'Arewa Media': Hadimin Tinubu Zai Jagoranci Babban Taro a Gidan Gwamnatin Kano

'Arewa Media': Hadimin Tinubu Zai Jagoranci Babban Taro a Gidan Gwamnatin Kano

  • Gwamna Mai Mala Buni ya amince da ɗaukar nauyin tawagar mutum 50 daga jihar Yobe zuwa taron Arewa Media Summit da za a yi a Kano
  • Tallafin ya haɗa da kuɗin sufuri, masauki, abinci da alawus, yayin da kowace ƙaramar hukuma 17 za ta samu wakilai biyu zuwa taron
  • Babban hadimin shugaban kasa kan kafofin sadarwa na zamani, Abdulaziz Abdulaziz ya ce taron zai tattaro masana daga fannoni daban daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Yobe – Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da ɗaukar nauyin dukkan tawagar jihar da za ta halarci taron 'Arewa Media Summit', wanda za a gudanar ranar Litinin, 6 ga Yulin 2026, a Kano.

An bayyana cewa tallafin ya haɗa da kuɗin sufuri, masauki, abinci da alawus na tafiya ga mahalarta 50, waɗanda suka ƙunshi mambobin kwamitin shirya taron da masu gudanarwa da ke wakiltar jihar.

Gwamnatin Yobe ta dauki nauyin wasu mutane su halarci taron Arewa Media Summit a Kano
Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni (hagu) da hadimin shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz (dama). Hoto: Mai Mala Buni Social Media Team
Source: Facebook

Yadda aka tsara wakiltar Yobe a taron

Sakataren kwamitin mahalarta taron na jihar Yobe, kuma shugaban karamin bankin kasuwanci na YMFB, Farfesa Sheriff Almuhajir, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa kowace ƙaramar hukuma 17 ta jihar za ta tura wakilai biyu zuwa taron.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun cafke mutum 5 na kusa da tsohon gwamna kan yunkurin juyin mulki

Ya ƙara da cewa sauran mahalarta taron za su fito daga shiyyoyin sanatoci uku da kuma hedikwatar jihar, domin tabbatar da adalci wajen wakilci da kuma ƙarfafa haɗin kai.

A cewar Farfesa Almuhajir, bayan amincewar da Gwamna Buni ya bayar, shugaban kwamitin da sauran mambobin kwamitin ba su da sauran wata damuwa kan shirye-shiryen tafiyar tawagar, domin gwamnatin jihar ta riga ta tanadi duk abin da ake buƙata.

An yabawa jami'an gwamnati

Farfesa Almuhajir ya gode wa sakataren gwamnatin jihar Yobe, Dr. Mohammed Goje, bisa goyon baya da ya bayar wajen tabbatar da halartar matasa a taron.

Haka kuma, ya yaba wa shugaban matasan APC na jihar, Mohammed Musa Gulani, bisa jagoranci da gudummawar da ya bayar wajen haɗa mahalarta taron.

Ya bayyana wannan mataki na Gwamna Buni a matsayin wata alama ta ƙudirin gwamnatinsa na bunƙasa matasa, ƙarfafa harkokin yaɗa labarai da haɓaka ƙwarewar al'umma.

Abin da taron 'Arewa Media Summit' ya kunsa

Legit Hausa ta fahimci cewa, Malam Abdulaziz Abdulaziz, babban mai ba shugaban kasa shawara kan kafofin sadarwa na zamani ne ya shirya kuma zai jagoranci wannan taron.

Kara karanta wannan

Iyayen daliban da aka sace sun rusa kuka bayan ziyarar tawagar Zulum

Kamar yadda aka wallafa a shafin Arewa Media Summit na intanet, taron zai gudana ne a babban dakin taro da ke cikin gidan gwamnatin jihar Kano a ranar Litinin mai zuwa.

An ce taron zai tattaro kan 'yan jarida, masu shirya fina-finai, kafofin watsa labarai da masu wallafa rahotanni na zamani don tattauna yadda za a sauya akalar yadda ake kallon Arewa a duniya.

An ce za a gudanar da tattaunawa, bita, musayar bayanai, nazari kan tsare-tsare da kuma bada ilimi game da yadda duniya ta sauya ta fuskar kafofin sadarwa na zamani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com