Wasu ‘yan bindiga da suka kai hari kauyen Dansarai da ke karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina sun fuskanci turjiya daga mazauna yankin, inda suka kasa cimma burinsu.

Mazauna yankin sun ce maharan sun shiga kauyen ne ranar Talata a kan babura dauke da manyan makamai ciki har da bindigogin AK-47.

Kara karanta wannan

Yadda ake farautar 'yan Najeriya da sauran kasashe da sanduna a Afrika ta Kudu

'Yan bindiga sun sha kashi a hannun mutanen gari a Katsina
Taswirar jihar Katsina inda mutanen gari suka fafata da 'yan ta'adda. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kashe mutane hudu a harin Katsina

Bayan shiga kauyen, ‘yan bindigar sun fara harbe-harbe ba tare da kakkautawa ba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane hudu, kamar yadda Dily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin kauyen da ya shaida lamarin ya ce:

“Sun rika harbi babu kakkautawa lokacin da suka shigo kauyen. An kashe mutanenmu hudu nan take.”

Bayan fusata da kisan da kuma barnar da maharan suka yi, mazauna Dansarai tare da hadin gwiwar jami’an sa-kai sun tattara karfi domin tunkarar ‘yan bindigar.

Wani mazaunin yankin ya ce mutanen garin sun yi nasarar fatattakar maharan, inda aka kashe ‘yan bindiga hudu yayin arangamar.

Ya ce sauran maharan sun ranta a na kare bayan sun kasa aiwatar da shirin satar dabbobi da kwace dukiyoyin jama’a.

An koka kan rashin zuwan jami’an tsaro

Rahoto ya nuna cewa an jikkata wasu mazauna kauyen takwas a harin, inda aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa cibiyoyin lafiya da ke kusa.

Kara karanta wannan

Mutum 18 'yan asalin jihar Sakkwato sun mutu lokaci guda a hanyar dawowa daga Legas

Mazauna yankin sun bayyana cewa sun rika kiran hukumomin tsaro domin neman dauki a lokacin harin, amma babu jami’in tsaro da ya isa wurin kafin maharan su tsere.

Wani jagoran al’umma ya ce:

“Mun yi iya yinmu wajen neman taimako, amma babu wanda ya zo. An bar mu ne mu fuskanci lamarin da kanmu.”
Mutanen gari a Katsina sun yi zargin cewa sun nemi daukin jami'an tsaro lokacin da aka farmake su amma ba a je ba
Sojojin Najeriya kusa da motar yaki a wani sansanin soji. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

An nemi karin jami’an tsaro a yankin

Bayan faruwar lamarin, mazauna Dansarai da kauyukan da ke makwabtaka sun yi kira ga gwamnatocin jiha da tarayya su kara tura jami’an tsaro zuwa yankin gabashin Malumfashi.

Sun bayyana yankin a matsayin daya daga cikin wuraren da suka fi fuskantar matsalar ‘yan bindiga a shiyyar Funtua, a cewar rahoton Daily Post.

Yankin Funtua ya kunshi kananan hukumomi 11 a jihar Katsina, kuma bangaren gabashin Malumfashi na daga cikin wuraren da matsalar hare-haren ‘yan bindiga ta fi shafa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce tana binciken lamarin. Kakakin rundunar, Sadiq Aliyu, ya bayyana cewa zai tabbatar da bayanan kafin bayar da bayani.

Mutane gari sun yi artabu da 'yan bindiga

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a jihar Sokoto inda suka yi awon gaba da mutanen wani kauye zuwa cikin daji.

Kara karanta wannan

Harin Borno: Adadin daliban da ake nema yanzu ya haura 30, wani kansila ya yi bayani

Rahoto ya nuna cewa Mutanen garin da lamarin ya auku sun yi ta maza, suka fantsama cikin daji domin yin artabu da tantiran 'yan bindigan da suka kawo musu hari.

An ce wannan namijin kokarin da jajirtattun mutanen garin suka yi, ya sanya sun samu nasara kan 'yan bindigan da suka zo cutar da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com