Iran Ta Gindaya Sharuddan Kawo Karshen Yaki da Amurka

Iran Ta Gindaya Sharuddan Kawo Karshen Yaki da Amurka

  • Iran ta ce ta mika wa Amurka sharuddan kawo karshen yakin ta hannun Qatar, kuma tana jiran martanin Shugaba Donald Trump
  • Tehran ta bukaci kawo karshen yakin a dukkan fagen daga, sakin kudaden Iran da aka kwace da kuma kawo karshen killace tashoshin ruwa
  • Iran ta ce shirinta na soji ya karkata wajen mayar da hankali kan jiragen ruwan Amurka daga Tekun Gulf zuwa Tekun Oman

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Iran ta ce ta mika wa gwamnatin Amurka wasu sharudda na kawo karshen yakin tsakanin kasashen biyu.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa ta mika sharuddan kawo karshen yakin ne ta hannun masu shiga tsakani daga Qatar.

Iran ta mika bukatarta ga Amurka
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Babban jami’in tsaron Iran, Mohsen Rezaei, ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da tashar Al Jazeera a ranar Asabar, 19 ga watan Satumban 2026.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Houthi ta kai hare hare a wurare masu muhimmanci a Saudiyya

Rezaei ya ce Iran na ci gaba da tuntubar Qatar, wadda ta mika wa Washington sharuddan Tehran domin kawo karshen yakin.

“Har yanzu muna tuntubar mai shiga tsakani, Qatar, wadda ta mika wa Washington sharuddanmu domin kawo karshen yakin. Muna jiran martanin Shugaba [Donald] Trump,” in ji shi.

Iran ta bayyana sharuddan da take nema

Rezaei ya ce Iran na bukatar kawo karshen yakin a dukkan fannonin da ake gwabzawa, da sakin kudaden kasar da aka kwace, da kuma kawo karshen killacs tashoshin ruwan kasar.

“Sharuddanmu su ne a kawo karshen yakin a dukkan fagen daga, a saki kudadenmu da aka kwace, sannan a kawo karshen killace tashoshin ruwa,” in ji shi.

Rezaei, wanda ya karbi mukamin sakataren Majalisar Koli ta Tsaron Kasa ta Iran kusan wata guda da ya gabata, ya ce amincewa da sharuddan zai kasance cikin muradun Washington.

Ya kuma ce barazanar Trump ba za ta haifar da sakamakon da Amurka ke bukata ba, yana mai cewa Iran a shirye take domin fuskantar yaƙi mai tsanani.

Kara karanta wannan

Matakin da Gwamna Bago ya dauka kan mutuwar mutane 37 a hannun NSCDC a Neja

Qatar da Pakistan na kokarin dawo da tattaunawa

Qatar da Pakistan, wadanda ke shiga tsakani tsakanin bangarorin, suna kokarin sake farfado da tattaunawar Iran da Amurka tun bayan karewar yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da bangarorin suka cimma a watan da ya gabata.

Kasashen yankin su ma na kokarin ganin an kawo karshen yakin da ya fara bayan da Amurka da Isra’ila suka kai hare-hare kan Iran a karshen watan Fabrairu.

Rahotanni sun ce hare-haren sun yi sanadin mutuwar Jagoran Juyin Juya Halin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Iran ta ce tana shirin fuskantar sabon hari

Rezaei bai yi watsi da yiwuwar Amurka ta sake kai hari kan Iran ba, inda ya ce bisa kimantawar sojojin kasar, yiwuwar hakan tana nan sosai.

Sai dai ya jaddada cewa Tehran a shirye take idan aka sake kai mata hari. Ya ce tun bayan fuskantar rikice-rikicen soja guda biyu a baya, Iran ta sauya tsarin shirinta na soji.

A cewarsa, yanzu Iran ta fi mayar da hankali kan jiragen ruwan sojin Amurka da ke yankin, daga Tekun Larabawa zuwa Tekun Oman da kuma Tekun Arabiya.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da musayar wuta, manyan shugabannin ƙasar Iran za su shiga Amurka

Sai dai Rezaei ya ce wuraren da ke bayan wannan iyaka, musamman wajen Tekun Indiya, za su kasance a wajen inda dakarun Iran za su iya kai wa.

Iran ta gindaya sharudda ga Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka da shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugabannin Iran za su je Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa Amurka za ta bai wa wata tawagar Iran damar halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) a birnin New York.

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta tabbatar da cewa matakin zai shafi Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng