Dama Ta Samu: Tinubu Ya Kaddamar da Sabon Shiri da Matasa 5,000 Za Su Samu Aiki

Dama Ta Samu: Tinubu Ya Kaddamar da Sabon Shiri da Matasa 5,000 Za Su Samu Aiki

  • Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da shirin horar da matasa 5,000 kan gyara da girka mitar wutar lantarki domin samar da ayyukan yi
  • Shirin da aka yi wa taken 'The Power Force' zai ba matasa horo kan ƙwarewar fasaha tare da sama masu damar aiki a fannin wuta
  • Gwamnatin tarayya ta ce za a fara shirin cikin kwanaki 30 masu zuwa, kuma wadanda suka gama sakandare da 'yan NYSC za su iya nema

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da ƙaddamar da wani shiri na horar da matasa 5,000 kan gyara da girka mitar lantarki a ƙarƙashin shirin samar da mita na shugaban kasa (PMI).

Shugaba Tinubu ya ce shirin, mai suna The Power Force, na daga cikin manufofin gwamnatinsa na Renewed Hope Agenda domin samar da ayyukan yi ga matasa.

Kara karanta wannan

Bayan shan wuta, mayakin ISWAP na kan kogi ya mika wuya ga jami'an sojoji

Shugaba Tinubu ya kaddamar da shirin ba matasa 5,000 horo kan gyara da girka mitar lantarki.
Shugaba Bola Tinubu ya na duba wasu takardu a ofishinsa da ke fadar shugaban kasa. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Tinubu ya kawo sabon shiri ga matasa

Kamar yadda Legit Hausa ta gani, shugaban kasar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis.

Tinubu ya ce shirin zai bai wa matasan horo kan ƙwarewar aiki tare da haɗa su da damar samun aikin yi a bangaren wutar lantarki.

Ya ce:

"Ta hanyar Shirin Samar da Mita na Shugaban Ƙasa (PMI), wanda muka ƙaddamar domin rage gibin mita, kawo ƙarshen cajar wuta ba gaira babu dalili, kare masu amfani da lantarki da ƙarfafa kasuwar wutar lantarki, yau mun buɗe wata sabuwar dama ga matasa 5,000 domin samun horo a matsayin masu kula da girka mita ƙarƙashin The Power Force. Wannan shiri ya shafi ayyukan yi, ƙwarewa da mutunci."

Waɗanda za su iya shiga shirin

Shugaban ya bayyana cewa shirin zai kasance a buɗe ga 'yan Najeriya da suka kammala karatun sakandare.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi abin da zai gudana a taron cika shekara 1 da rasuwar Buhari

Ya ƙara da cewa an ware kaso na musamman ga masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) domin su ma su amfana da wannan dama.

Tinubu ya ce ƙara yawan gidaje da sana'o'in da ke da mita zai taimaka wajen inganta samar da wutar lantarki da kuma tabbatar da adalci wajen biyan kuɗin amfani da ita.

A cewarsa:

"Idan gidaje da kasuwanni suna da mita, 'yan Najeriya za su riƙa biyan kuɗin wutar da suka yi amfani da ita kawai. Hakan kuma zai bai wa kamfanonin rarraba wutar lantarki damar tara kuɗaɗensu cikin gaskiya, rage asara, gyara kayan aiki, faɗaɗa haɗin wuta da kuma inganta ayyukansu."
Shugaba Bola Tinubu ya roki matasa su daure su cike wannan sabon shiri da aka kawo masu
Shugaba Bola Tinubu ya na jawabi a wani muhimmin taro a Abuja. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Za a fara shirin cikin kwanaki 30

Tinubu ya ce ya umarci masu gudanar da PMI su yi aiki tare da Ma'aikatar Raya Matasa ta Tarayya, da Cibiyar Horar da Ma'aikatan Wutar Lantarki ta Najeriya (NAPTIN), da sauran hukumomin da abin ya shafa domin fara aiwatar da shirin cikin kwanaki 30 masu zuwa.

Ya kuma buƙaci matasan da suka cancanta su nemi shiga shirin, yana mai cewa hakan zai ba su ƙwarewar da za ta taimaka musu samun abin dogaro da kai, tare da taimakawa gwamnati wajen kawo ƙarshen tsarin ƙiyasta kuɗin wutar lantarki da inganta samar da wuta a faɗin Najeriya.

Kara karanta wannan

Babbar magana: CBN ya soke lasisin bankuna 46, sun daina aiki a Najeriya

Gwamnatin Tinubu za ta dauki matasa aiki

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Bola Tinubu ta bude shafin daukar matasa aiki a karkashin shirin kiwon lafiya na NHFP daga dukkanin jihohin Najeriya.

Gwamnatin ta sanar da cewa za ta ba wadanda aka dauka aikin alawus mai gwabi da kayan aiki don kawo sauyi a tsarin kiwon lafiya.

Legit Hausa ta yi bayani dalla dalla yadda matasa 'yan kasa da shekaru 35 za su iya neman wannan aikin da takardun da ake bukata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com