Tinubu Ya Sanar da Karya Farashin Sufuri a Najeriya, Ya Kafa Hujja da Kaduna da Wasu Jihohi
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce ‘yan Najeriya sun fara ganin raguwar kudin sufuri tun kafin ranar 1 ga Oktoba, 2026
- Ya ce amfani da motocin gas na CNG da masu amfani da wutar lantarki ya taimaka wajen rage kudin sufuri a jihohi da dama
- Tinubu ya ce Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa gwamnonin da ke amfani da CNG domin fadada shirye-shiryen rage kudin sufuri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ‘yan Najeriya sun fara ganin raguwar kudin sufuri yayin da ake shirin samar da sufuri mai rahusa daga ranar 1 ga Oktoba, 2026.
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da bayani kan alkawarin samar wa ‘yan Najeriya da sufuri mai saukin kudi daga ranar 1 ga Oktoba, 2026.

Kara karanta wannan
"Ku nemi mafaka," NiHSA ta jero jihohi 15 da za a yi mummunar ambaliyar ruwa a Najeriya

Source: Twitter
Tinubu ya ce kudin sufuri sun karye
Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar 27 ga Agusta, Tinubu ya gana da gwamnonin jihohi, inda suka tattauna matakan da za a dauka domin rage kudin sufuri a fadin kasar tare da rage radadin matsin tattalin arziki.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Tinubu ya ce bayan ganawar an kafa kwamitin aiwatar da shirin sufuri mai araha, wato National Affordable CNG Transit Programme, karkashin kulawar Kungiyar Gwamnonin Najeriya.
Shugaban ya kuma kawo misalai kan yadda motocin sufurida ke amfani da CNG da wutar lantarki suka rage kudin sufuri, yana mai jaddada cewa tuni ‘yan Najeriya suka fara samun saukin tafiye-tafiye.
Jihohin da Tinubu ya kafa hujja da su
“A Kaduna, an samar da motocin bas 100 masu amfani da gas wadanda ke jigilar mutane kyauta a manyan hanyoyi a fadin jihar. A shekararsu ta farko ta aiki, motocin sun dauki fasinjoji kusan miliyan 3.2.

Kara karanta wannan
Tsofaffin shugabannin majalisa sun tsaida ‘dan takara, har da masa alkawarin kuri’u miliyan 11
“A Oyo, motocin bas masu amfani da CNG da aka tura karkashin Pacesetter Transport sun rage kudin tafiyar Lagos zuwa Ibadan daga kusan N8,000 zuwa N3,200 a farkon fara aikin.
“A Adamawa, sn rage kudin mota da kashi 50 cikin 100, daga N8,000 zuwa N4,000. A Enugu, inda aka tura motocin bas 100 masu amfani da CNG, an rage kudin tafiyar Enugu zuwa Nsukka daga N2,500 zuwa N1,500."
- In ji Bola Tinubu.
Shugaban ya kara da cewa, ta hanyar hadin gwiwa da NURTW, fasinjojin motocin haya da aka sauya zuwa amfani da CNG a wasu hanyoyin zirga-zirgar Abuja na samun rangwamen kashi 40 cikin 100 na kudin mota.

Source: Facebook
Tinubu ya jinjinawa gwamnoni
Ya ce daga cikin hanyoyin da ake samun wannan rangwamen akwai Area 1 zuwa Gwagwalada, inda kudin mota ya ragu daga N1,500 zuwa N900; Nyanya daga N700 zuwa N420; da Wuse daga N400 zuwa N240.
Tinubu ya yaba wa gwamnonin da ke fadda amfani da CNG, amma ya ce akwai sauran aiki da ya kamata a yi. Ya yi alkawarin cewa Gwamnatin Tarayya za ta tallafa musu domin fadada shirye-shiryen.
Tinubu na shirin gyara dokokin haraji
Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta fara nazarin sababbin dokokin haraji na tsawon mako shida domin gano gibin da ke tattare da aiwatar da su
An ware wa kwamitin fasaha mako shida domin kammala aikin nazarin dokokin tare da gabatar da shawarwari kan yadda za a inganta aiwatar da su.
Asali: Legit.ng
