Babbar Magana: CBN Ya Soke Lasisin Bankuna 46, Sun Daina Aiki a Najeriya
- Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke lasisin bankunan microfinance 46 daga ranar 1 ga Yuli, 2026 bisa gazawar cika ƙa’idojin aiki
- Bankunan da abin ya shafa sun haɗa da waɗanda ke Kano, Legas, Kaduna, Kebbi, Abuja da sauran jihohin Najeriya
- CBN ya ce matakin na da nufin kare masu ajiya da tabbatar da ingancin tsarin hada-hadar kuɗi a ƙasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin gudanar da aiki na kananan bankunan kasuwanci (MFB) 46 a faɗin ƙasar, matakin da ya fara aiki daga ranar 1 ga Yuli, 2026.
CBN ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne bisa ikon da doka ta ba shi ƙarƙashin dokar bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade (BOFIA) ta 2020.

Source: UGC
CBN ya soke lasisin bankuna 46
A cikin wata sanarwa da CBN ya wallafa a shafinsa na Facebook, bankin ya ce bankunan sun kasa cika wasu ƙa’idojin da ake buƙata domin ci gaba da aiki a matsayin cibiyoyin kuɗi masu lasisi.
Sanarwar ta ce gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ne ya amince da soke lasisin bankunan bayan gano matsalolin da suka shafi gudanar da ayyukansu.
A cewar CBN, wasu daga cikin dalilan da suka jawo ɗaukar matakin sun haɗa da rashin isassun kadarorin da za su iya biyan basussuka, dakatar da aiki ba tare da amincewar hukumar ba, rashin gudanar da harkokin kuɗi, da kuma rashin fara aiki cikin watanni 12 bayan samun lasisi.
Hukumar ta kuma ce wasu bankunan sun gaza wajen kiyaye mafi ƙarancin jarin da ake buƙata domin ci gaba da aiki, lamarin da ya sa aka yanke shawarar soke lasisinsu.
An rufe bankunan Kano, Legas da sauran jihohi
Daga cikin bankunan da lasisinsu ya shafa akwai wasu kananan bankunan kasuwanci da ke aiki a jihohin Kano, Legas, Abia, Kebbi, Kaduna, Abuja, Rivers, Ogun da sauran wurare.
A Kano, waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da Zain MFB (tsohon Dawakin Tofa MFB), Bompai MFB, Ajwa MFB (tsohon Gezawa), NOW NOW DIGITAL MFB, Minjibir MFB, Shanono MFB, Sumaila MFB, Rimin Gado MFB da TOFA MFB.
Haka kuma akwai wasu bankuna kamar Gold MFB, Safegate MFB, Creditville MFB da Entrepreneur MFB da ke jihar Legas, da sauran bankuna a jihohi daban-daban.
CBN ta sbayyana manufar matakin
Babban Bankin Najeriya ya ce soke lasisin wani ɓangare ne na ƙoƙarinsa na kare masu ajiya da kuma tabbatar da ingancin tsarin kuɗin ƙasar.
Hukumar ta bayyana cewa za ta ci gaba da sanya ido kan cibiyoyin kuɗi tare da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da cewa bankunan da ke aiki a Najeriya suna bin dokoki da ƙa’idojin da aka shimfiɗa.
CBN ta ƙara da cewa manufarta ita ce tabbatar da tsarin kuɗi mai ƙarfi, aminci da dorewa, tare da kare amincewar jama’a ga harkokin banki a Najeriya.
Jerin bankuna 46 da aka soke lasisinsu

Source: Twitter
Ga jerin kananan bankunan kasuwanci da CBN ya soke lasisinsu:
- Minji-Se Churchill MFB – Rivers
- Merchant MFB – Abia
- Janmaa MFB – Kwara
- Busu MFB – Niger
- Gold MFB – Lagos
- Zain MFB (tsohon Dawakin Tofa MFB) – Kano
- Bompai MFB – Kano
- Ajwa MFB (tsohon Gezawa) – Kano
- NOW NOW DIGITAL MFB – Kano
- Crystabel Microfinance Bank – Bayelsa
- Chanelle MFB – Lagos
- Abia SME MFB – Abia
- Kamba MFB – Kebbi
- Iwade MFB – Ogun
- Winview MFB – Abuja
- Zuru MFB – Kebbi
- Minjibir MFB – Kano
- Shanono MFB – Kano
- Sumaila MFB – Kano
- Rimin Gado MFB – Kano
- Mwaghavul MFB – Plateau
- Sycamore MFB – Kano
- TOFA MFB – Kano
- Safegate MFB – Lagos
- Creekline MFB – Delta
- Bestar MFB – Oyo
- Livingspring MFB – Cross River
- Apple MFB – Ogun
- Stanford MFB – Uyo
- Frontline MFB – Anambra
- Zafec MFB – Kaduna
- Supreme MFB – Lagos
- Bejin-Doko MFB – Niger
- Kanopoly MFB – Kano
- Bellbank MFB (tsohon Tsanyawa) – Kano
- Yeneng MFB – Plateau
- Creditville MFB – Lagos
- MBAG MFB – Lagos
- STRAIGHT SAHARA MFB – Benue
- OURPASS MFB – Ondo
- VERDANT MFB – Lagos
- BASAWA MFB – Kaduna
- CASHA MFB – Abuja
- ESTEEM MFB – Kano
- ENTERPRENEUR MFB – Lagos
- AVANTUS MFB – Osun
CBN ya soke lasisin bankuna 2
A wani labari, mun ruwaito cewa, CBN ya bayyana cewa ba zai lamunci bankuna su jefa kudin da jama'a ke ajiyewa cikin garari ba, zai dauki matakin da ya dace.
Babban bankin Najeriya ya sanar da soke lasisin wasu bankuna biyu na bangaren ba da rance da ajiyar kudi don mallakar gida a Najeriya.
CBN ya ce bankunan da lamarin ya shafa sun gaza a bangarori da dama, ciki har da mafi karancin jarin aiki da doka ta kayyade.
Asali: Legit.ng


