Rikicin Kabilanci Ya Barke a Niger, an Kona Mutane da Ransu

Rikicin Kabilanci Ya Barke a Niger, an Kona Mutane da Ransu

  • An samu barkewar wani rikicin kabilanci a jihar Niger wanda ya jawo aka samu asarar rayukan mutane masu yawa
  • Rundunar 'yan sandan jihar Niger ta bayyana cewa daga cikin mutanen da aka kashe har da wadanda aka kona kurmus
  • Tuni aka tura jami'an tsaro zuwa yankin da lamarin ya auku domin dawo da doka da oda biyo bayan barkewar mummunan rikicin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Niger - Akalla mutane 18 ne aka kashe a wani rikici kabilanci da ke da alaka da takaddamar fili da ta dade tana faruwa a karamar hukumar Rafi da ke jihar Niger.

An bayyana cewa mutum 15 daga cikin wadanda abin ya shafa an kona su kurmus bayan da maharan suka cinnawa wani gida wuta.

An yi rikicin kabilanci a jihar Niger
Taswirar jihar Niger, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sabon farmakin ya faru ne a daren ranar Talata, 30 ga watan Yunin 2026 a Angwan-Baago kusa da kauyen Godoro, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Mutum 18 'yan asalin jihar Sakkwato sun mutu lokaci guda a hanyar dawowa daga Legas

Yadda rikicin kabilancin ya auku

A cewar rundunar 'yan sandan jihar Niger, wadanda abin ya shafa, an ritsa su ne a cikin ginin sannan aka kona su kurmus.

Rundunar ‘yan sandan ta ce an kuma kashe wani mutum guda a wani guri na daban, lamarin da ya sa adadin mutanen da suka mutu a rikicin ya kai 18, Vanguard ta kawo rahoton.

An yi amanna cewa tashe-tashen hankula sun samo asali ne daga takaddamar fili da ta dade tsakanin garuruwa biyu a yankin.

Kafin nan, rundunar ‘yan sandan ta ce rikicin ya fara ne a ranar 29 ga watan Yuni lokacin da wasu da ake zargi dauke da makamai suka harbe wani matashi mai shekaru 25, Ibrahim Musa, har lahira a kauyen Godoro.

An kashe mutane da dama

A cewar rundunar, kisan ya tunzura wani harin ramuwar gayya inda kungiyar ‘yan banga, da aka fi sani da 'yan sa-kai, ake zarginsu da tare hanya tare da kashe Bashir Mazi mai shekaru 28.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi martani kan zargin tura tsofaffin 'yan Boko Haram aikin soja

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Wasiu Abiodun, ya ce hare-haren suna da alaka da takaddamar fili da ta dade tana faruwa.

Wadanne al'ummomi rikicin ya shafa?

Wata majiya daga cikin garin, wacce ta bukaci a sakaya sunanta saboda fargabar harin ramuwar gayya, ta yi zargin cewa rikicin ya shafi al'ummar Fulani da na Kamuku.

Majiyar ta ce an kona gidaje da dama, yayin da mata da yara suna cikin wadanda rikicin ya fi shafa.

An yi rikicin kabilanci a jihar Niger
Gwamnan jihar Niger, Mohammed Umaru Bago Hoto: @HonBago
Source: Twitter

Shugaban Karamar Hukumar Rafi, Ayuba Katako, ya tabbatar da aukuwar rikicin amma ya ki bayyana adadin mutanen da suka rasa rayukansu.

Ya ce an tura jami’an tsaro domin maido da zaman lafiya, yayin da ake ci gaba da kokarin gano wadanda ke da alhakin hakan.

'Yan bindiga sun kona makaranta a Niger

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun ƙone wata makarantar firamare da ke garin Dekara a ƙaramar hukumar Borgu ta Niger.

Hatsabiban 'yan bindigan sun ɗauki wannan matakin ne duk da cewa sun karɓi harajin Naira miliyan 10 daga al’ummomin yankin.

Majiyoyi sun bayyana cewa ƙauyuka da al’ummomin gundumar Dekara sun haɗa kuɗi tare domin biyan Naira miliyan 10 da 'yan bindigar suka nema bayan sun yi barazanar kai hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com