Babbar Magana: Houthi Ta Kai Hare Hare a Wurare Masu Muhimmanci na Saudiyya

Babbar Magana: Houthi Ta Kai Hare Hare a Wurare Masu Muhimmanci na Saudiyya

  • Mayakan Houthi a Yemen sun ce sun kai hari kan wasu wurare masu muhimmanci a Riyadh da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa
  • Saudiyya ta ce dakarunta sun lalata wani makami mai linzami da Houthi suka harba zuwa Riyadh, tare da dakile wasu hare-hare
  • Jordan ta yi Allah wadai da harin, tana mai bayyana goyon bayanta ga Saudiyya da kuma yin tir da hare-haren da aka ce an kai kan fararen hula

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Riyadh, Saudiyya - Ƙungiyar Houthi da ke Yemen ta ce mayaƙanta sun kai hari kan wasu “wurare masu muhimmanci” a birnin Riyadh na Saudiyya.

Mai magana da yawun ƙungiyar, Ameen Hayyan, ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Asabar, 19 ga watan Satumban 2026, inda ya ce an yi amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-haren.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An kai korafin dan majalisa gaban NDLEA kan zargin shan hodar iblis

Houthi sun kai hare hare Saudiyya
Wani wuri na ci da wuta bayan hari a Saudiyya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta ce Houthi sun kuma yi ikirarin kai hari kan wani wurin sarrafa ko adana man fetur na kamfanin Aramco da ke Yanbu.

Saudiyya ta ce ta dakile harin

A nasa martanin, mai magana da yawun rundunar haɗin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta, Manjo-Janar Turki al-Maliki, ya ce dakarun tsaron sararin samaniyar Saudiyya sun tare, tare da lalata wani makami mai linzami da Houthi suka harba zuwa Riyadh.

Al-Maliki ya bayyana Houthi a matsayin ƙungiyar “’yan ta’adda”, yana mai cewa suna ƙara yunƙurin kai hare-hare kan fararen hula da muhimman ababen more rayuwa a babban birnin Saudiyya.

Ya kuma ce an dakile yunƙurin kai hare-haren Houthi kan fararen hula da ababen more rayuwa a biranen Taif, Baish, Farasan da Yanbu.

A cewarsa, dakarun tsaron sararin samaniya sun dakile hare-haren kafin su isa wuraren da aka nufa.

Rundunar haɗin gwiwar ta yi barazana da ɗaukar mataki

Kara karanta wannan

Amurka na fama da kanta, ta amince da sayar da manyan makamai ga Israila

Mai magana da yawun rundunar ya ce Rundunar Haɗin Gwiwar tana da ’yancin ɗaukar matakan da suka dace domin dakile ayyukan Houthi.

Ya ce za a ɗauki irin waɗannan matakai ne bisa tanadin dokokin ƙasa da ƙasa na jin ƙai.

Jordan ta yi Allah wadai da harin

A gefe guda, ƙasar Jordan ta yi Allah wadai da harin makami mai linzami da Houthi suka kai kan babban birnin Saudiyya, Riyadh.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Jordan ta ce an tare tare da lalata makamin mai linzamin da aka harba zuwa Riyadh.

Ma’aikatar ta kuma yi tir da yunƙurin kai hare-hare kan fararen hula da wuraren farar hula a Bisha, Taif, Farasan da Yanbu.

Kakakin ma’aikatar, Fouad Majali, ya bayyana hare-haren a matsayin “babban take doka”, yana mai cewa Jordan na nuna cikakken goyon baya ga Saudiyya.

Houthi sun kai hari Saudiyya
Mai magana da yawun kungiyar Houthi, Yahya Saree Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Houthi ta kakkabo jirgin yakin Saudiyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Houthi ta Yemen ta ce dakarunta sun harbo jirgin yaƙin Saudiya kirar F-15 a sararin samaniyar ƙasar, yayin da yake gudanar da wani samame na soji.

An bayyana cewa an kakkabo jirgin yakin na Saudiyya ne a sararin samaniyar lardin Marib na kasar Yemen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng