An Zo Wajen: Kwankwaso Ya Yi Maganar Yafewa Gwamna Abba

An Zo Wajen: Kwankwaso Ya Yi Maganar Yafewa Gwamna Abba

  • Rabiu Kwankwaso ya ce zai iya sulhunta wa da Gwamna Abba Yusuf idan gwamnan ya nuna bukatar yin hakan
  • Madugun Kwankwasiyya ya ce bai taba watsi da Abba Kabir Yusuf ko neman ya sauya jam’iyya ba, kuma har yanzu yana son sa
  • Kwankwaso ya ce ba ya rike da gaba, yana mai cewa ya taba yafewa tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje duk da rashin jituwar da ta taba faruqa tsakaninsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce a shirye yake ya sasanta da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, idan gwamnan ya nuna bukatar hakan.

Gwamna Abba Yusuf, wanda ya kasance mai biyayya ga tafiyar Kwankwasiyya, ya lashe zaben gwamna a Kano a shekarar 2023 karkashin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Kara karanta wannan

Rigima ta kunno kai a NDC kan kwamitin yakin neman zaben Kwankwaso da Obi

Kwankwaso ya yi magana kan Abba
Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Abba Kabir Yusuf, Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Daga bisani, Yusuf ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), lamarin da ya haifar da tsamin dangantaka tsakaninsa da Kwankwaso.

Abba Yusuf ya yi aiki a matsayin mataimaki na Kwankwaso tsawon shekaru da dama, kuma alakarsu ta siyasa ta dade tana karfafa tafiyar Kwankwasiyya a Kano.

“Ban taba watsar da shi ba”

Jaridar Daily Trust ta ce a wata hira wadda aka wallafa, Kwankwaso ya ce zai iya yafewa tare da sulhunta da Gwamna Abba idan shi ma yana son hakan.

Kwankwaso ya ce bai taba watsi da Gwamna Abba ba, kuma bai taba neman ya bar jam’iyyarsa ko korarsa daga tafiyar siyasa ba.

“Ban watsar da shi ba, ban ce ya tafi ba, kuma ban kore shi ba. Har yanzu ina son sa,” in ji Kwankwaso.

Kwankwaso, wanda ke takarar mataimakin shugaban kasa tare da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), ya ce shi ba mutum ne mai son daukar fansa ba.

Kara karanta wannan

Dickson: Jagoran NDC na kasa ya fadi dalilin kin shiga APC, ya aika sako ga Kwankwaso da Obi

Ya bayyana cewa yana yawan yafewa mutanen da suka taba masa laifi, yana mai kawo tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, a matsayin misali.

Ya tuna da rashin jituwarsa da Ganduje

Kwankwaso ya ce ya taba samun sabani da Ganduje sau da dama, musamman lokacin da suke aiki a ma’aikatar tsaro.

Ya ce a shekarar 2007, lokacin da Ganduje yake aiki a matsayin mataimakinsa na musamman, an gudanar da tarurruka da nufin ganin an kayar da shi a siyasa saboda ya shiga takara da wasu.

“Sau nawa na samu matsala da Ganduje? Ya kalubalance ni a lokuta da dama,” in ji shi.

Ya kara da cewa duk da rashin jituwar da ta kasance tsakaninsu, ya goyi bayan Ganduje tare da taimaka masa wajen neman kujerar gwamnan Kano, amma bai samu nasara a wancan lokacin ba.

Kwankwaso ya yi magana kan Gwamna Abba
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Rigima ta kunno kai a NDC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabancin NDC ta yi martani kan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa da kungiyar OK Movement ta kafa don goyon bayan Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Jam'iyyar NDC ta nesanta kanta da kwamitin yaƙin neman zaɓe mai mambobi 59 da ƙungiyar OK Movement ta kafa domin tallata Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng