Senagal da Kasashen Afrika 4 da Aka Koro daga Gasar Cin Kofin Duniya zuwa yanzu
- Senegal ta zama kasa ta biyar daga Afirka da ta fice daga gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026 bayan ta sha kashi a hannun Belgium.
- DR Congo ma ta yi bankwana da gasar bayan Ingila ta doke ta da ci 2-1 duk da cewa ita ce ta fara zura kwallo a farkon fara wasan
- Duk da haka, har yanzu kasashe biyar daga Afirka na ci gaba da fafatawa domin neman zama nahiyar farko da za ta lashe Kofin Duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Fatan nahiyar Afirka na lashe Kofin Duniya ta FIFA 2026 ya kara fuskantar koma baya a ranar Laraba bayan da Senegal ta zama kasa ta biyar daga Afirka da ta yi bankwana da gasar, kuma ta hudu da ta fice a zagaye na 32.
Senegal ta sha kashi da ci 3-2 a hannun Belgium bayan karin lokaci, duk da cewa ta fara jagorantar wasan da ci 2-0.

Source: Getty Images
Shan kashin Sengal da DR Congo
Belgium ta fara farfadowa ne lokacin da Romelu Lukaku ya zura kwallo a raga a minti na 86, kafin Charles De Ketelaere ya farke kwallo ta biyu a karin lokaci na minti na 90+2, in ji rahoton Sky Sport.
Daga bisani Youri Tielemans ya ci bugun fenariti a minti na biyar na karin lokaci, wanda ya tabbatar da nasarar Belgium tare da kai ta zagaye na 16.
A ranar Laraba din kuma, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo) ta fice daga gasar bayan ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Ingila a wani wasan zagaye na 32.
'Yan wasan DR Congo sun fara cin kwallo ta hannun Brian Cipenga a minti na 13, bayan ya keta mai tsaron ragar Ingila Jordan Pickford.
Sai dai kyaftin din Ingila Harry Kane ya jagoranci nasarar kasarsa, inda ya ci kwallaye biyu a mintuna na 41 da 75, lamarin da ya kai Ingila zagaye na 16.

Kara karanta wannan
An mika wa Tinubu rahoto kan kara wa shugaban kasa da masu mukaman siyasa albashi
Kasashen Afrika da suka fice daga Kofin Duniya
Yanzu Ingila za ta kara da kasar da ke karbar bakuncin gasar, Mexico, domin neman gurbi a wasan daf da na kusa da na karshe, yayin da Senegal da DR Congo suka bi sahun sauran kasashen Afirka da suka fice daga gasar.
Ga cikakken jerin kasashen Afirka da suka fice daga gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026:
1. Senegal
Ta sha kashi da ci 3-2 a hannun Belgium bayan ta bari an farke mata kwallaye biyu. Belgium ta yi nasarar jan ragamar wasan ne da bugun fenaritin Youri Tielemans a karin lokaci.
2. Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DR Congo)
Ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Ingila. DR Congo ta fara cin kwallo ta hannun Brian Cipenga, amma Harry Kane ya ci kwallaye biyu ya kai Ingila zagaye na gaba, in ji rahoton BBC.
3. Tunisia
Ta kare a matsayi na hudu a rukunin F bayan Netherlands, Japan da Sweden, lamarin da ya hana ta tsallakewa zuwa zagaye na gaba.

Source: Instagram
4. Côte d'Ivoire (Ivory Coast)
Ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Norway, wanda ya kawo karshen burinta na kai wa zagaye na 16.
5. Afirka ta Kudu
Ta sha kashi da ci 1-0 a hannun Canada a zagaye na 32, lamarin da ya sa ta yi bankwana da gasar.
Duk da ficewar kasashe biyar, har yanzu akwai kasashe biyar daga Afirka da ke ci gaba da fafatawa a gasar Kofin Duniya ta FIFA 2026, inda suke kokarin zama kasa ta farko daga nahiyar da za ta lashe kofin duniya.
Sabon shiga gasar cin kofin duniya
A wani labari, mun ruwaito cewa, gasar cin kofin kwallon duniya ta 2026 za ta kasance ta musamman domin a karon farko za a kara yawan kasashen da za su halarta daga 32 zuwa 48.
Wannan lamarin da ya bai wa karin kasashe damar shiga gasar ciki har da wadandaba su taba taka leda a gasar kofin duniya ba a tarihi.
A Kofin Duniya na 2022 da aka yi a Qatar, kasa mai masaukin baki ce kadai ta fara halartar gasar ta kwallon kafa a karon farko.
Asali: Legit.ng

