Rigima Ta Kunno Kai a NDC kan Kwamitin Yakin Neman Zaben Kwankwaso da Obi
- Shugabancin NDC ya ce jam’iyyar ba ta da hannu wajen kafa kwamitin yaƙin neman zaɓe na mambobi 59 da OK Movement ta sanar
- Shugaban NDC, Cleopas Moses, ya ce sanarwar ba ta fito daga jam’iyyar ba, don haka ya buƙaci jama’a da kafafen yaɗa labarai su yi watsi da ita
- Jam’iyyar ta gargadi ƙungiyoyin magoya baya da kada su kafa wasu tsare-tsare a madadinta ba tare da amincewar kwamitin NWC ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugabancin NDC ta yi martani kan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa da kungiyar OK Movement ta kafa don goyon bayan Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Jam'iyyar NDC ta nesanta kanta da kwamitin yaƙin neman zaɓe mai mambobi 59 da ƙungiyar OK Movement ta kafa domin tallata Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban NDC na ƙasa, Cleopas Moses, ya fitar ranar Asabar, 19 ga watan Satumban 2026.
Ya ce jerin sunayen kwamitin bai fito daga jam’iyyar ba, don haka ya kamata a yi watsi da shi.
OK Movement ta bayyana kwamitin mambobi 59
A ranar Alhamis, OK Movement ta sanar da kafa kwamitin mai mambobi 59 wanda ya ƙunshi masu kula da shiyyoyi da jihohi, da kuma daraktocin sassa daban-daban.
Daga cikin sassan akwai wayar da kan jama’a, harkokin mata, tsare-tsare, tsaro, harkokin shari’a da sauran fannoni.
Ƙungiyar ta ce shugabanta, John Ughulu, da Sakatarenta na ƙasa, Saadatu Sani, za su kasance Darakta-Janar da Sakatare na kwamitin yaƙin neman zaɓen.
‘Ba daga NDC ta fito ba’
Sai dai Cleopas Moses ya ce jam'iyyar NDC ba ta da hannu wajen kafa wannan kwamitin.
“Jam’iyyar ta nesanta kanta gaba ɗaya daga sanarwar kwamitin yaƙin neman zaɓe na OK Movement. Ba daga jam’iyyar ta fito ba, don haka jama’a da kafafen yaɗa labarai su yi watsi da ita,” in ji shi.
Moses ya jaddada cewa dukkan ’yan takarar jam’iyyar suna ƙarƙashin ikon NDC da dokokinta, yana mai cewa shugabancin jam’iyyar ne kaɗai ke da hurumin kafa da sanar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa.
NDC ta gargadi ’yan takara
Shugaban jam’iyyar ya ce ya kamata dukkan ’yan takarar NDC su fahimci cewa ba sa takara ne a matsayin ’yan takara masu zaman kansu ba.
“Su ne ’yan takarar da jam’iyyar ta samar, kuma suna ƙarƙashin ikon jam’iyyar da dokokinta."
“Saboda haka, shugabancin jam’iyyar ne kaɗai zai iya kafa tare da sanar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa,” in ji Moses.
Ya kuma gargadi mambobi, ’yan takara da ƙungiyoyin magoya baya da kada su yi abin da zai raunana jam’iyyar ko kuma su yi amfani da sunanta wajen kafa wasu tsare-tsare ba tare da izini ba.
Moses ya ce daga yanzu, babu wani mutum ko ƙungiya da aka ba izinin sanarwa, kafa ko wallafa wani kwamitin yaƙin neman zaɓe, tsari ko wata hukuma da sunan jam’iyyar ba tare da samun amincewar Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) ba.

Source: Facebook
Kotu ta yi hukunci kan rajistar NDC

Kara karanta wannan
Gwamna a Najeriya ya kamu da rashin lafiya har ya gaza fitowa aiki? Gaskiya ta bayyana
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar NDC ta ce kotun daukaka kara da ke Abuja ta soke hukuncin babbar kotun tarayya da ke Lokoja, wanda ya shafi rajistar jam’iyyar.
Jam’iyyar ta ce an soke hukuncin kotun tarayya da mai shari’a Isah Dashen ya yanke watanni kadan da suka gabata.
Asali: Legit.ng

